LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL


Ladidi kwance cikin jini gefen kunne ta ya fashe yana digar da jini gashi ya kumbura leb’anta ya kumbura had’e da saman idon ta,duk hallitun fuskar ta sun jirkita tana kwance bata san in da take ba, hanya ce da ba kowa ne yake bi ba sai masu kiwo sune suka bi tare da dabbobinsu shiyasa har yanzu babu Wanda ya kawo mata dauki.

D’an Fulani ne ya shigo gurin tare da d’anshi Mati da dabbobin su, sai da suka zo dabda ita sannan suka fahimci mutum ne a kwance ,Mati yayi saurin birkitoto kawai sai yaga Ladidi d’iyar yayarsa Amina, me rasuwa, cike da tsoro ya kira mahaifin nasa yana fad’in “Baffa zo ka ga Ladidiyar Mai koko ce…….

COMMENT VOTE AND SHARE
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????20

Da sauri d’an Fulani ya k’araso gurin, hankalinsa a tashe yace.” Maza d’auke ta muje gida nasan ana can ana neman ta.” Mati ya sab’ata a kafad’a bata san inda kanta yake ba, suka nufi gida.
Mai koko na aikace-aikacen ta na gida kawai taga an shigo da Ladidi a kafad’a, da sauri ya yar da tsintsiyar hannunta tana salati, Mati ya shimfid’eta a tabarma da sauri ya nufi gidin rijiya ya jawo ruwa cikin wata roba ba tare da b’ata lokaci ba yazo ya kwara mata a fuskar.
Minti biyar tsakani ta saki wata wawar ajiyar zuciya, nuffashin ta ya dawo amma kuma bata bude ido ba.
Mai koko ta dinga share hawaye cike da tausayin ta tace.” A’ina kuka ganta kuma waye ya fasa mata baki har ya zubar mata da jini.”? Dan Fulani yace.” Inda kika ganta muma haka muka ganta kwance hanyar titi bata san inda kanta yake ba. Amma nafi tunanin wani tayiwa rashin kunya ya gwada mata rashin imani.”
“Shiyasa kullum nake gargad’inta da rage haikewa manya domin nasan watarana dole ta had’u da wanda zai hukuntata.”
tafad’a tana goge hawayen ta da gefan zanin ta.
D’an Fulani yace.” Ai tun farko an fada miki abunda za’ayi mata a huta kink’iji, ni kinga tafiya na Dade da sanin duk lalatar da yarinyar take kece kike daure mata gindi,ni babu abunda zance sai dai ince Allah shi kyauta.”
Yana gama maganar shi ya kad’a kansa ya futa, Mati ya rufa masa baya
Mai koko tabisu da kallo cike da takaici ya share hawaye tace.” Duk dan kunga marainiya ce shiyasa kuke mata haka, wallahi idona idon wanda yayi wa jikata wannan b’arnar sai na rotsa masa kansa shima.”
Ta fada cike da jin haushi da takaici, Ladidi ta fara motsa idonta a hankali -a hankali ta bude tana kallon Iya, tayi saurin dafe kanta tana rumtse ido! Da sauri Mai koko ta rike hannun tana yi mata sannu, da k’yar tace.” Iya bani ruwa insha wayyo kaina!!!! Iya ta mike da sauri ta d’ebo mata ruwa. Ta tashe ta zaune tare da karata a jikinta ta fara bata ruwan. Kad’an tasha ta kauda kanta.
Mai koko tace.” LADIDI ina kikaje waye yayi miki wannan dukan. “? Kamar da dutse take magana. ta kara maimaita maganar tata. Ladidi batasan ma tanayi ba
hannunta ta tab’a tare da fad’in .” magana nake miki fa.” Da k’arfi tace.” Iya me kika CE.” Itama Iya sai ta bud’e murya sosai tace.” Cewa nayi waye ya doke ki haka har ya kumbura miki fuska tare da zubar miki da jini.”?
Kuka ta fashe dashi tace.” Wani d’an burni ne ya doke ni babu abunda nayi masa kawai don na zo wucewa Iya Allah kuwa sai narama bazan barshi ba.”
Cike da takaici da jin zafi tace.” Ai nima bazan barshi ba,sai nabi miki hakkin ki, domin bazai shigo garinmu yaci albarkaci na kuma ya doke ki har da zubar miki da jini kowa daga ya tashi muguntarsa sai yace ke,to sai nabi miki hakkin ki, ko dame yake tak’ama kuwa.”. Kuka sosai Ladidi take, hankali Mai koko ya kara tashi, tunda taga Ladidi na kuka tabbas tana jin jiki.


K’arfe biyar shaura kwata sun shirya tsaf! suna tsatsaye a harabar gidan suna jiran futowar general, kana kallon fuskokinsu kasan suna cikin damuwa, mussaman Hajiya Asiya.
General ya futo cikin sauri yana d’aura agogo hannunshi, duk ya bisu da kallo, yace.” Ina Hakkim d’in yake.” Yusuf ya sunkyar da kanshi yace.” Bai futo ba.” Cikin b’acin rai! General yace.” Maza jeka kira shi,Hakkim yana so mu sanya k’afar wando guda dashi wallahi.” Salim yace.” Dady kayi hakuri
” ko kallonsa baiyi ba ya shiga mota Mama da Salima suka bude suka shiga. Minti biyar tsakani sai gasu nan sun futo Hakkim sai cin magani yake, Dady yayi k’wafa yana girgiza Kai cikin zuciyarsa yace.” Zakaci malafar ubanka ne yaro.”
Yace.” Ka shiga kayi driving domin babu wani direba da zan d’auka. ” zuciyarsa babu dad’i ya shiga motar gami da kunna ta, suka futa daga gidan.


Hankali Mai koko bai k’ara tashi ba sai da taga tana yiwa Ladidi magana tana shiru tamkar bata ji ba,sai ta d’aga murya sosai sannan take amsa mata, tace.” Oh! ni ‘yarnan Allah yasa wannan mugun mutumin bai lahanta miki kunne ba.” Jira kawai take D’alha ya dawo domin tafad’a masa hankalin ta yayi mugun tashi, duk da ta gaggasa mata jiki tare da shafe mata jiki da Robb hakan bai hana ta cize baki ba,daga an tab’ata zata kurma ihu!! Jikinta duk ciwo yake.
D’alha ya dawo a gajiye ya Tatar da wannan tashin hankalin ,Iya ta kwashe komai ta fada masa hankali sa ya tashi shima ya kwatanta kiran Ladidi shiru sai da ya d’aga murya sannan taji shi, nan ya k’ara tambayar ta abunda ya faru, tana kuka ta warware masa komai.
Shikam bai yadda ba yafi yadda da cewar wani abun tayi masa shine shi kuma ya mata wannan dukan, tunanin mafuta kawai yake, d’an jarinsa bai taka kara ya k’arya ba shi zai rusa dole ya kaita asibitin burni a duba mata kunnuwan ta, tun kafin Abu yayi tsanani, dama asibitoci suna kuka dasu mutanan k’auye cewa basa tashi zuwa asibiti sai sunga cuta tayi tsanani, shikam baya fatan haka.


Gudu yake shararawa General ya buga masa tsawa! tare da fad’in.” Ka jamu a hankali ka kaimu ko muma za ka gwada mana zafin zuciyar ne, sai faman gudu kake damu a mota kamar Wanda zai bar gari.”
Hakkim ya rage gudun da yake, yana jin wani daci a zuciyarsa wai yau shi Dady yakewa tsawa kan wata bare yarinyar da bai sani ba, kwata-kwata ya kasa fahimtar shi, fad’a sosai General ya dinga yi masa har suka Isa Kano bakinsa baiyi shiru ba, Hakkim duk ya koma kalar tausayi saboda abunda bai saba ne, Yusuf ne dinga bawa Dady Hakuri,shima Yusuf din ya samu rabonsa, sai yaja bakinsa yayi shiru cikin zuciyarsa yake cewa” da alama allurar soja ce ta motsawa Dady.

COMMENT VOTE AND SHARE
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button