LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

Ladidi kuwa tunda ta samu ta d’auki fansar abunda Dan burni yayi mata sai kawai ta manta dashi da al’amuran shi ta cigaba da sabgarta.
Tafe take fakam-fakam da allo a hannunta ta cire d’ankwalin ta taci Uwar d’ammara dashi, tana sane ta cire ko wani zai tsokane ta ta samu na duka, bayan haka kuma tana so ta b’akantawa Kawun ta D’alha rai tunda ta lura baya so ya ga tana yawo babu d’ankwali, shi kanshi hijab dinta na hannuta, karo suka ci da Iliya dai-dai wani lungu,
Tun daga nesa yake k’unshe dariya, har ya k’araso daf da ita, taki kaucewa tamkar zasu bangaji juna, Iliya ya sha kunu ya d’an kauce mata tazo ta wuce, shima kamar zai wuce sai ya tsaya ya mik’a hannusa ya daki! kanta sosai yace.’ Woooo k’waryar malo dama a namiji aka hallice ki domin kin fi kyau da maza!yana gama fad’ar haka ya runtuma da gudu yana dariya, aikuwa a sittin! Ta bishi da wani irin mugun gudu kamar zata tashi sama, yana gudu yana waiwayen ta,ganin ta kusa cimma sa yasa ya kara k’aimi!wani irin tsalle me had’e da gudu ta buga sai gata a gabansa,ba tayi wata-wata ba ta zura k’afarta k’arkashin tasa ta tad’o shi ya fad’i wanwar a gurin, ya yunk’ura zai mik’e, da sauri ta d’ebi k’asar gurin ta watsa masa a fuska, aikuwa ya saka ihu! Yana rintse idonsa, kamar walkiya ta bar gurin. Iliya ya dinga lalube yana ihu gami da mutsika idanunwansa k’asa sai gurin-gurin take masa a ciki ruwa ne kawai yake shatata da k’yar ya mike ya fara tafiya, aikuwa ya jishi cikin kwata tsumbul, yayi zaman ‘yan bori, ya dinga salati yana neman d’auki.
Yau kwanan so biyar a garin d’an kunkuru Hakkim ya warke tsaf, kullum cikin zuba ido yake yaga ko Ladidi zata kara dawo wa, shiru safe da yamma sai sun futa ganin gari cikin mota, ya dinga kalle-kalle kenan ko zai ganta babu alamunta, cikin zuciyarsa shi kadai yasan irin tanadin da yayi mata, Labarin abunda ya faru kuwa har su Dady sun sani domin Salima ta fada musu komai, Dady ya kira shi a waya tare masa fad’a kan ya kula kar ya k’ara dukan yarinyar kowa a garin shi kam baya son tashin hankali, amma ya Dade da sanin halin dashi mafad’aci ne sosai idan aka tab’o shi, tun yana yaro haka yake,amma fa in baka tab’o shi ba zaka jima dashi kuna mu’amula domin yana da saukin kai. Duk wannan gargad’in da Dady yayi masa yaji ne kawai amma yanda yaci alwashi kan yarinyar yana gani in bai dauki fansa a kanta ba ma kamar ya aikata zunubi ne.
Yau Juma’a tun sassafe Mai koko ta tsaya kan Ladidi sai da taga tayi Wanka tas sannan ta k’yaleta ta shiga sabgogina, tana zaune tsakar gida, sanye da atamfa nicham jajazur da ita,ta sallahr ta ce ta bara,dinkin riga da zani ne da d’ankwali, tayi kwaliyya rabazau a fuskarta da d’ige-d’ige inda ta labta Jan jan baki a leb’anta da kan hancin ta saman idonta da girar ta, Mai koko ta k’araso gurin da Murmushi a fuskarta tace.” Ko kefa Jikar Mai koko Ladidiya matar gwamna da shugaban k’asa,Ladidiya matar sarakai da Alhazai Ladidi matar masu mulki, kinyi kyau sosai, ki dinga tsafta kina wanka ki nutsu kinga kin fara girma wai baki ga kirjin ki bane har kin fara k’irgan dangi.”? ta k’arashe maganar tana ‘yar dariya.
K’irjinta ta kalla jin abunda Iya tace zumb’ura baki tayi ta cigaba da goga jar hodar ta,a fuska.Mai koko tace.” Hodar ta isa haka ai kar tayi miki yawa.” Aje abun shafar tayi tace.” Dandali zamu je yau akwai gad’a kuma kin san nice shugaba.” Mai koko tace.” To babu laifi, amma idan kin je don Allah ki nutsu kar ki shirme banda fad’a da maza ki kama kanki kinji ko.” Tab’e baki tayi tace.” Nifa Iya kin san duk wanda ya takale ni mace ko namiji babba ko yaro sai na rama ehee.” Iya tace.” To naji ai duk Wanda bai kula ki ba babu ruwan ki dashi.” Gyad’a Kai tayi ta mike tsaye tana warware wani mayafin ta me kama da abun tata, sai uban k’yalli yake wani har yana zuba a k’asa, k’okarin d’aura k’ugunta take dashi, Mai koko tace.” A’a ke da zaki yafa kuma kyayi d’amara dashi.” ” Ni dai k’yale ni nafi son haka.” Tafad’a tana zura silifas dinta sabo dal dashi,da alama yau zata fara sawa. Mai koko tace.” To sai an dawo kar kiyi dare.” Uffan bata ce ba takama hanyar futa fakam-fakam zanin jikinta sai harde ta yake, tana futa waje ta kwance shi ta jashi sama sosai duk k’waurin ta a waje, ta fi jin dadin tafiya a haka.
Har ta nufi hanyar Dandali sai ta fasa ta nufi hanyar titi.
Cikin kyakyawan shiri suka futo duk su ukun Salima sai washe baki take yau zata koma gida, shima Yusuf murna yake saboda yayi kewar sweetyn shi kullum suna mak’ale a waye tana masa mita.
Shi ko gogon naku cikin b’acin rai yake,gashi har sun gama hutun su zasu koma bai ga al’janar yarinyar nan, balle ya dauki fansar abunda tayi masa,motsi kad’an zai buga musu tsawa kamar wani ubansu Yusuf har ya gaji ya fara mayar masa da martani,sai da suka kusa yin fada da juna, yana huci ya bude mota ya shiga suka shiga suma,da gudu ya figeta suka futa daga gidan, kasancewar hanyar babu kyau kafin a futa titi yasa tayar su tayi faci, cikin jin haushi Yusuf yace.” Gashi nan garin zagin zuciya ka satar mana da taya sai ka futa ka d’aura mana wata.” Yace.” Sai dai in kai ka futa ka d’aura wallahi.” Sanin halinsa na taurin kai yasa ya bude motar ya futa. Yana dubawa yaga babu wata spire yace.” Babu wata fa.” Gabansa ne ya fad’i jin abunda Yusuf yace futowa yayi yana tunanin yaya za’ayi, Yusuf yace
” Dole a futa bakin titi a siyo wata bari inje da kaina. “. Daga masa kai kurum yayi, Yusuf ya kama hanya tafi.
Bayan tafiyar Yusuf da kamar minti goma Ladidi ta bayyana a gurin.
COMMENT VOTE AND SHARE
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????LADIDI????????????
????♀????♀????♀K’WADAGA????♀????♀????♀
~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}
ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????
We are here to educate motivate and entertain our reades
JAN KUNNE⚠
Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????18
Kanshi a k’asa ya dinga jin alamun tafiya, a nutse ya d’ago kanshi, suka had’a ido da ita ta kusa k’arasowa inda yake tsaye, wannan karon ma bai gane taba saboda kwalliyar da tayiwa fuskarta, kauda kansa kurum yayi, ita kam Ladidi ta gane shi sosai, wuce shi tayi, sai kuma ta dawo da baya, ta d’an tsaya nesa dashi, tace.” Kai d’an burni.” Da sauri ya d’ago kansa jin muryar yarinyar da yake nema ruwa a jallo. aikuwa k’wayar idonta ya kalla ya gane itace, fuskarsa ta rikid’e tayi murtuk kam bai tab’a dariya ba tunda Allah ya hallice shi, kanta yayi da sauri! tana tsaye tana jiran isowarsa tana dariya kamar mahaukaciya, tana ganin ya kusa k’arasowa gurin ta sunkuya ta d’ibi k’asar gurin ta watsa masa a fuska tana shek’a dariya fad’i take” Zo ka kamani ka gani in zaka iya, hahahahaha.” Hakkim yaji shigar yashi idonsa sosai bai damu ba, cikin wata irin zuciya ya kai hannunsa zai mare ta ta sunkuya tana dariya,ya mari iska! cikin rashin imani! Ya kwarfo k’afafunta duk biyun, ta zube a gurin,yunk’urin mik’ewa take ranta a b’ace yayi saurin take mata k’afa guda ya dinga murzata da takalmin shi sawu ciki, ihu!! Ta kurma tafa d’ura masa ashar! ya daki! Bakinta da gwiwar hannusa, kafin kwace kwabo bakin ya fashe, hannunsa guda ya sa ya d’ago ta, ta rike hannunsa tana cizo,ko a jikinsa, ya shak’e mata wuya sosai! Suka fara kallon-kallon ita dashi, idonta yayi bala’in ja na azaba! Shims nasa idon sunyi jajazur! Ko da yake dama tunda suka futo haka nasa yake, a zafafe! Yace.” Ke dan ubanki ya sunanki.”? Cikin shak’ewar nuffashi tace.” Ba dai Ubana wallahi meye ruwanka da sanin sunana,kuma zaka san ni ka Mara.” Yace.” Sai dai uban wa.”. Ko nuffasa bata bari yayi ba tace.” Sai dai ubanka.” Murmushi yayi kana ganinsa kasan zaiyi mugunta, sakin ta yayi ta fad’i gurin tana mai da nuffashi, ta zabura zata mike yq maida kafarsa kan tata, blet din jikin shi ya Ciro, ya fara lafta mata, Ladidi ta fara ihu tana neman d’auki. Salima na cikin mota tana kukan tashin hankali tana jin tsoran kar yayan ta yayi kisan kai! Dukan Ladidi yake ko ta ina tana ihu! Wanda babu hawaye, da wuya tayi wuya sai ta fara sharb’en kuka tana cigaba da zaginsa,Salima ta bude mota a tsorace tazo ta rike shi tana bashi hakuri ya bangaje ta tafad’i a gurin,ya cigaba da laftar Ladidi har sai da yaga bakin ta yayi shiru, duk da haka bai saurara mata ba sai da yaga ta daina nuffashi sannan ya k’yaleta! Ya maida belt d’insa gami da matsawa gefe guda yana mai da nuffashi.