LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

Alhmdullahi jiki yayi sauk’i
Gaskiya naji dad’i sosai da kularwar ku akaina nagode masu kirana a waya kuna yimin ya jiki da fatan samu lafiya,masu min sannu ta pravite wanda na sani da wanda ban sani ba nagode sosai da sosai ina muku fatan alkairi
Jan kunne⚠
Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin book d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ ki siyar min da littafi ba da sanina ba, Wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan haka, hattara dai!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje yaci gumin sa, kane mi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????13
Cikin sauri Yusuf ya k’araso gurin da Ladidi take kwance, ya bud’e ruwan,ya fara zuba mata a fuskar ta furgice! ta mik’e zaune ta k’wala k’ara! Waige-waige take tana neman Hakkim a gurin, Salima ta rik’e hannunta tana son tayi mata magana. Fuzge hannunta tayi da sauri ta mik’e tsaye tana fad’in” Yana ina.”? Duk suka mik’e suna kallonta, Yusuf yace.” Ke yarinya me ya shigo dake gurin nan?,da har kika jawo wa kanki suma.” Banza kallo tayi masa ta murgud’a bakinta, bata ce masa komai ba, ta bar gurin bagazan-bagazan! kallo suka bita dashi, Yusuf ya kalli Salima yace.” Anya kuwa yarinyar nan me lafiya ce”? Salima ta k’unshe dariya tace.” Lafiyan ta lau. Kamar ka manta da a k’auye kake dole kaga haka.” Yusuf ya girgiza kai yace.” Ni abunda ya bani mamaki da ita shine yadda ta shigo gurin nan wallahi”. “Gaskiya nima nayi mamaki.” Salima tafad’a yayin da suke k’okarin futa dafa gurin.
Ta inda ta shiga gurin tanan ta haura ta futa Hakkim na kallonta tun futowar ta har lokacin da take haure katangar yana gani, zuciyar sa yana mamakin ibilicin yarinyar, yau d’in nan zai sanya a kewaye katangar gurin, da waya mai k’ayoyi, duk saboda ita dole kuma a zuba masu gadi a gurin. tuni ya cire kayan da ta b’ata masa ya watsar dasu harabar gurin, domin mugun k’yamk’yami ne dashi, idan ya tuno halittar yarinyar sai yaji zuciyarsa tana wani irin tashi! sosai zuciyar sa take masa zafi, tunda yake a rayuwarsa babu wanda ya tab’ai masa irin abunda yarinyar tayi masa dole ne ya d’auki mataki akanta mutukar ya kara ganin k’afarta a gidan, karya ta zaiyi kawai kowa ya huta. Su Yusuf suka k’araso gurinshi ya sha kunnu domin baya son ma yayi masa maganar, Simi-simi Salima ta shiga ciki, Yusuf ya samu kujera ya zauna yana kallon Hakkim d’in, da yake k’ara yin kicin-kicin da fuska, yace.” Zauna zamuyi magana da kai”. A fusace! Ya juyo yana fad’in”Ubana ne kai zaka bani umarni”. Yusuf ya kalleshi , da alama zuciyar sa har yanzu batayi sanyi ba. Yace.” A’a ba ubanka bane”. “To ka fad’i duk abunda zaka fad’a kunne na yana ji”. Ya k’arashe maganar yana juya masa baya. Yusuf ya mik’e ya k’arasa inda yake, kafad’arsa ya dafa cikin taushin murya yace.” Aboki wai me ya faru tsakanin ka da yarinyar nan? Wallahi hankalina ya tashi sosai domin ta dad’e kafin ta farfad’o,haka kurum daga zuwanmu guri zakayi kisan kai saboda zafin zuciya”. Hakkim ya juyo yana fuskantar sa, cikin kaushin murya ya fara fad’a masa abunda ya faru. Yusuf ya sauke ajiyar zuciya yace.” Gaskiya kam yarinyar ba tayi maka dai-dai ba,amma kai ma bai kamata kayi mata irin wannan dukan ba,saboda yadda na lura da ita kamar irin yaran nan masu lalurar k’wak’walwa kasan k’auye ko d’ansu na cuta basa mai da hankali sai abu yayi tsanani, sannan zaka gansu sun nufi asibiti hankali a tashe.” Zuciyarsa ce fara sanyi ya zauna kan kujera guda Yusuf ma ya zauna kusa dashi, yace.” Ka bari kawai Yaro wallahi zuciyata a lokacin ji nake tamkar na kashe ta na huta da b’akin ciki.” “Kayi hakuri don Allah ka rage zafin zuciya.” Yusuf yafad’a yana dukan kafad’unsa.
Salima ya k’walawa kira, tana can ta shagala da kallon yadda aka tsara falo da kayan jin dad’i da more rayuwa, har ta kunna kallo tanayi taji kiran big broth amsawa tayi ta mik’e da sauri, tana zuwa yace.” Ki shiga kchin kiyi mana abunci.” “Angama big broth” tafad’a cike da bin umarni, kai tsaye kichin d’in ta nufa, gashinan komai akwai na amfani nan take ta fara aikinta.
To can gidan su Ladidiya kuwa Mai koko ta saddak’ar ta fawwala wa Allah cewar Ladidi ta mutu cikin rijiyar don haka mutane sun cika gidan ana yi mata ta’aziyya, Jama’a sun kewaye ta, tana zaune da carbi a hannu ga idonta yayi jajazur! taci kuka ta k’oshi, D’alha na waje da mutane zazzaune kan tabarma, sam yak’i yadda cewar Ladidiya ta mutu cikin rijiya k’wak’walwar sa tafi tunanin yarinyar tana can gurin gantalin ta, shiyasa ya kasa zaune ya kasa tsaye sai zurga-zurga yake a gurin. Duk Wanda yazo gurin sai ya hau yi masa gaisuwa, ko kallon su baya yi
Tafiya take fakam-fakam!! sak’e-sak’e kawai take a zuciyarta da tunanin d’aukar fansa kan, d’an burni,sunan da ta sama sa kenan, wallahi bai dake ta a banza,sai ta rama duk hanyar da zata bi ta sani, leb’anta ta tab’a da hannunta, cire hannuta tayi tana girgiza kai! a fili tace.”Wallahi he na rama idan ubanka ne shugaban k’asa he na rama, nima sai na fasa maka baki,hummm!! Zaka san ka tab’o Ladidi jikar Mai koko, bana barin takwana kuma bana manta ranar d’aukar fansa.” Da tafiyar ta ya gane i tace jiki na rawa ya k’wala mata kira,”Ladidi” da sauri ta juyo tana waigen idan taji ana kiranta. Kakanta ne D’an fulani, yake tawo wa inda take, yana can gurin kiwo labari ya same shi na mutuwar ta,shine ya tawo cikin tashin hankali! Abun mamaki kuma sai gashi ya ganta a hanya, yana k’arasowa inda take ya damk’i hannuta, bai ce mata komai ba suka fara tafiya, zub’uro baki tayi tace.” Ni ka sake ni ka rik’e min hannu da k’arfi ai gida zani ba wani guri ba.” D’an Fulani yayi mata shiru, shi dai k’okarin shi kawai yaga ya danganata da gida,hankalin kowa ya kwanta. Tun daga nesa jama’ar dake gurin suka hango tawowar su, sai aka fara kallon-kallo tsakanin su, da suka tabbatar da cewar itace sai kowa ya fara zura silafas d’insa yana guduwa, D’alha ya juya yaga wayam! babu kowa a gurin, girgiza kai kurum yayi yana jin wani d’aci cikin zuciyarsa wato Ladidi ta zama abun tsoro kenan? D’an Fulani ya d’amk’ata a hannunsa yana fad’in”Gatanan can wajejan titi na gano ta tana tafiya ita kad’ai.” D’alha ya sauke ajiyar zuciya yace.”Alhamdullahi, dama ni jiki na bani yarinyar nan tana raye,amma jama’ar gari suna ta fad’in ta mutu a cikin ruwa,Allah nagode maka daka bayyana mana ita ko hankalin Mai koko ya kwanta.” Sai sanan Ladidi ta tuna da abunda ya faru d’azu tsakaninta da Mai koko, dariya ta kece dashi,hahahaha! D’alha ya gaura mata mari! Yana fad’in”Rufe miki don buhun ubanki, shashasha, shakatafe, naga ranar da zakiyi hankali dai” D’an Fulani kuwa a’lamarin Ladidi ya fara bashi tsoro,don haka yace.”D’alha mu shiga cikin gidan sai mu San abun yi.” Kai tsaye cikin gidan suka shiga.
Tofaa ko ya zata kasance idan jama’ar gidan sukaga Ladidi Wanda suka dauka ta mutu cikin rijiya,ko yaya Mai koko zatayi in taga Ladidi? To Ku cigaba da bina dai cikin labarin domin in warware muku
COMMENT VOTE AND SHARE
[10/2, 5:54 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????LADIDI????????????
????♀????♀????♀K’WADAGA????♀????♀????♀