LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL


Tafiya suke suna hira irin ta abokai sai dariya suke ma junansu Salima na bayan mota da waya a hannunta tana chat fa friends d’inta, sam bata jin abunda suke cewa to suma k’asa-k’asa suke hirar su, har suka shigo Kano suka d’auki hanyar K’auyan d’an kunkuru Yusuf yace”Har na fara jin wata iska me dad’i wallahi” Dariya Hakkim yayi yace.” Sai ma ka shiga garin sosai zakaji dad’insa shiru babu hayaniya sai manya bishiyu masu bada iska mai dad’i”.

Wani dank’areran get nake hangowa tunda nesa nan naga Hakkim ya nufa da mota, wasu mutane dake tsaye bakin gurin suka bud’e masa get d’in ya shiga da motar ciki, sai da yayi tafiya sosai sannan ya samu guri yayi parking Yusuf ya futo daga motar yana fad’in”Wow kaga guri sai kace a k’asar waje Yaro” ? Murmushi Hakkim yayi ya kashe motar futowa yayi yana mik’a ta gajiya gurin kawai yake bi da kallo cike da sha’awa irin bokokin nan na k’asar waje hudu ne sai part biyu da gurin kiwo an kewaye shi na kaji daban na kifi daban na talo talo daban ko wanne an kewaye shi, gefan hannunsa kuma wasu manya-manya lambu ne a kewaye da raga k’ofar da mutum zai shiga tana can baya, da sauri yaja hannun Yusuf suka nufi gurin shiga Salima na binsu a baya tana tsalle da dariya fad’i take”Zanci d’ata in more abuna dama a abuja babu sai mutum ya sha wahala kafin ya samu. Suna shiga kowa ya kama gabansa domin kashe kwarkwatar idonsa , Hakkim ya nutsa sosai ciki, yaji motsi saman bishiya d’aga kai yayi da sauri, wata halitta ya gani ita ba mutum ba ita ba aljana ba, gabansa ya fad’i, dake namijin duniya ne sai ya dake yana hirji cikin zuciyarsa cikin jarumta yace”Ke wacece ke mutum ko aljana”? Ladidi ta tsura masa ido tana kallonsa,a zuciyar ta tace”Dube shi kyakyawa d’an burni yasa fararan kaya gaskiya yayi kyau”!! Buga mata tsawa! yayi a karo na biyu ya sake fad’in”Mutum ko aljan nace kun tsura min ido babu kyawun gani kuna kallo” Soso kanta tayi ta ciro kwarkwata har biyu, ta kalle shi ya kalle ta daga saman bishiyan ta sako masa kwarkwartar ta fad’o jikinsa, abunka da fararan kaya, aikuwa nan take suka nuna kwarkwata ga tanan tana bin gefen kafad’ar shi har guda biyu, tsalle! Ya buga ganin k’awaro baki na bin jikinsa ya bugeta cike da k’yamkyami ya tsartar da miyau! Ya d’ago kansa a fusace! Ganinta yayi mak’ale jikin bishiyar tana k’okarin sakkowa kamar me sufa, dura k’asa tayi yayi sauri matsawa baya gaban shi na bugawa! Amma idan ka kalli fuskarsa baza ka gane razanar sa ba,, cikin minti biyu ya gama k’are mata kallo, k’anjamammiyar yarinya mai k’irar muciya kanta wani gurin da gashi wani garin babu fuskarta a rame sai uban dogon hanci irin na aljani ga hannuta da k’afar ta k’ananu duk jijiya” hirji yake Cikin zuciyar sa, yace.”Ke aljana ce ko mutum”? Kai tsaye tace”Aljana ce” Cikin tsawa yace”Bar nan yanzu don ubanki ko na zane ki, dagani ke ba aljana bace ibilishiya ce,me ya kawo nan har da hawa kan bishiya” ? “kar ka k’ara zagina” tafad’a idonta a kansa, a zabure! Yace”Ubanki uwarki kajini da shegiyar yarinya k’azama zo ki fuce daga gurin nan ko in karya miki k’afafu” ya k’arashe maganar yana zuwa kanta, wani tsalle ta buga! Ta d’ane jikin bishiyar mangwaro can kololowa, cikin mamaki ya d’aga kai yana kallonta, itama shi take kallo tace.” Idan ka isa kazo ka Kore ni, bayan ma gonar ta kakana ce kuka sace mana” Hakkim ya saki baki galala! Yana kallonta ,wasu mangwaro ta Ciro sun gaji da nuna ta mulmulasu sukayi ruwa tafasa da bakin ta ta saita shi, ta jefo masa a jiki kafin kace me yayi fallatsi ya b’ata masa duk gaban rigar sa da fuskar sa.

COMMENT VOTE AND SHARE
[9/29, 6:51 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

Ayi hak’uri da errow⚠

Yau pege d’in babu yawa saboda ina fama da zazzab’i, ina b’ukatar addu’ar ku????????????

????12

Cikin tsantsar b’acin rai! Ya d’aga kansa sama yana kallonta, tana k’okarin saukowa sai dariya take k’yalk’yala masa, tana dura k’asa ya cafki hannunta wanda yaji tamkar ya rik’e bushashan ice dan tauri, k’okarin fuzge hannunta take tana zabga masa harara tamkar idonta zai fad’o k’asa!. A fusace! ya kai mata wani wawan mari! ta kauce da sauri! amma duk da haka sai da ya samu gefan fuskar ta, zagi ta hau d’ura masa tana tsalle, kamar zata kai masa duka take fad’in “Sakar min hannuna ni ba ” yar iska bace”. Hakkim ya buge mata baki da d’aya hannun nasa, kafin kace kwabo jini ya fara zuba, ihu! ta kurma wanda yasa su Yusuf suka runtumo da gudu gurin. Hakkim na tsaye hannunsa tam! da na Ladidi sai buge-buge take tana kwanciya a k’asa dole sai ta k’wace daga hannunsa, wawan hauri ya kai mata da k’afar shi guda, ta k’ara k’wala k’ara tana kuza masa ashariya! Yusuf ya k’araso gurin, hankali a tashe yake fad’in”Wai meye yake faruwa ne? wannan yarinyar fa, daga ina”.? Bak’in ciki da b’acin ya hana shi cewa uffan,sai cije baki yake yana dukanta da k’afar sa, Salima ta k’araso gurin jikinta a sanyaye take fad’in”Broth waye ya b’ata maka jiki da wannan k’azantar ” Yusuf ya Kai dubansa gurin shi sam bai lura ba, hankalin sa na kan Ladidi, har hanzu hannuta na rike a nashi yana dukanta da k’afafunsa ita kuma bakin ta bai bar zaginsa ba, tana deb’o k’asar gurin tana watsa masa a jiki. Yusuf ya fara k’okarin kwace daga hannunsa, ya fuzge da k’arfin yayi wani mugun boll da ita ta gangara can gurin k’ofar futa kanta ya bugu da wani dutse, da sauri ta mike tamkar ba ita akai wa wannan dukan ba, wani mugun tsalle tayi sai gata a gabansa, dama ya tsammaci zuwan ta, k’afar sa ya sanya ya tad’eta! Ta fad’in a gurin a sume!! Yusuf ya saka salati yana fad’in”Shikkenan kaga ka kashe yarinyar mutane ko, innalilahi wa’inna ilahi raji’un”!! Salima ta fashe da kuka tayi kan Ladidi tana tattab’a jikinta, Yusuf ya futa daga gurin da sauri, gabansa sai fad’uwa yake, ashe k’addara ce ta kawo shi, shi ko Hakkim ko a jikinsa, karkad’e rigar sa yayi cike da bak’in ciki da b’acin rai! Yake k’okarin barin gurin,Salima ta rik’e hannunsa tana kuka take fad’in”Broth ina zakaje LA tsaya ka duba wannan yarinyar ko suma tayi don girman Allah, ni kam Wallahi da nasan haka zata faru da ban biyo ka ba” . Fuzge hannunsa yayi cikin b’acin rai! Yace”Yanzu ma kina iya komawa gida babu Wanda ya rike miki k’afafu ga hanya nan” yana gama fad’in maganar shi ya futa daga gurin. Karo suka ci da Yusuf ya tawo da sauri hannunsa rike da robar ruwa na faro, ko kallonsa bai yi ba yayi fucewar sa.

COMMENT VOTE AND SHARE
[9/30, 10:08 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button