LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

LIKITAN ZUCHIYAH COMPLETE HAUSA NOVEL

[29/04 12:05 pm] ????◾◼▪????: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•Rahma Muh’md Rufa’i Nalele..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

Labari me tab’a zuciyata…. Karatu cikin harshen hausa… Tafiya cikin nutsuwa da tunani me kyau… Yanayi na d’aukar hankali….. Soyayyar gaskiya me tafiya da qauna Zallah….
Bani da lokacin b’ata lokaci akanku dan kunsan dawa kuke… Da marubuciyar data nishad’antar daku cikin Novel nata na Y’AR QAUYE KO Y’AR BIRNI…. MASEEFAR SOO… Birnin masoya… SADEEQ.. Amakirci na… SAMAREEN BANAH…. HAYATUDDEN..

Ban yarda kina budurwa ko kina bazawara. Ko kana saurayi. Koka tab’ayin Aure Ku karanta min littafi ba. Nayi shine kawai DON Ma’Aurata???? ba dan Kuba…

Jaruman cikin labarina….
ADAMSY
NUFAISAT
TAUDAT
MUSLEEMAT
RAHMA NALELE Auntyn Luv☆
Junior Ramadan nah????????

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 01☆

ADAMSY Likitan zuciya… Aka rubuta ajikin allon bangwan dazai sataka da cikin ofishin nasa..
Da rikicewa wata Yarinya me sanye da kayan asibiti farare (Norse) take kwankwasa k’ofar ofishin nasa..
Kyakkyawan mutum ne.. Wanda ya had’u tako ta’ina. Shekarunsa bazasu wucce 33 ba. Saidai idan kagansa zakayi tunanin d’an shekara ishirin da shidda ne. Yana sanye da rigarsu ta likitoci kan kujerar da take mallakinsa. Yana da dogwan hanci me d’auke siririyar fuska wacce take da fad’i kaɗan.. Ma’ana dai anan shine fuskarsa baza’a kirata da ririya ba kuma baza’a kirata dame fad’i ba. Tana dai tsaka tsaki..
Sannan yana d’aya daga cikin mutanan nan waƴanda sudai baza’a kirasu da dogayeba. kuma baza’a kirasu da gajeru ba.. Saidai yana da ɗan ƙiba kaɗan.. Wacce bazamu kirata dame muni ba.
Sannan yana da faɗin ƙirji me ɗaukar hankali..

Yana da San ƙamshi yana da San tsafta. Yana da San kwalliya. Yana da San gaye. Yana da San abu me kyau. Yana San gaskiya. Yana San mutum me bin ra'ayinsa. Yana San wulɗa da mutanan kirki. Yana San matarsa San gaskiya. Yana san iyayansa. Yana San yara so me tsanani. Yana San temakwan su. Yana San temako arayuwarsa. Yana San mutumin da yake San shiga al'amuransa. Yana San sana'arsa ta ceton rai da kasuwancinsa da yakeyi

Ga Y’a mace kuma. Yana San mace me SHAGWAƁA. Me kirki. Me nutsuwa. Me San KWALLIYA. Me tsafta. Me kissa. Me iyayi. Me iya kalaman qauna. Me nutsuwa yayin da yake jinta. ME IYA GIRKI…
Baya San rainin hankali da wulaƙanci haɗi da munafunci.. Mutum ne me aji!!!. Aji!!!! Fah????. Irin sosai d’innan.????????
Baya shiga harkar daba tashi ba.
Sam ADAMSY bashi da yawan abokanaye.. Saidai ko’ina ya shiga afad’in garin KADUNA sanshi ake. Ƙaunarsa ake. Jinsa ake…. Saboda halinsa nagari ne. Me kyauta ne. Me tsausayine. Me kwantar dakai ne agun duk wani mutum Wanda yasan ya girme masa ya haifesa.. Toh ADAMSY yana da halin bashi girmansa..
Wannan kad’an kenan daga cikin halaye na ADAMSY..


“Yas shigo… Yace da wannan yarinyar da take kwankwasama mai ƙokar
Ahankali tashiga tana cewa.. “Sannu doctor. Dama mahaifiyatace aka kawota yanxu. Shine doctor RAMADAN yace pls kazo kad’an samai hannu.. Yau baya jin dad’ine. Sannan yace dan Allah kayi hakuri yasan lokacin tafiyanka yayi. Danya kiraka baka d’auka ba.
ɗan rintse ido yayi kad’an. Sai hakan ya qara masa kyau..

Sarki ya tabbata ga Allah. Mamallakin kowa me komai. Allah kabani miji irin ADAMSY. Me kyau. ne me tausayi. me dukiya. duk da mahaifiyarta ce kwance rai ahannun me dukka. Amman bai hana zuciyarta fad’in wannan kalamai cikin ranta ba!!????

Ahankali cikin sanyayyiyar muryarsa me dad’in sauraro yace.. “Owkie. Jeki ganinan zuwa..
Da Murmushi akan fuskarta tayimai godiya da ficcewa daga ofishin..
Sauri-sauri gudu-gudu ya saka laptop ɗinsa a jaka tare da ɗaukar wayarsa ya fitto da kulle office ɗin nasa..
Cike da nutsuwa yake tafiya kamar yanda ya saba.. Cikin nutsuwa masu tsaran lafiyansa sukaxo garesa da karb’ar laptop ɗin tasa. Da wayansa. Suka saka cikin motar da yake hawa.
Sannan yace musu baya fitto tafiya bane. Zai d’an duba wata ne a part na doctor RAMADAN Yanxu zai fitto. Ai da ladabi suka mai fatan alkairi yanufi part ɗin doctor RAMADAN

 "Bayan doctor RAMADAN ya gama yimasa bayani akan tana da ciwan sugane.. Sai kuma yanxu ya lura Kamar tana da matsala da zuciyarta. Hakan yasa ya nemi saka hannunsa...

Shuru doctor ADAMSY yayi yana duba matar.
Can yace… “Eh. Zuciyarta tafara karɓan wasu sakwanni. Wanda ada bata karɓarsu. Wannan dalilin ne yasa take qoqarin San taga taba me ita wahala. Kafin tabuga.
Zan mata wani aiki da ɗorata akan wasu magunguna.
Idan Allah yaso. Zata samu lafiya. Saidai fah dole ta kaucema waƴancen sakwannin da suke San tarwatsa mata zuciyar tata..
Jan numfashi doctor RAMADAN yayi da cewa.. “Masha Allah. Naga zuciyar tafi buƙatan kulawa ayanxu. Dan haka kagama naka aikin nayi nawa..
“Toh akai min Ita part d’ina… Ya faɗi hakan yana me ficcewa daga gun.
Da “toh doctor RAMADAN ya bishi dashi..

Awa d’aya ya d’auka yana mata aikin. Kafin ya gama ya baro asibitin..

Motoci bakwai ne suke tafiya akan titin..
Uku a baya uku a gaba.. D’aya ƙaramar a tsakiya..
Kaf dukkansu motacin anrubuta.. ADAMSY..
Kina dai gani kinsan dukiya na aiki..

Direct supermarket d’insa suka nufah Wanda yake da girman gaske.
Babuce kawai babu a supermarket ɗin..
Ma’aikata wajen suna ganin tawowarsa kowa ya gyara kansa.. as oga yaxo..????????
ɗan zagaye zagayensa kawai yayi da duba wasu mahimman abubuwa sannan ya kalli wani qaninsa Salim Wanda ya ɗorasa akan al’amuran. Yace dashi… “Ka qara kula sosai da aikinka.. Dan naga kamar kana wasa dashi..
“Insha Allah zan qara kula.. Amin afuwa..
Maida gilashinsa ADAMSY yayi da sakin wani Murmushi ya juya yana bashi amsa da cewa.. “Anyi maka. Dafatan zakayi qoqarin kiyayewa.
“Insha Allah.. Salim ya faɗi cikin sauri da girmamawa..
[29/04 12:05 pm] ????◾

[29/04 12:05 pm] ????◾◼▪????: ☆´-☆´-
☆“˜•☆•
¸☆“☆ª☆_☾☆• ❉ *.¸¸.*♠*.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ *.¸¸.*⚫.¸¸.*♠ *LEEKITAN ~ZUCHIYAH* *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ¸¸.*⚫¸*♠ *.¸¸.*⚫*.¸¸*❆ ☆´-☆´- ☆“˜•☆• ¸☆“☆ª☆_☾☆•
{Zoka Gyara Tunanina}
A true life story

Labari da rubutawa zuwa ga tsarawa.. ☾•RAHMA MUH’MD RUFA’I NALELE..☆

© REAL HAUSA FULANI WRITER’S FORUM????
☆We the best ☆

Email:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&tn=H-R

” بسم الله الرحمن الرحيم

☆page 02☆

Gidan marayu matuqan nasa sukayi dashi Kamar yanda suka saba..
ADAMSY duk wata yana kaima gidan marayuwa tallafi.. Sannan kullum Idan ya tashi daga aiki bayan yaje duba wajen kasuwancinsa toh Lalle saiyaxo ya duba yara agidan marayun nan yaga Ko suna lafiya…
Bama wannan kad’ai ba. Kaf yaran dayake temako bawanda bai san shi ba.
Suna matuƙar sanshi da ƙaunarsa..
Yana zuwa wajen dama suna tsaye wajen jiransa. dan haka yana fittowa suka sungumesa suna masu suna murna da farin cikinsu na ganinsa..
Yafi kula yara qanana. Irin waƴanda suke da shekaru uku biyar takwas goma Sha d’aya Sha biyu. Qasa da haka..
Toh yauma haka yana fittowa ya gansu zaune kawai shi suke jira..
Aƙalla zasukai hamsin.
Haka sukazo da gudu suka rungumesa suna murna
Duk sun cukwikwaiya masa kaya..
Saiya ɗaga wannan ya sauke.. Ya ɗaga wancan ya sauke..
Sanda ya gama raba musu alewa as sadaka. Sannan yaba masu kula dasu wasu kayayyaki Wanda yake da tabbacin akullum yaran suna buƙatansu..
Sannan yayi musu sallama ya fito masu tsaransa suka bud’e mai ƙofar mota ya shiga suka rufe kana sukaja motocin..
Basu tsaya yanxu ako’ina ba. Sai’a gidansa..
Gidane Wanda yatara abin duniya.
Gidane Wanda kana kallansa zaka kirasa da aljannar duniya..
Ya haɗu iya kar haɗuwa.
A far fajiyan gidan motucine na alfarma guda uku… Bayan Wanda aka dawo dashi dasu. Da alama wannan na Matar gidan ne.. Wajen parking na motocin kansa abin kallo ne
Dan yana da girman gaske..
_Haka Allah yake ikwansa.. Wasu yabasu wasu kuma ya hanasu. Kaidai karoqesa ya baka na halak ba haram ba; ya baka Wanda zai maka amfani. Wanda zaka bisa akan tsarin addinin musulinci!!!
Ahankali suka bud’emai motar ya fito da karb’ar y’ar jakarsa. Dan dokace baya barin masu tsaran nasa su shigamai cikin gida inda iyalinsa take.
Kawai Idan yana gida toh suma suyi nasu shashin..

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62Next page

Leave a Reply

Back to top button