LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

Iya tace.” Ke kam anyi mara wayo wallahi ke da baki da lafiya kike tsalle-tsalle.”
Da sauri tace.” Nifa lafiya na lau ni dai kice kar ayi min allura bana so.”

General yace.” Ai dama ba allura za’ayi miki ba, dawo nan kusa dani dactor ya duba ki kaman matsalar kunnen ki,sai ya baki magani bazan bari yayi miki allura ba.”
A d’arare taje ta zauna inda yake nuna mata sai harara Dactor take yi, bai lura ba yana can yana aikin sa. Ya d’ago kansa a nutse yace Alhaji meye Matsalar ta ne.” Iya da ba’a tambaya ta fara zayya no masa abunda ya faru.”
A hankali ya ambaci sunan Ladidi Wanda ya gani jikin kati wato Amina sai yaga bata dago kai ta kalle shi ba, da Ladidi ya kira ta da k’arfi sai ta dago kanta tana kallonsa. Mik’ewa yayi hannunsa rike da wani Abu,ganin yana zuwa inda suke ne yasa ta tsora ta ga wani Abu a hannunsa. Kafin General ya ankara ta buga tsalle, wajan kofar futa suka tsince ta tana kici-kicin budewa ta futa.

General ya mike da sauri yana kiranta ko sauraron sa ba tayi ba Allah ya bata sa'a ta bude tayi waje da gudu.!

Su Hakkim na zaune reception suka ga futowar ta kamar walkiya tayi kofar futa. D’alha gyangyad’i yake bai ganta ba, kasan cewar jiya baccinsa ragagge ne.
General suka gani ya futo hankali a tashe yake fadin “Tana ina ne.” Kofa ya kalla yaga gilmawar ta ta futa, ya bugawa Hakkim tsawa tare da fad’in” Maza tashi kaje ka dauko ta.wato kana kallo ta futa baka yi wani Abu akai ba ko.”?

Hakkim ya mike da sauri ya futa yana kunshe dariya yaji dad’i da Ladidi ta nunawa Dady wacece ita.

General ya jin gina da hango yana sauke ajiyar zuciya gefe guda kuma yana mamakin halin yarinyar kamar aljana, yanzu ya fara sarewa da lamarinta.

Hakkim na futa ya hango ta bakin get tana rigima da masu gadi, dole sai sun barta ta futa su kuma sun hanata saboda ganin yanda ta futo daga ciki tana fella guda sai kace me tab’in hankali. Kuma sunga lokacin da suka zo cikin mota sosai asibiti yake da tsaro. A hankali ya Isa inda suke dama tun kafin ya k’arasa yayi shiri ya tattate hannun rigarsa, yana isa ya sunkuce ta, sosai ya rike tamau! Ya had’e k’afafun ta da hannaye ta ya sab’a a kafad’arsa. Ladidi ta dinga ihu! Tana zandare masa a baya Hakkim ya rik’e hannuwan balle ta doke shi, sai ta kafa kanta a wuyansa ta gartsa masa cizo. Ko a jikinsa, bai sauke ta ba sai ya kaita har ofis din dactoe.
Iya tace.”Sannu na yaba da k’okarin ka samari da baka d’auko ta ba wallahi futa waje zatayi k’arshe mu rasa inda take, Maza danne ta likita ya duba ta.” Hakkim ya b’ata fuska bai mata komai ba ya fara k’okarin futa sai suka ci karo da General da D’alha suna k’okarin shigowa, Dady yace.” Koma muje ka riketa a duba kunnen nata. Babu yadda ya iya ya koma ya zauna kan wata kujera Ya jawo Ladidi tana turjewa ya rike tamau! A jikinsa Dactor yazo da Abu a hannunsa ya kunna hasken sa, ya kafa kunnen Ladidi yana dubawa.

Ihu!!!!! Take kurmawa tun k’arfin ta,tana haure-haure da hannuwata da k’afafun ta tare da ya kushin Hakkim ko ta Ina.ganin hakane yasa D’alha zuwa gurin ya rike hannunwan nata tamau! Dactor ya cigaba da aikinsa.

COMMENT VOTE AND SHARE
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHIMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????25

Hakkim zuciyar sa zafi take masa yana jin kamar ya saki Ladidi ta fad’i kasa saboda yanda take ta faman duk k’irjinsa duk ta ya kushe masa fatar hannunsa ga majinarta da miyau duk sun b’ata masa jikinsa, lokaci guda yaji zuciyarsa na tashi kyamkyamin Ladidi yake sosai.ya dinga kauda fuskarsa har dactor ya gama dube-duben sa ya matsa daga gurin.

 Da sauri ya sake ta ta fad'i kasan gurin ya mik'e da sauri yana duba jikinsa. Saboda fargabar da suke ciki babu Wanda ya damu da fad'uwarta a gurin itama bata damuba ta mik'e zumbur tana sharb'e hawayen fuskar ta. 

General ya k’araso kusa da ita cikin taushin harshe yace.” Yi hakuri kinji Aminatu kinga ni ai na fada miki ba allura za ai miki ba kin tashi hankalin ki da namu kiyi shiru ki fada min me kike so in siya miki.”
Ya k’arashe maganar sa lokacin da suke zama kujerar dake fuskantar ta dactor.

Tsabar takaici da b’acin rai yasa Hakkim kasa cewa komai ya bude kofa ya futa a fusace.!!

Dactor ya gama rubuce-rubucen sa ya d'ago yana kallon General yace." Alhaji gaskiya ta samu matsala daga kunnen ta na hagu,  Wanda ya dumd'e ba taji sosai ta bangaran sa,amma insha Allahu in an bi doka zai dawo dai-dai yanzu zan dorata kan magani kuma kullum za'a dunga kawo ta ana mata wankin kunnen tsahon sati uku, insha Allahu idan akayi haka za'a samu maslaha."

General ya d’aga kansa cike da takaici yake Neman Hakkim a gurin sai ga babu shi girgiza kai yayi ya maida kallonsa gurin Dactor yace.” Babu damuwa dactor INA so ka tsaya min kan yarinyar nan domin bana so ta rasa wani Abu me muhimmamci a rayuwar ta mussaman ma kunne domin jikin dan Adam yana da muhimamci duk abunda ake buk’ata zan biya insha Allahu a kula min da ita.”

Dactor yace." Insha Allahu za muyi iya iyawar mu Matsalar daga yarinyar ne Allah yasa ta bamu hadin kai."

General yace.” Insha Allahu babu Matsala.” Dactor ya mik’e tsaye yace.” Muje pharmacy zan had’a mata magani gobe misalin takwas na safe sai a kawo ta domi fara yi mata wankin kunne.”

Duk suka mik'e suka futa a reception suka zauna Dactor shi da wata nurse suka nufi dakin magana.

General ya dinga laluben inda Hakkim yake bai ganshi ba Yusuf ya kalla da fuska a daure yace.” Ina Hakkim yake.?

Kai a sunkuye Yusuf yace.” Ya tafi sanjo kaya.”

Cike da mamaki General yace.” Kamar yaya ya tafi sanjo kaya wato yana nufin mu tsaya jiran shi ya tafi da mota sai sanda ya ga damar dawowa ko me.?
K’asa da kai Yusuf yayi cike da girmamawa.

General yace.” Ya kyauta ai.”

Suna zaune Dactor ya dawo hannunsa rike da Leda me tambari da sunan hospital din nasu cike da mugunguna nasha dana digawa a kunne dactor ya mik’awa General yana fad’a masa yanda za’ayi amfani dasu.

 Nan General ya karb'i numbar account ni dactor din domin ya turo musu da hakkin su sukayi sallama suka futa.


Hakkim ne ya shigo asibitin cikin mota General ya sauke ajiyar zuciya a fili yace." Kayiwa kanka k'iyamun laili wallahi da ka bari mun bi motar haya sai na b'ata maka rai."

Shiru yayi yana sunkuyar da kai kasa ya sanjo kaya yanzu yana sanye da wata lafiyyyare shadda geznar sai maiko take brown ce babu hula kanshi sai sumar shi tasha gyara da alamu sai da ya sake sabon Wanka kafin ya dawo.

General da kansa ya budewa Ladidi kofar ta shiga su Iya da D’alha suka shiga sannan ya shiga, Yusuf ya zauna kusa da Hakkim ya ja motar Dady na d’agawa Dactor hannu.

General ya zurfafa a tunanin yaya za'ayi wannan bayin Allah su yarda da shawarar da ya yanke kan Ladidi, zuciyarsa a dake ya kalli Mai koko da tayi tsumu! Cikin hijabi tana shan Ac mota sai zare ido take yace." Iya akwai shawarar da na yanke kan Aminatu. "

Mai koko ta kalle shi tace.” To Alaji ai babu komai ka fada min naji ai kana da kirki kai kam ko ajikin masu kud’in samun kamar ka sai an tona lallai albasa batayi halin ruwa ba wancan yaron naka me zuciyar kafurai da rashin imani.”
Tafad’a tana hararar Hakkim dake driving

Takaici kamar ya kashe D’alha Ji Iya da wata magana don Allah ya juyo yana kifta mata ido Iya ko ganewa ba tayi ba ta cigaba da surutun ta daga ni tana cike da jin haushin Hakkim din.

Sai da General ya Bari ta gama surutun nata sannan yace.” Dama cewa nayi me zai hana Aminatu ta dawo hannuna saboda shan maganin ta kan k’aida idan yaso idan lokacin da dactor din ya d’iba ya cika sai ta dawo gurin ki ko yaya kike CE.”

General ya karashe maganar a tausashe domin ya lura tsohuwar yar taratsatsi ce.

Mai koko ta kalli General baki na rawa tace.” Me kake cewa Alhaji.”!!!!!!?

Inga ruwan comment da dogon sharhi kan book din nan idan ba haka ba tammm! Zan mai dashi…….. Ba sai na fada ba kun San sauran ehe, ko ta ina ina ga ruwan comment na zuba Lol????

COMMENT VOTE AND SHARE
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button