LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

Yusuf ya mike zaune yana fad’in “Na daina ni da da nake so gobe ma ka rakani gurin ta””” tab’e baki yayi yana fad’in”Sai dai ka bari sai na dawo domin zan tafi Hutu ne”?
“Ina zakaje Hutu kaji d’an iska”” Hakkim yayi wani k’ayattacen murmushi yana fad’in “Kano zani Dady yayi gidan gona wani k’auye shine nake ta zumud’i””” Yusuf yace”A’a kace zamu huta yaushe zamu tafi”? Kallonsa yayi yana fad’in “Zakaje ne”? Gyad’a kai yayi yace” K’warai kuwa””” kashewa sukayi suna dariya yace”Gobe nake so mu tafi”” Yusuf yace “Yayi Allah ya kaimu”.
COMMENT VOTE AND SHARE
[9/28, 10:16 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????LADIDI????????????
????♀????♀????♀K’WADAGA????♀????♀????♀
NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}
ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????
We are here to educate motivate and entertain aur reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
Ayi hakuri errow⚠⚠
????11
Cikin kyakyawan shiri ya futo daga part dinsa , kai tsaye part d’in Mama ya nufa cikin nutsuwa yayi sallama, Mama da mai aikin ta Jummai suna tsaye suna shirya daining ta amsa fuska a sake take fad’in “Har ka shirya kenan”? K’araso wa yayi inda suke, da murmushi a fuskarsa yace” Tuntuni na shirya yanzu ma Yusuf nake jira,banason tafiyar rana” Mama tace”Yusuf ma zashi ne”? Zama yayi kan daya daga cikin kujerun cin abunci yana fad’in”Jiya daga ji ina zancan yace shima zashi” Salima dake zaune can falo tace”Babban yaya nima zani don Allah” hararata yayi yace”Babu inda zani dake” Mama tace.”Kai kuwa kaje da ita mana dama sunyi Hutu”. Yace. “Mama kin san ko kwana zamuyi kuwa”? Girgiza kai tayi tana fad’in” Sai ka fad’a”. “Sati biyu zamuyi fa” Mama tace”To meye a ciki ka tafi da ita kawai” shiru yayi baya son musu da Maman shi, Gen.Abbas ne yake saukowa daga bene yana sanye da jallabiyya ruwan toka hannunsa rike da Jarida ta Daily trus, idonsa farin galashi ne, zama yayi suna gaisawa Mama ta fara had’a musu Kalaci, bayan sun kammala Hakkim yace.”Dady na fa shirya” Gen. Yace. Na gani ai daga dawo wa zaka k’ara tafiya jiya munyi waya da masu aikin komai ya kammala, mybe yau zasu bar gurin amma dai na fada musu su zauna sai kazo”. Yace. “Dady yanzu ma Yusuf nake jira tare zamu tafi”. Salima ce ta futo cikin shiri sai murna take hannuta rike da trolly d’inta ya loda uban kaya, Dady yace.” Ke kuma fa”? Narai-narai tayi da ido, Mama tayi saurin cewa”Tare zasu tafi” .”Shine ta lodo kaya Cikin jaka kamar wacce zata bar gari” tsuro-tsuru tayi, Hakkim ya buga mata tsawa! Tare da fad’in”Maza je ki rage kayan nan idan ba haka ba wallahi inki zuwa dake”. Da gudu ta koma dakinta
Ihun!! Ladidi ne ya cika gidan,inda har daga waje ma ana jinta, sai zageye tsargidan take tana buga tsalle Mai koko na bin ta sai ta kamata,hannuta rike da sabuwar reza cikin takardar ta,fad’i take” Baki tsaya ba ko Ladidi ki daina wahalar dani, gwara ki tsaya a aske miki gashin kema kya huta da wannan azababbiyar kwarkwatar da ta dame ki”. Ladidi tace”Wallahi ba zaki min aski ba,haka kurum sai kice sai kin aske min gashi ne,ina ruwanki da kwarkwatata ki bar min kayata mana, Mai koko tayi kanta da sauri zata damk’e ta, ta buga wani uban tsalle! Sai gata ta tsallake rijiya da baya!! A gigice Mai koko take salati, babu shiri taje ta aje rezar tana fad’in”Kinga na aje rezar futo daga bayan rijiyar Ladidi”mak’e kafad’a tayi tana fad’in”Wato in futo ki kamani,wallahi na gadama sai in fada rijayar ma” Sanin rashin hankali da gab’unta na Ladidi yasa Mai koko ta fara rarrashin ta da dadad’an kalamai, tace.”Kinga d’azu munyi magana da Mairo mai dashi cewar zata bani d’auka ta uku shine nace da ta bani zan shiga kasuwar burni na siyo miki kayan kallo” Ladidi tasa dariya tana fad’in”Nagane wayo zakiyi min, ni sai na fad’a a rijayar ma” tayi taga-taga!! Kamar zata fad’a!Mai koko ta rafka salati zaninta na k’okarin fad’uwa tayi waje da sauri ko ina zata oho”! Dariya Ladidi take mata, ta buga tsalle ta futo daga bayan rijiyar, can wani guri da ya rushe Cikin gidan taje ta b’oya dake tunda gurin ya rushe babu mai zuwa gurin,Mai koko ta dawo ciki tare da wasu mutane biyu ita a nufinta su taya ta bawa Ladidi hakuri, wayam! Babu ita a gurin, Wani irin salati Mai koko ta kurma tayi bakin rijiyar gadan-gadan tana fad’in”Shikkenan ta fad’a cikin rijiya dama nasan Halin ladidi kome tace zatayi sai tayi, kuka ta farayi tana kara zura kanta cikin rijiyar, sai akayi sa’a tarwad’ar dake cikin rijiyar suka dunga motsi a ciki, kuka sosai Mai koko take tana fyace majina tace”Kunyi tsaye meye amfanin ku, kuzo Ku shiga Ku d’auko ta,Idan ma mutuwa zatayi ta mutu a gabana”
Kallon juna sukayi suka kama hanya futa suna fad’in”A’a Mai koko bari dai mu garzaya mu kira miki sarkin ruwa, wannan yarinyar me k’wamk’wamai watak’ila ma su suka jata ta fad’a ciki, haka kawai mu shiga su kama mu, domin ita suna iya sakin ta, tunda tasu CE”Mai koko ta saki baki har suka fuce. Suna futa d’aya yace.”Allah yasa ma su kaita bakin ruwa su d’auke kayan su kowa ya huta da masifa”.
Mai koko ta lek’a rijayar tana fad’in”Mai yasa zakiyi min haka Aminatu mai yasa zakiyi min ke kad’ai nake kallo a matsayin Aminu shine zaki fad’a rijiya Haba Ladidiya kiyi hakuri da halina da halin Kawun ki, majina ta fyace! da gefen zaninta sai zura kanta take cikin rijar tana sambatu! Ladidi ta lek’o daga kanta ta wata ‘yar kafa sai dariya take yiwa Mai koko ganin yadda take kuka tana fyace majina dariya har sai da ta kwanta.
Kafin kace kwabo labari ya bazu a cikin unguwar Ladidi ta fad’a rijiya wasu suyi jaje wasu suyi ko murna suke cewar an rage mugun iri, D’alha na gurin sana’ar sa labari ya riske shi, babu shiri ya tawo gida ko kayan sana’ar bai d’auko ba, Mai koko kuwa ganin kamar tana son fad’awa cikin rijiyar yasa mak’otan ta suka nufi gudansu da ita sai sambatu take, hakan ya bawa Ladidi damar futowa daga mab’oyar ta tayi waje a guje! Kanta ko d’ankwali babu,wani abun mamaki da al’ajabi idan ka kalli gashin nata sai ya baka tsoro domin Duk ya dunk’ule ya cure guri guda yayi wata muguwar dauda ga tsakin kwarkwata da amosani man burjiki! Wani gurin sal-sal babu d’igon Gashi wani gurin da akwai, ita kanta idan tana sosawa ciro gashin take da hannunta ta yar. Ni kaina sai da nace Ladidi da kin sani kin bari anyi miki aski domin shine mafuta a gare ki
Can hanyar titi ta nufa tana fafara gudu kamar mahaukaciya, ko da wasa babu wanda ya ga gilmawar ta.
Sarkin ruwa tare da jama’ar gari suka shiga cikin gidan, jin ance ga Sarkin ruwa nan yazo yasa Mai koko futowa daga gidan da take da sauri duk tayi wujuga-wujuga, suka had’u da D’alha sai gumi yake zabgawa babu wanda yace da Dan uwa sa komai suka afka cikin gidan, To duk iya lalube Sarkin ruwa yayi amma bai ga Ladidi ba kusan awarsa guda a cikin ruwa ya futo yana fad’in”Da Ladidi tana cikin rijiyar nan to ko da na ganta domin na baje basira ta sak’o da loko, kogo da kogona babu inda ban duba bata ciki”. Guri yayi Tsitt!! D’ai-d’ai jama’a suka fara futa suna surutu cewar “dama tuntuni suna zargin yarinyar ” yar ruwa ce to gwara da suka d’auke kayansu kowa ya huta.