LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

Lado yace”Ko kaje gurin me gari babu abunda za’ayi mata, kawai ka jawa “yar ka kunne ta daina shiga sabgar ta,, su daina tsokanar ta,Iya me koko tana da fada a gurin me gari wallahi babu wani hukunci da za’a d’auka kan Ladidiya”

COMMENT VOTE AND SHARE
[9/21, 8:18 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????2

Harisu yace”Dole ne fa naje na fad’awa Iya mai koko domin ta ja mata kunne kar watarana ta jiwa yarinya ta rauni, ta barni da siyan magani, ko ka manta ne ko wata uku ba ai ba, yarinyar ta karya “yar gidan Tanimu Harira,, yarinya sai kace k’ashi saboda da rama, sai mugun k’arfin tsiya malam, anya kuwa babu aljanu a tare da ita”?
Ya k’arashe maganar yana goge gumi dake tsattsafo masa a goshi.

Lado yace” Ka iya bakin ka dai in kaje gurin me koko kasan halin Masifar ta, domin kuwa ta tsani ace da Ladidi tana da jinnu”

Harisu ya kama hannun “yar sa Habiba sukayi gaba, sai mita yake.

Shiko Lado redio ya kunna abunsa yana sauraron dawowar shi yaji ya suka kwashe da me koko.

Iya na tsaye da abun tata a hannun ta, tana gyarawa gefe guda kuma wata k’atuwar tukunya ce,cike da mark’ad’an gero da ruwa a gefe cikin wani duro,, tun d’azu take jiran dawowar Ladidi tazo ta taya ta zuba kullun gasara domin ta tace, saboda kokon gobe da safe, ko guntuwa bata da ita, gashi tun asubah ake mata layi na siyan koko. Gajiya tayi da jiran Ladidi ya sa ta mike tana mita taje ta fara gyara matacin tata,, kawai sai ga ta ta afko gidan babu ko sallama.

Cikin mamaki ta kalle tace”Yau ba arzk’i kenan kin shigo babu ko sallama”?

Zumb’ura baki tayi ta wuce bagazan-bagazan ta d’auki buta, ta duba taga babu ruwa a ciki wata tsohuwar rijiya ta nufa ta zura guga na gwangwani, ta jawo ta zuba a ciki ta jefar da gugan kan jar k’asar dake jik’e a bakin rijiyar ta shige ban d’aki abunta.

Tunda Iya taga haka tasan da walakin goro a miya yau za’ayi kwanan masifa kenan in ba Allah ne ya rufa asiri ba, aikuwa tana tsaka da zan can zuci ne taji sallama daga can waje.

Abun tatar ta rataye kan Igiya ta d’ora mayafi aka tana tafe tana amsa sallamar. Malam Harisu ta gani tsaye shi da “yar sa Habiba sai muzurai yake, Gyara fuska tayi ta sha kunu sosai tace” Amun wa’alaikassalamu da Harisu wannan sallamar fa kuma? Sai ka wacce taci bashi”

“Ba dole in zabga Sallama iyi,, Ladidi tana nema ta rauna ta min yarinya dubi yadda ta fasa mata baki ya kumburi har leb’an kasa ya Tsage,shine Nazo na fada miki ki ja mata kunne wallahi ta kiyaye ni, kuma ta daina dukar mi ” yata domin ni ba Tanimu bane ehe”!

Wani kallo iya ta watsa masa tace”Kaji ka da wani zance Harisu, ni dai na san haka kawai Ladidi baza ta doki Habiba sai da dalili watak’ila tsokanar ta sukayi, ayyo! Shiyasa naga ta shigo gidan a fusace”!

Harisu yace”Ai dama nasan baza ki yadda ba,, kullum idan an kawo miki k’arar ta sai kice tsokanar ta akayi to ni daina wallahi na fada miki ki ja mata kunne gudun abunda zai biyo baya “

Mai Koko tace”To gatanan ga kanan Harisu, kun bi gun addabi marainiyar Allah ta’ala komai tayi a unguwa sai a hau zaginta da ai bata ta, nace Harisu ga Ladidiya nan ga kananan Ku zuba mugani tunda dai ka k’i ka tsaya balle in baka hak’uri”

Katangar band’akin had’e take da ta soran gidan Duk abunda ake Ladidi naji ko gama kashin bata yi ba ta d’auraye jikinta ta futo jefar da butar tayi ta futa da sauri
Tsayuwa tayi a tsakiyar su,, tana sosa kanta gami da duddukan sa,, da sauri Harisu ya matsa da baya domin baiyi tsammanin ta a gurin ba, tsidig! ya ganta, ita kan ta Mai koko ganin ta kawai tayi kamar an jefo ta,, Habiba ta rakub’e a bayan Baban ta tana zare ido..

Fashewa tayi da dariya, har yanzu hannunta na kanta tana sosawa tace”Harisu Dan Hindiya Hahahaha yanzu ma k’ara gwada naushi na ka gani ko zaka same ni,, Hahahaha ta cigaba da k’yalkyala dariya, ta kalli Mai koko dake b’oye dariyar ta tace”Kinga Iya wai Babansu Habibu ne d’azu ya kawo hannu zai naushe ni, sai na kauce da sauri ya naushi bakin “yar sa,, wai dole ga Ahe kumar wannan me k’arfin nan na hindiya”

Iya ta sa dariya tana fad’in”Yo Ashe kaine ma ka fasawa d’iyar ta ka baki amma saboda neman magana ka kawo k’ara”

Tsabar bak’in ciki bai bar Harisu yace Komai ba yaja hannun “yar sa suka wuce gida yana cizon ya tsa.

Iya ta gimtse da dariyar da take tana kallon Ladidiya tace” Ina raba ki da kiwon kyalla kina kyalla ta haihu,, ki sani fa baki da wani gata a cikin wannan garin , ni da kike tunk’awo dani bani da k’arfi nema nake kullum duk a kanki, hakanan wannan k’aramin uban naki D’alha da yake fad’i tashi duk akan ya in gan ta miki rayuwa ne, kullum ina fada miki babu ruwan ki,, da yara unguwa ki daina dukan “yayan mutane kada watarana ki jawo mana masifar da baza mu iya ba, Yo in badan ma me gari yana daure miki gindi ba, ai da nasan mutanan garin nan sunyi k’uli-k’ulin kubura dake saboda yadda kika addabe su babu yara babu manya”

Kartar kanta kawai take hannu bibbyu tace”Iya wallahi kin san halina bana barin bahi duk hegiyar da ta tsokane ni sai na zane ta,, da Alwayya da Habiba da Fainusa da Abule da Mariya ne, suke tsokana ta a makarantar allo sunayi min ihu bayan an tashi Wai me kwarkwata, to na kama biyu saura uku billahil lazi sai na zane su suma”

Tsaki Iya taja tana fad’in “Kece ai ko ina sai ki ta sosa kai in ta kama ma ki d’auko ki kashe dan shashanci,, ni narasa wace irin kwarkwata ce wannan me mugun naci sai kace iska sam bata jin magani”

“Tabd’ijam kin San yadda take cizo na kuwa iya wallahi in ina sosawa har dad’i nake ji” Ta k’arashe maganar tana dukan kanta gurin da yake mata k’yayk’ayi.

Iya tace”Ni wuce muje ki d’auraye hannun ki k’azama ki tayani tatar kullu, ga magariba ta gabato”

Ladidi ta tsani a kira ta da k’azama, haushin Iya ya kamata, tw zumb’aro baki gaba,, hanya futa daga gidan tana nufa

Iya tace”Ina kuma zakije”

“Ki samu wanda zai taya ki tatar tunda ni k’azama ce”
Tayi fucewar ta.

Mai koko tabi ta da kallo da baki a sake.

COMMENT VOTE AND SHARE
[9/22, 10:03 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain reades


DEDIGATE
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

Da sauri ta biyo bayanta tana k’wala mata kira tayi mata banza,, ko juyo wa ba tayi ba, hanyar dandali ta nufa, girgiza kai kurum tayi ta koma cikin gida tana fad’in “Ubangiji Allah ya shirya min ke Ladidi”

D’alha ne yake tafe yana tura baro dake d’auke da goba da mangwaro d’ata,, duk sunyi saura da alama yau kasuwa tayi kyau, can Ladidi ta hango shi ya karyo kwana, zai shiga gida, da sauri ta shige soron wani gida tana lek’en shi, har ya wuce, tai sauri ta futo da gudu ta bar gurin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button