LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHIMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????26

General yace.” Iya cewa nayi ki bar min Aminatu a hannuna domin tafi jin dadin karb’ar magani cikin nutsuwa kinga lalurar tata tana buk’atar hakan ,zamu zauna da ita a gidana na nan garin tsawon lokacin da dactor din ya fad’a insha Allahu komai zai yi dai-dai.”

Girgiza kai Mai koko tayi tace." Ayyo! yanzu na fahimci inda ka dosa Alaji, ni kam ban amunce ba domin bazan iya baku ladidi ba ta zauna tare da wanda yayi yunk'urin nakasta ta."

 General yace." Maganar ki haka take Iya amma wannan karon ina me tabbatar miki da cewar idan Hakkim ya kuskura hannunsa ya sauka kan Aminatu da sunan duka to babu shakka zan dauki k'wak'warar mataki kansa."

Girgiza kai Iya tayi tace." Oh!-oh! Ni kam ban yarda ba Alaji kawai ka bamu magani ai naga lokacin da likita ya ke nuna maka yanda za'ayi amfani dashi sai in dinga bata."

Shiru motor tayi kowa na tunani a zuciyarsa hak'ika General bai ji dadin rashin amincewar Iya ba. 

D’alha ya juyu a nutse yana kallon General yace.” Allah kada ranka ya b’aci kan hakan hak’ika nasan zuciyarka daya ka fad’i haka za mu baka Ladidi kamar yanda ka buk’ata tunda ba nisa zakuyi da ita ba kuna cikin garin nan sai in dinga kawo Iya tana ganinta kullum ina ganin haka yayi ko.”?

General yace." Haka yayi samari naji dad'i kuma daka fahimce ni sosai da sosai." Iya ta kalli D'alha cike da takaici gani tayi fuskarsa a murtuke sai tayi shiru bata kara cewa komai ba sam bata son b'acin ransa kasamcewar shi kadai ne da ita a halin yanzu.

 Cike da mamaki suka ga motar ta tsaya gidan gonar dasu ke hira a kwanaki, da sauri Iya tace." Alaji nan ne gidan naka. " ? Da murmushi a fuskarsa yace." Eh nan ne amma ba'anan muke da zama ba ni da iyalina muna abuja, kwanaki na siyi gurin nan nayi gidan gona domin mu dinga zuwa hutu ni da iyalina."

 Caraf! Ladidi tace." Dama bana fada miki ba Nace gonarmu ce suka sace, mana shine daga zuwa zan tsinko mangwaro ya kamani yayi ta duka ni da gonarmu Allah ya isa ban yafe ba kuma sai na rama."

Hakkim tun sanda ta fara magana yake kallonta ta mirror yana jin wani kuttun bakin cikin da takaici ji yake kamar ya tsayar da mota ya futar da yarinyar waje, amma babu hali yin haka. Yanzu tunanin da yake yaya za'ayi ya bar garin domin dai bazai iya had'a guri da ita yana jin zai iya kasheta saboda yanda yake jin zafinta a cikin zuciyarsa. 

Dariya General yayi jin abunda Ladidi take fada ya kalli D’alha dake sunkuyar da kai cike da kunya yace.” Hakane abunda ta fad’a ‘yan samari.”? D’alha ya sunkuyar da kansa kasa sosai yace.” Hakane Alhaji mun siyar da gurin ne ni da mahaifina kafin rasuwar sa shekaru goma sha biyu da suka wuce,sai dai ba duka ne gurinmu ba.” General yace.” Ayya! Allah ya jikansa da rahama, ya kyauta makwancin mazan jiya hak’ika nasan babbar matsala ce tasa ya daga gonarsa ya siyar haka.” D’alha yace.” Hakane Alhaji. ” General yace.” Ku futo mu shiga ciki ai duk Iyalina na ciki sai Ku gaisa.”

Futowa sukayi dukaninsu, banda Hakkim shi tunda yayi parking gurin da aka tanada domin aje mota yayi fucewarsa ya barsu cikin motar. Kai tsaye sharararn farlo suka nufa dukansu, Iya sai kalle-kalle take na k’auyanci ita ko Ladidi dama ba wannan ne zuwanta na farko ba.

Hajiya Asiya na hakimce kan kujera da romot control a hannunta tana neman tashar kallo, Salima ta Dora kanta a cinyarta suna hira, suka ji sallama.

 Hajiya Asiya ta amsa a nutse tana yi musu sannu da zuwa, Salima ta mike da sauri tana kallon Ladidi cikin tsoro.

General yace.” Bisimilh Ku zauna mana.” D’alha ya zauna yana satar kallon farlo. Iya ma haka suka zauna guri guda da Ladidin ta.

Cike da farin ciki Hajiya Asiya tace." Alhaji da alama waccan CE yarinyar."? Yace." Itace Momy kin ganta k'arama ko." Tace." Wallahi kuwa, zo nan kinji mu gaisa." Tafad'a tana mik'awa Ladidi hannu." Kin zuwa tayi sai da D'alha ya buga mata tsawa sannan ta tashi tana zumb'ura baki.

Mama tace. ” kayi mata a hankali mana.” Ladidi ta k’arasa kusa da ita, da sauri Salima ta mike ta bar gurin jikinta na b’ari! Kusa da Dady dinta ta koma tana zare ido! Ya kalleta yana fadin.” Ga ‘yar uwa na kawo miki zata zauna damu sati uku ta karb’i magani Dan uwanki yayi mata lahani ke shaida CE kin gani da idon ki.”

Hajiya Asiya tace.” Alhaji ban fahimci abunda kake nufi ba.” Nan General ya warware mata duk abunda ya faru da abunda dector yace . salati kawai takeyi tana duba kunnen Ladidi tace.” Oh ni Asiya yaro na nema ya jawo mana masifa.” Mai koko ta kalla tace.” Kuyi hakuri don Allah tsautsayi ne.” Mai koko tace.” A’a babu komai ai ya wuce. Sai dai ga Ladidi nan amana Ku kula da ita domin marainiya CE, zan dinga zuwa kullum ina dubata”

Hajiya Asiya tace.” Ai kar ki damu Iya insha Allah za kula da ita yanda ya kamata Allah ya bawa zuciyoyinku hakuri dai.”

D’alha yace.” Ai magana ta wuce mu zamu tafi gida.”

Mik’ewa sukayi suna shirin tafiya. Abun mamaki sai naga Ladidi ko a jikinta ta nemi guri ta zauna gami da tsurawa TV ido fuskarta d’auke da murmushi sai motsu-mutsun dad’i take, TV din D’alha ya kalla sai yaga jarumi Salman khan da kayan ‘yan sanda a jikinsa yana suburbud’an ‘yan gidan boss! D’auke kansa yayi cike da takaici.

Iya ta kalleta tare da fad’in.”Ladidi mun tafi babu rakiya ne.”? Inaa!! Ladidi na can ta na kallo tama manta dasu a gurin.

COMMENT
VOTE AND
SHARE

16/October/2009
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain our reades


JAN KUNNE⚠

Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.

DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????27

General yace.” Iya Aminatu ta samu kallo ai ba zata saurare ku ba.” Murmushi Mai koko tayi tace.” Aikam gashinan naga alama Humm Ladidi da son kallon talabijin ai sai addu’a.” Dariya sukayi dukaninsu Hajiya Asiya ta mike domin tayi musu rakiya, tare suka futa harabar gidan Wanda yayi dai-dai da shigowar Salim cikin mota yana k’okarin gyara parking General yace.” Ya bari tukkuna ga bak’i nan ya mai dasu gida, cike da mamaki Salim yake kallonsu suka gaisa sama-sama ganin kallon da yakewa su D’alha na rashin sani yasa ya fara yi masa bayaninsu, sai ya saki fuskarsa sosai suka shiga mota General na daga musu hannu suka futa daga gidan.

Salima kuwa da aka futa aka barta ita da Ladidi cike da tsoro take kallonta, sai taga Ladidi kwata-kwata hankalinta baya kanta tana can tana kallo abunta. Muryar ta na rawa tace." Ya sunan ki na gaskiya."? Ladidi ta juyo fuskarta d'auke da murmushi tace." Amina kefa."?  Tace." Salima sunana." Dariya Ladidi tasa tace." Sunan 'yan gayu 'yan burni da dad'i Wallahi. " Salima tasa dariya wanda yayi dai-dai da shigowar su General  yace." Yawwa Salima kuje da ita ki nuna mata komai tayi wanka sosai sai kuzo muje cikin gari a siya mata kayan kwalliya irin naki domin so nake Aminatu ta dawo 'yar burni.'

Ladidi ta buga tsalle ta koma kusa da General tana washe baki tace." Ni so nima wallahi baba daga yanzu ka zama Ubana zan zauna daku ina sha'awar Ku." Tausayin ta yaji sosai yace." Muma muna sonki Aminatu zan nemi alfarma gurin Kawun ki ya bani aronki in sanya ki a makaranta.". Murna sosai ta dinga yi, Hajiya Asiya taji tausayin ta da so da kaunarta. Nan Salima ta jata d'akinta suka shiga toilet ta nuna mata komai. Dake Ladidi akwai saurin fahimta bata sha wahalar hada ruwan Wanka ba tayi tsaf ta wanke bakin ta da miskilin kamar yarda Salima ta nuna mata ta futo daure da towol Wanda ta aje mata.

Salima ta kalleta tana b'oye dariya ganin yanda kanta yake babu gashi duk yayi cibiri-birici gashi nan ya fara futowa ta wanke shi tas! Tace." Yanzu in muka shiga cikin gari za siya miki man gashi me kyau daka gani kina da kufan gashi ganin ya fara daga farko sinkif dashi." Ladidi ta zauna kusa da ita tace." Kwarkwata ce ta dame ni shine Kawuna yasa aka aske min amma duk cikin k'awayena babu wacce ta fini gashi."

Salima tace.” Aikuwa naga alama gashinan ai.yanzu ungo wannan kayan ki sanya a jikin ki sai kizo muje farlo.” Ladidi ta kalli kayan da Salima ta mik’a mata, ta sanya hannu ta karb’a da fuskarta da murmushi tace.” Ina son mai sona nagode sosai wallahi ina son babanku.” Salima tace.” Dady ya gode, ai mu ‘yan gidanan haka muke ba yabon kai ba duk Wanda ya zauna damu sai yaji yana son mu.” Ladidi ta mike tsaye tana k’okarin saka kaya tace.” Amma banda mutum daya a cikinku na tsane shi wallahi.” Salima tace.” Wai kina nufi Yaya Hakkim.”? D’aga kai tayi tana saka riga a jikinta, Salima tasan dalilin da yasa tace haka sai ta basar da maganar kawai. Tace “baki saka vest a ciki ba.” “K’yaleni haka wannan shimin takura min take.” Ladidi ta fada tana zura siket a jikinta sosai Riga da siket na atamfa Ghana suka yi mata kyau tamkar an gwada jikinta kasan cewar Salima itama bata da wani jikin kirki bayan haka kuma bata da tsayi sosai ga yanayin dinkin ‘yan matan abuja a matse shiyasa kayanta suka yiwa Ladidi cif.

Tare suka futa farlo Ladidi sai hardewa takeyi na rashin sabo saboda siket din ya dame mata cinye sosai yanayin rigar yasa k’irgar danginta suka futo currr! Kamar gobar da bata gama nuna ba. Lokacin da suka futo Hakkim ya shigo yana zaune cikin kujera yana cin magani duk yak’i kula kowa.

Ladidi na gano shi ta zabga masa harara tana zumb’ura baki sosai ta tsane shi.Hajiya Asiya ta d’an d’aga muryar ta yanda Ladidi zata ji sosai tace.” Iyee! Aminatu ashe haka kike da kyau bafulatana dake, kin ga yanda kikayi kyau kuwa zo nan ‘yata.”

 Ladidi ta washe bakinta ba tun yau ba take son taga ana cewa tana da kyau da sauri ta je gurin Hajiya Asiya sai wata dariya take ta shashanci. Salim da Yusuf sai b'oye dariya suke kar suyi ransu ya b'aci gurin Dady Dan ma baya gurin. 

Ta zauna kusa da ita tace.” Hajiya da gaske kike ni me kyau ce hehehehe.”! Ta kyalkyale da dariya. Hajiya Asiya tace.” Sosai kuwa wallahi son kowa kin wanda ya rasa.”

Dariya su Yusuf ce ta dawo da hankalinta Kansu ta daina dariyar haukan da takeyi ta kalli Hajiya cike da b’acin rai tace ” kin ga sunayi min dariya ko.” Rai a bace Hajiya Asiya tace.” Wallahi duk Wanda ya kara yi mata dariya nan gurin ransa zai b’aci.” Shiru sukayi dukaninsu Ladidi ta b’ata rai sosai tana tabkawa Hakkim harara shida bai ko kalli inda take ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button