LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

 Iya tace." Hakane kuma dole mu jirasu domin muji da abunda zasu dashi."

Lokacin dasu Hakkim suka koma gida babu kowa a farlo sai General kawai duk sun je sun kwanta, yana zaune yana jiran dawowar su

 Ko zama bai bari sunyi ba yace." Kun samu inda take.?
 Yusuf yace." Eh Dady mun samu saboda dare yasa muka ce mu bari gobe da safe sai mu koma."
 Dady ya mike tsaye yana kallonsu yace." Allah ya kaimu gobe nima dani za'aje domin inga inda yarinyar take."

 Shiru sukayi kai a kasa sai da ya wuce tukkuna suka dago Kansu, Hakkim ya zube. Cikin kujera yana shafa kansa yayi wata muguwar gajiyq

 Yusuf kuwa tv ya kuna ya zauna yana fadin ." duk yanda kake ganin ga gaji ni nafi ka gajiya wallahi."
Hakkim yayi masa shiru yana lumshe ido, mik'ewa yayi ya nufi firji domin d'auko Lemo ko ya samu ya samu sassauci a zuciyarsa.

Da safe da k’yar Iya ta taimakwa Ladidi tayi wanka domin jikin nata ya kara d’aukar zafi mussaman gefen wuyanta wanda da k’yar take iya motsa shi, har dan kumbura yayi.
Tana zaune cikin wani leshi wanda ya gaji da kodewa yayi haske sosai dinki riga da zani ne da d’ankwali Iya ma ta shirya tsaf hijab dinta na aje a gefe D’alha ya shigo ya tarar dasu suna karyawa iya na lallaba ta tasha koko, tana kin sha, saboda zafi da take ji gurin hadiyar abu shiyasa ma ko kosai ba ta Ciba.

   Iya tace." Har yanzu basu zo ba ko." Daga kai D'alha yayi Yace. " gashi yanzu k'arfe takwas ba."

 Tace." To ai sai muta fi domin ba zamu tsaya su katse mana abunda mukayi NIyya ba."
 Yace." Hakane kuwa hankali na ya kara tashi da yanda naga yarinyar ta tashi da jiki yau." Iya tace." Yanzu da k'yar take hadiyar koko dan taki cin k'osai ma."
Kallonta D'alha yake cike da tausayi..... Sallama suka ji daga waje D'alha ya mike da sauri ya futa

Gaban shi ne ya fad’i ganin hamshakin mutum jingine da mota, fuskokin su Hakkim yake karewa kallo yana so ya fahimci ko sune mutanan na jiya.

A hankali ya k’arasa kusa dasu ya dan rankwafa gami da fadin.” Barka da zuwa ranka ya Dade.”

General ya mik’a masa hannu fuskar sa a sake yace.” Barka kadai samari fatan mun same Ku lafiya. “

D'alha yace." Lafiya lau Alhaji." Hannu ya mik'awa su Hakkim sukayi musabaha ga juna yace." Hala kune bakinmu na jiya da daddare ko."?
Yusuf yace." Mune wallahi."
D'alha yace." To bari in shiga gida in sanar da mahaifiyata dama yanzu muke shirin futa."

  General yace." Babu laifi samari." D'alha ya shiga gida cikin sauri.

Gogon ku na tsaye jikin mota ya harde hannuwansa a k’irji jira kawai su shiga gidan ya kara yin ido hudu da marakaunyar yarinyar nan yaga tayi ladaf ko kuwa.
Minti biyar D’alha yayi ya dawo da sauri yace.” Bisimillah Alhaji ku shigo daga ciki.”

Bayan sa suka bi. Yaran unguwar dake tsaye na kallonsu suka biyo su yuuuuuuu! D'alha ya buga musu tsawa, suka koma gefe,wasu na cewa Ladidi ce taje ta jawo futuna.
 Mai koko na zaune gefan tabarma ta lullub'e jikinta da mayafi. Sukayi sallama suka shiga gurin zama ta nuna musu tana musu Barka da zuwa cike da mamakinsu
Suka zauna babu kyankyamin komai domin gidan tsaf yake tun safe tayi shara da wanke wanke ko ina tas iskar Safiya na kadawa 

Gaisawa suke cike da mutumchi, General yace." Ina fata nan ne gidan su wata yarinya Ladidi."
Mai koko tace." K'warai kuwa nan Alhaji ina fatan ba wani abun tayi muku ba."
Cike fa tausayi yake kallonta yace." Mine dai mukayi mata laif............ Kafin ya gama maganar shi Ladidi ta bayyana a gurin, ta tsaya tsakinyar ta barmar idonta kan  Hakkim! suka kurawa juna ido. Ihu!!! Ta kurma tana nuna shi da hannunta tace." Iya!!! Gashinan shine ya dinga dukana kamar zai kashe ni wallahi Iya shine, Allah ya kawo shi gidanmu mu dauki fansa domin bazan  barshi ba."

COMMENT VOTE AND SHARE
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????23

Cike da mamaki General yake kallon Ladidi. dake tsaye Kansu D’alha mata tsawa ta matsa daka kan mutane amma kamar kara ingizata ake tanayi kamar zata kaiwa Hakkim duka.

General ya kalli Yusuf da alamun tambaya.

Yusuf yace.” Itace yarinyar Dady.”

Sosai General yayi mamakin kankantar ta ya kalli Hakkim cike da takaici yace.” Meye abun duka jikin wannan k’aramar yarinyar.”?

Sunkuyar da kansa kasa yayi. Yana jin tsoron kar dady ya tsinkashi a gaban mutane.

Ladidi ta ruga kicin da gudu! Duk suka bita da kallo. D’alha kamar yasan abunda zatayi ya mike da sauri zai bita.sai gata ta futo hannunta rike da doguwar muciyar da Iya take dama koko tayi kan Hakkim da gudu.

Hakkim yasan gurinsa ta nufo sai ya shirya tsaff ta d’aga muciyar da k’arfi zata maka masa.ya rike ta da sauri yw fuzgota sai gata ta fad’o jikinsa,cike da mugunta ya wurgar da ita gurin kanta ya bugu da bango ihu!! Ta kurma tana fadin.” Wayyo kaina.”!! D’alha yazo ya daga ta cike da jin haushi ya kwarfa mata mari yana fad’in.” Ashe rashin lafiyar naki na k’arya ne.”

  General yace." Yi mata a hankali samari." D'alha yace."Alhaji baka San halin yarinyar nan ba ne."


  General yace." Koma meye dai ni ta burge ni tunda take k'okarin k'watar 'yan cinta ga Wanda ya cuce ta, saboda rashin imani kamar Hakkim da shekarunsa da komai ya zage k'arfin shi kan yarinya k'arama kamar wannan."



  Mai koko tace." Alhaji bamu game me kake nufi ba."?

General yace.” Wannan da yake zaune shine ya sumar muku da ita jiya nine kuma mahaifinsa Nazo domin in nemi afuwar Ku.”

Iya ta mike tsaye da sauri ta gyara d'aurin zaninta tace." Ko dana ji ahwo!!! Shiyasa naga yana sinne kai tamkar b'arawo a hannun mata,wato dama kaine kake k'okarin kurman tamin da jikita. ? Babu shakka Ladidi ta kurmance sai munyi sha'ra'a dakai."

Wani mugun haushin Matar yaji a zuciyarsa yace.” Da zata kurman ce ma ai da kowa ya huta da alak’ak’ai.”

 Ladidi ta taso da sauri tana rike Iya tana kuka take fad'in." Iya kar ki barshi nima bazan barshi ba."


General yace." Innalillahi wa'inna ilahi rajinu. Ashe abun yayi tsanani haka,shiyasa zuciya ta kasa amunta nace dole sai Nazo naga halin da take ciki. Tabbas dole ki dauki hukunci Iya amma ki zauna muyi mgn dake ta fahimta. "

Mai koko ta koma ta zauna tana maida nuffashi Ladidi ta jawo jikinta ta rungume ta tana rarrashin ta.

Haushi duk ya tuk’e D’alha ya kalli General a nutse yace.” Alhaji ka kwantar da hankalin ka don Allah ni nasan duk abunda ya faru da dalili haka kurum shi bazai kamata ya doke ta ba.”

General yace.” Haka kake gani samari inace gashinan a gabanka ya wurgar da ita da mugunta ta buga kanta a hango ko baka gani bane.”?

D’alha yace.” Nagaji Alhaji ai kana ganin abunda tayi masa ko.”?

Shiru General yayi yana girgiza kansa.

D’alha ya bugawa ladidi tsawa tare da fad’in” yimana shiru shashasha kawai kin bude baki kina kukan banza da wofi.”

Iya tace.” K’yaleta tayi kukan ta to kaji.”!!!!.

General yace.”ina me bawa zuciyoyin Ku hakuri sosai domin narasa dame zan fara a halin yanzu amma kafin wani hukunci ya biyo baya ina rokon Ku da muje mu kai yarinyar nan asibiti a duba ta, domin hankalina ya tashi da jin maganar da kikayi.”

D’alha yace.” Dama yanzu zamu tafi asibitin cikin gari.”

Mik’ewa General yayi yace.” Maza Ku futo muje Allah ya kiyaye gaba.”

Mai koko ta zura mata hijabinta tana goge mata fuska suka futa

To gurin shiga motar ma Ladidi ki tayi ta dinga turjewa wai bata yarda ba gurin yankan kai za’a kaisu a siyar musu da kai.

Da k’yar Dady ya rarrashe ta ta shiga motar. Hakkim kamar ya Dora hannu aka Dan takaicin ta.

Comment vote and share
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????24

Cikin gari suka futa General yace.” Zamu samu pravite hospital anan kurkusa sai mu tsaya kawai ba sai mun je babban asibiti na Murtala ba.”

D’alha yace.” Za’a samu Alhaji.” Yace.” Sai mu tsaya anan kawai a duba ta.”

Cikin birget suka samu hospital.Hakkim ya kashe mota duk suka futo suka shiga ciki.

Idan da kud’in ka babu wahala da kaskantar da kai da zakayi,D’alha yayi mamakin yanda ma’aikatan asubitin suke karrama Alhaji sai rawar jiki suke.nan ka yanki kati likita na ofis General yace.” Da Ladidi tazo su shiga tare. Mak’ale kafad’a tayi tana b’uya bayan Mai koko, murmushi yayi yace.” Zo muje ciki dactor ya duba ki kinji ko.” Ladidi ta zumb’uro baki gaba. Yace.” Dawa-dawa kike so mu shiga tare.” ? Shiru tayi masa. Haushi yasa D’alha ya buga mata tsawa tare da fad’in.” Idan baki sake ta wallahi sai Nazo nan na gaura miki mari.”

 Mai koko tace." Kaga D'alha rabu da ita don Allah.Ina dalili nifa wannan asibitin be kwanta min a rai ba,asibiti ko ina sanyi hatta k'afar ka in ka aje ta a kasa sanyi ga wasu abubuwa a bango naji fa ana cewa wasu asubitin duk barna suke aikata wa. Gwara muje na Murtala kawai."

Takaici ya hana D'alha cewa komai. General yace." Iya wannan hospital din ana biyan kudi sab'anin sa dana gwamnati kenan kinga ai baza mu bi wannan dogon layin ba, kiyi hakuri mu shiga tare dake babu abunda za'ayi mata."
 Mai koko ta kalli Ladidi tana yi mata magana k'asa-k'asa sannan ta sake ta suka mike General yayu gaba suka bishi a baya. D'alha ya nemi guri ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.

Hakkim kuwa takaici ya hanashi cewa komai yarasa me yasa Dady ya damu da al’amarin yarinyar nan wallahi. Shiko Yusuf Dariya yakewa Ladidi ganin yanda take ta kalle-kalle kauyacinta kawai take.
Dactor suka gaisa da General cikin mutum ci yana tsokanar Ladidi bata San ma yanayi ba domin tana can tana kallon tv mak’ale a bango na wani India film na fad’a, amma ba fassarar hausa bace. Dariya ta kyalkyale dashi tace.” Iya kalli wannan film din ki gani don Allah, na fada miki afton nan Dan bala’in ne hinefa singam da nake fada miki,hahahahahaha.”

General da Dactor suka saki baki suna kallon mara lafiya tayi tsalle gaban tv tana kallo tamkar zata rikito da ita daga sama.

Wannan karon kunya ce ta kama Iya ganin abunda Ladidi take babu kamun kai,kokari kawai take tayi tsalle ta tab’o tv in da jarumi Ajay devgan yake ragargaza ‘yan gidan boss da bundigar sa,Ihu!! Kawai ta kurmawa tana buga tsalle.
Sosai dariya take cin General yana k’okarin dannewa sai da ta subuce. Ganin yana dariya yasa Dactor ya fara yi shima Suna kallon juna.
Iya tana k’okarin kamo ta tana fuzgewa duk kunya ta ishe ta gashi tun farko dama bata iya sarrafa Ladidi. Dactor ne da ya gaji da abunda take ga jama’a a na jiran shi a waje yasa ya buga mata tsawa! Tare da fad’in.” Ki nutsu yanzu ko in sa a zo a zuk’i jinin ki kuma inyi miki allura goma.”
Firgigit ta dawo nutsuwar ta jin zan can Allura sai taji kallon ya fuce mata daga rai mugun tsoran dactor ya shiga zuciyar ta simi-simi ta dawo kusa da Iya tana zare ido.!

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button