LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

????15
Mai koko tace.” To kinji inda maganar take, don haka sai kiyi hak’uri kinji da kunnen ki,wanda ya aske miki kanki.” D’alha ya kalle ta cikin taikaci ya buga mata tsawa tare da fad’in.”Rufe min baki ko inzo k’ara fasa miki shi,shashasha kawai!! Gum! tayi da bakin ta dama kukan babu hawaye sai dai ihu! Sai dai kana kallon idonta kasan tana cikin b’acin rai! Yarinya ‘yar shekara goma sha biyu ta san d’aukar fansa, abunda take ta raya wa kenan cikin zuciyar ta Kawunta da d’an burni sai ta rama abunda sukayi mata. Mai koko ta kalleta ganin yadda take ta sauke ajiyar zuciya yasa ta sassauta murya tace.” Yanzu ke kanki zaki ji dad’i kuma iska zata shiga kanki sosai kinga kin rabu da kwarkwata har abada,domin wani sabon gashi ne zai futo miki.” Banza tayi mata. Kawu D’alha ya futa ya barsu a d’akin, Mai koko dai da taga tak’i kulata sai ta futa ta k’yaleta tana addu’ar kat Allah yasa ta b’ullo da wani abun kuma. Aikuwa futowa tayi babu d’ankwali a kanta nufi gidin rijiya, ‘yan siyan koko suka bita da kallo, tuni wasu daga cikinsu suka fara futa waje cikin tsoro ganin kan Ladidi a cikin rana sai k’yalli yake, Mai koko tace.” Ya kuke futa kuma kowa ya tsaya a sallame shi.” Wani Yaro yace.” Iya wacece wacan kamar Ladidiya ko.” Iya ta kalli inda Yaron yake nunawa Ladidi ta gani da buta a hannu tana durzar bakin ta da dakakkaken gawayi kanta sai k’yalli yake cikin hasken ranar da ya fara futowa, cikin takaici tace.” Ladidi ke ko kika futo babu Dan kwali ko kunyar k’awayen ki baza kyaji, ki koma ki dauro dan kwalin ki.” Kuskure bakinta tayi tace.” Daga yau na bar d’aura d’ankwali wallahi haka zan dinga yawo da kai na, kuma duk yaron da ya tsokane ni, inci Ubansa.” Jiki a sanyaye Mai koko ta juya ta cigaba da abunda take cikin zuciyar ta take fad’in”Ba a rabu da bukar ba an haifi Habu,dama ni nasan wata futunar zata k’ara b’ullo da ita.”
Tana gama Alwalar ta bar gurin. Wani tsohon buhu ta kwance nan kayan ta na sawa suke ta ciro wata doguwar riga irin ta kanti duk taji jiki dan wani gurin ma d’inkin ya soma zarewa gashi ta tattare sosai ta d’angale mata duk k’waurinta a waje ta saka, ta zura hijabin da take sallah ta tayar da sallah.Bayan ta idar ta tub’e hijab d’in ta aje shi kan gado, haka ta futo babu d’ankwali kai tsaye hanyar futa ta nufa, tunda ta doso gurin suka fara matsawa kowa na k’okarin ya bata hanya kar ta make shi, ball tayi da kofin Alawiyya dake bisa layi, Iya ta juyo da sauri tana fad’in.” Kar Ku har gitsa layin fa.’ Ladidi ta gani tana k’okarin futa,da sauri tace.” Ina zakije a haka sai da nace ki d’aure kanki ke ku kunya ba kya ji.” Ko kallonta ba tayi ba ta fuce abunta,girgiza kai kurum tayi ta cigaba da aikin ta tan addu’ar Allah yasa Kawunta na waje ya koro ta, aikuwa D’alha na tsaye da kayan sana’arshi suna gaisawa da mak’ocin su Yahaya,suka had’a ido dashi, sam bata tsorata ba. Ta fara k’okarin wuce shi,tsawa ya buga mata yana fad’in”Koma ki d’auro d’an kwallinki” Ido jazur! Ta koma ta cikin gidan, D’alha yayi sallama da Yahaya ya kama hanya ya tafi, lab’ewa tayi bayan k’yaure sai da ta tabbatar da yayi nisa sannan ta futo, tana ganin Yahaya yana gyara kwatar gidansa, ta galla masa harara, yana sunkuye bai sai abunda take ba, sai saukar Abu yaji a jikinsa, da sauri ya dago yana karkad’ewa sai ga tarkacan da ya kwaso daga kwata suna fad’owa k’asa, bayan rigarsa duk ya b’aci da kwata, waige-waige yake yana neman yaron da yayi masa wannan sha’ani, ido hud’u sukayi da ita, zabura! Yayi ya matsa gefe guda baki na rawa yace.” Lad..ladid..katsaye shi tayi ta hanyar fad’in” Jiya har da kai gurin cewa na mutu har kuna shimfid’a tabarma da zama, to ban mutu, kuma duk sai na kashe Ku.” Cikin Yahaya ya bada sautin kulululu!! Bakin sa sai motsi yake, zare masa manyan idonta tayi, ganin yanda yake gumi! ne yasa ta k’yalk’ale da dariya “hahahahahaaaa! fyallawa tayi da gudu ta barshi tsaye a gurin,saura kad’an ya saki futsari.
Cikin mutuwar jiki ya zauna kan dakalin gidansa yana sauke ajiyar zuciya,sai zare ido yake.
Babu inda tayiwa tsinke sai gidan gonar su Hakkim, tana isa ta tarar da an kewaye katangar da waya mai fasa k’afafu dan wani gurin ma har da k’ananun k’walabe, b’uya tayi wani gurin tana tunanin ya za’ayi ta shiga gurin. Can taji motsi an bude kofa, lek’awa tayi kad’an , d’an burni ta hango ya futo daga ciki jikinsa sanye da singlet da wando iya gwiwa 3quetar, suna magana da wani me wanki takalmi, tsura masa Ido tayi tana girgiza kai, a fili tace.” Wannan girman jikin naka da wannan k’wanjin naka da wannan murd’ewar taka, duk baza su hanani in d’auki fansa akanka ba, hummm! Ko Kaine Singam gurin k’arfi sai na rama fasa min bakina da kayi.” Tana kallonshi suka gama magana da me gyaran takalman ya koma ciki ba tare da kulle k’aramar kofar ba. Da sauri ta futo daga gurin b’uyan ta, kamar walkiya tazo ta shige ciki, Mai gadi nacan na fama da redi’o a hannu, wata bukka ta shiga ta b’uya Kansan kujerun hutawar dake ciki, tana kallonshi ya futo daga wani d’aki hannunsa ruk’e da takalma biyu ya kara futa waje, wuf! Ta futo daga farko inda take, ta afka inda taga ya futo, Sam had’uwar falon ba ya gabanta burinta kawai ta d’auki fansa, ba ta tsaya kalle kalle ba ta afka wani d’aki da tagani a bude, tana shiga ta fara zare ido motsin ruwa taji a band’aki, da sauri ta matse jikinta ta b’uya bayan gado. dama kar ku manta Ladidi bata da k’iba siririya ce sosai, Yusuf ya futo daga toilet yana goge jikinsa da towol, sauri sauri ya sanya kayansa. Ya tsaya gaban mirror yana shafa mai ajikinsa, Hakkim ya shigo d’akin hannunsa rike da takalman su an wanke su tas sai kyalli suke, Yusuf yace.” Ka dame ni na tashi na shirya gashinan dai na shirya sai kayi sauri kaima.” Zube takalman yayi a gefe guda, toilet ya nufa yana fad’in” Yanda kake da nauyin bacci idan ba haka nayi maka ba ai baza ka tashi ba.” Yusuf yace.” Son bacci da nauyin bacci har na kai ka.” Shiru yayi masa ya shiga toilet din, shi kuma yana gama abunda yake ya futa farlor, Ladidi duk tana jinsu, tasan Hakkim ne ya shiga band’aki, futowa tayi daga inda take, ta zauna gefan gadon gami da tsurawa kofar band’ankin ido tana dakon futowar sa. Jikinsa d’aure da guntun towol ya futo cin yoyinsa duk a waje domin babu gajeran wando,a jikinsa dama da k’yar towol d’in ya ratsa masa jiki, yana futowa idonsa ya sauka a nata, tana zaune ta d’ora kafa d’aya kan d’aya, kanta sai k’yalli yake, sam! Bai gane ta ba, domin duk hattun ta sun sauya. Da k’arfi! Yace.” Auzibillahi minashaid’anirrajim”!!!! Nan take ya fara karantun ayatul kursiyo, har yanzu idonsa na kallonta itama ta k’ura masa ido k’urrrr!!
COMMENT VOTE AND SHARE
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????LADIDI????????????
????♀????♀????♀K’WADAGA????♀????♀????♀
~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}
ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????
We are here to educate motivate and entertain our reades
JAN KUNNE⚠
Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.