LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????21

Sai bayan sallahr magariba suka isa K’auyan D’an kunkuru, Dady ya futo daga mota yana hamdala ga Allah, gurin yake bi da kallo sosai yayi kyau ya k’ayatu haske fitila ko ina,nan ya jagoran ce su suka shiga ciki domin su samu nutsuwa suyi sallah, in yaso ko meye sai ya biyo baya.
Sallolinsu sukayi suka ci abinci, Dady ya kalli agogon dake manne a bangon farlon takwas da rabi na dare, ya kalli Hakkim da fuska a turb’une yace.'” Yanzu dai ka huta sai ka tashi ka fara laluben inda yarinyar mutane take domin inyi abunda ya kawo ni garin.”
Ya d’ago kanshi dake sunkuya yace.” Dady dare yayi yanzu ga hanya babu kyau ga yanayi na damuna gari duk ya jike kayi hakuri sai Gabe.”
Tsawa! Ya buga masa tare da fad’in.” Bana son wata banzar magana ka tashi ka fara laluben yarinyar nan da halin da take ciki.”

  Mik'ewa yayi da sauri Yusuf ya mike shima suka futa tare.
 Dady yace." Ai ka jawowa kanka tunda kai kace me kunnen k'ashi ne."
Cikin d'ari-d'ari Hajiya Asiya tace." Ayi hakuri Yallab'ai." Ko kallonta baiyi ba ya cigaba da girgiza k'afarsa guda.

Tsaye suke a harabar gurin suna shawarwarin me za suyi. Hakkim ya nufi gurin masu gadi jikinsa duk yayi sanyi fad’an Dady ta soma damunshi, Sam! bai saba ba.
Suna ganinshi ne suka nutsu nan ya k’arasa gami da mik’a musu hannu suka gaisa a mutunce. Sai ya rasa me zai ce.
D’aya daga cikinsu yace.” Akwai abunda za’ayi ne Oga.”? Girgiza kai yayi alamun a’a yace.” Tambayar ku kawai zanyi.”
Sukace Allah yasa mun sani.
“Wata yarinya siririya nake tambaya zaku ganta fara ‘yar fulani k’azama yarinyar bata da kintsi tana tafiya kamar mahaukaciya ko kun santa.”
Shuru sukayi na minti biyu daga bisani suka had’a baki gurin fad’in.” Gaskiya ba mu gane yarinyar ba domin kasan yaran K’auyan nan suna da yawa kuma dai duk haka d’abin ansu yake na rashin kintsi.”
Yusuf yace.” Ko d’azu ma ta wuce ta nan wajejen k’arfe goma na Safiya, ko gilmawarta baku gani ba.” ?
Nan suka ce Sam basu gane taba.
Cike da jin haushin su Hakkim ya futa waje yana kalle-kalle Yusuf yace.” Bari in d’auko mota mu nausa ciki ko za’a dace.”
Shiru yayi masa kawai ya soka hannuwansa duk biyun cikin aljuhu.

Yusuf ya futo da mota ya shiga suka kama nausa cikin karkarar ba tare da sun san ina zasu je ba.
Ganin mota tana shigowa ne yasa matasa da suke zaune Suna shan rake tsakiyar su futalar aci bal-bal ce sai hayaki take suna ta hira da shewa duk suka bi motar da kallo.
Yusuf yace.” Ina ganin mu tsaya mu tambayi matasan can.”
Parking yayi suka futo a tare matasan suka bisu da kallo. Cikin nutsuwa suka k’arasa kusa dasu duk suka basu hannu sukayi musabaha.
Yusuf yace.” Muna tambaya ne.” Sukaje Allah yasa mun sani.”
Shiru yayi domin ya rasa da yaya zaiyi kwatan Ladidi.
Hakkim yaja tsaki yace.’ Ka fara magana kuma kayi shiru, muna tambayar wata ibilishiyar yarinya a garin nan, ita ba mutum ba ita ba’ajana ba siririya tamkar tsolan rake, zaku ganta k’azama tana da manyan idanu.”
Shiru sukayi na minti biyu daga bisani sukace .”Gaskiya bamu gane taba, sai da Ku k’ara shiga cikin k’auyen ko za’a dace.”
Ko gama sauraransu baiyi ba yayi gaba ya bud’e mota ya shiga Yusuf ya biyo bayanshi shima duk ya sare da al’amarin. Har ya kunna mota zasu tafi, d’aya daga cikinsu ya taso da sauri yana fad’in.” Ku tsaya Ku tsaya.”
Hakkim yace.” Dallah ja mota mu tafi ya Wani taso yana mu tsaya mybe ma yayi mana shirme.”
Yusuf ya share shi kawai ya kashe mota, saurayin ya k’araso yana fad’in.” Ina kyautata zaton yarinyar da kuke magana akanta baza ta wuce Ladidi ba, domin duk siffofin daka fada ita take dasu.”
Yana daga cikin mota tace.” Shigo ka kaimu gidansu.”
Da sauri yaja baya cike da tsoro, chaiiiii! Akan me zai shiga motarsu ya sani ko ‘yan yankan kai ne, Karin abun damuwar ma Ladidi suke nema, tabbas yasan abun babbane.
Ina-inda ya fara da k’yar yace.” Yanzu dare yayi zani gurin iyalina,amma bari in yi muku kwatance.”
Yusuf yace.” Ok muna jinka.”

  "Idan kuka mike wannan hanyar zata kaiku har *Dausara* sai ku tsaya dai-dai majalisar Yahaya kuce ina ne gidan Iya Mai koko insha Allahu za a nuna muku nan ne gidansu Ladidi."
  Yusuf ya zura hannu a aljuhu ya Ciro gudar dubu daya ya mik'a masa, yana godiya, 
Da sauri ya karb'a yana zabga masa godiya
Motar yaja suka k'ara gaba.

D’alha da Yahaya na zaune a kan dakali suna hira Duk ‘yan majalisar sun tashi, nan D’alha ya samu damar fad’awa mak’ocinsa Yahaya abunda ya faru da Ladidi
Sosai Yahaya ya jimanta al’amarin yace.” Yanzu kana nufin jarin ka zaka rusa kan yarinyar nan D’alha ka k’yaleta kawai tunda tana ji kad’an kad’an sai nake ganin kamar wahalar da kanka zakayi kan hakan.’
Ajiyar zuciya D’alha ya sauke yace.” Wallahi Yahaya ina mutukar tausayin rayuwar Ladidi marainiya ce bata da uwa babu uba sam bata san su ba bata da gatan kowa sai ni sai Ubangiji kaga kuwa dole in tsaya kan lafiyarta domin nasan amana ce a hannuna.”
Yahaya yace.” Da ina da wasu kudi a aje dana ranta maka gaskiya bana so ka taba jarinka.”
“To yaya za’ayi insha Allahu zai farfad’o.”

Haske mota suka hango tun daga nesa yana haske su. Yahaya yace.” Baki mukayi daga burni kenan.’?
D’alha yace.” Da’alama dai.”
Ido suka zubawa motar har ta k’araso inda suke.
Yusuf yayi parking suka futo a tare. Suna isa kusa dasu suka mik’a musu hannu suka gaisa, Hakkim yace.” Da Allah muna neman majalisar Yahaya ne.”
D’alha yace.” Gatanan ga Yahaya nan yana jin ka.”
Yace.” Gidan Iya mai koko muke nema.”
Da hannu Yahaya ya nuna musu kofar gidan.
Hamdala Yusuf yayi yana jin farin ciki, yace.” Nan wata yarinya Ladidi take.”
Yahaya yace.” K’warai kuwa ince ko lafiya.”?
Hakkim ya juya ya da niyyar shiga mota a cikin zuciyarsa yace.” Tunda anga gidan kome me sauki ne, gwara inje in kwanta in huta ko na samu Dady ya k’yaleni.”
Bayani Yusuf ya tsaya yana musu Hakkim ya kunna Mota da k’arfi yake masa hon!!! Yusuf yace.” Kuyi hakuri Insha Allahu gobe zamu zo da safe kome ye sai ayi.” Yana gama maganar yaje ya bud’e mota ya shiga, Yusuf ya fige ta suka bar gurin.
Cikin takaici yace.” Duk wannan abun bazai kai maka ba, don ma ka samu ina taimaka maka na tabbata da kai kadai ne sai dai ka kwana a kauyen nan kana tambaya baka samu ba, shine kake k’okarin tafiya ka barni. “
Shiru yayi masa yana draving, Yusuf ya dunga masa mita hat suka Isa masaukinsu.

COMMENT VOTE AND SHARE
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????22

Motar su na barin gurin. D’alha ya mik’a da niyar shiga gida yana mik’awa Yahaya hannu sukayi sallama kowa ya shiga gida.

 Cikin bacci taji kamar murya D'alha yana tashin ta, ta mike zauna tana gyara d'aurin dankwalinta. Hasken Fitilar kwai ta karo tace." Lafiya kake tashina bacci na yayi nisa wallahi."

 D'alha ya zauna gefen katifar da take zaune yace." Wasu mutane ne suka zo yanzu, wai suna Neman Ladidi."

 Bude ido tayi sosai gabanta na fad'uwa tace." Wace Ladidi kuma,wacce yinin yau bata futa ba balle ace tayi Wani Abu."

 Kwantar da hankalin ki Iya suma basu ce tayi komai ba, sun dai ga gidan sun ce gobe zasu dawo da safe."
 Iya tayi jigum! Tana kallon Ladidi dake shararar baccinta tace." Kaganta nan ta sha wahala kafin bacci ya d'auke ta, motsi kad'an sai tace kunnenta."

 D'alha yace." Da'alama ai kunnen ba k'aramin bugu akayi masa ba."

 Iya ta share hawaye cike da tausayin jikar tata tace." Ko waye wannan ba k'aramin azzalimi bane wallahi. "

 Shiru D'alha yayi domin baya so ya tanka maganar yasan laifin Ladidin ne.

Mik'ewa yayi yana mata sallama, har zai futa ta tsayar dashi tana cewa." Kace gobe babu koko ko."?

“Eh kin san zamu futa da safe sosai domin mu kama layi,sai dai hanzari ba gudu ba, mutanan da zasu zo.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button