LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

A Karaf! Suka had’a ido dashi yana kishingid’e cikin kujera da airpic a kunne shi,zare mata ido yayi sosai wai taji tsoran shi,aikuwa itama ta zare masa nata tana zabga masa k’atuwar harara tare da murgud’a bakinta. Cike da mamaki ya yunk’ura ya tashi sosai yana kallonta itama ta kafe shi da idonta kwala-kwala, tsaki! Yaja me sauti k’asa-k’asa yace.” Yarinya ita ba mutum ba ba aljan ba ba mayya ba dubi wasu ido kamar daffafiyar gurjiya.” Babu Wanda yaji abunda yace a farlo saboda surutun da suke yi Hajiya Asiya ma nacan tana saka musu baki. Ladidi duk taji abunda yace da ita. Tayi k’wafa had’e da girgiza kanta itama a hankali tace.” Dube shi wai shi Dan burni da hanci sai kace na butorami. Hahahahahahaha”!!! Ta shek’e da mahaukaciyar dariya.
Duk suka juyo suna kallonta cike da mamaki sosai Hajiya Asiya tace.” Aminatu Lafiyar ki k’alau kike dariya haka.”? Bata fasa dariyar ba ta nuna mata tv da hannunta Hajiya Asiya ta kalli TV sai ga mage da b’era suna gudu sun sato nama a kicin din wata mata.”
Dariya tayi kawai tace.” Aminatu kenan. Salim da Yusuf kuwa kus-kus suke DOMIN suna ganin al’amarin yarinyar kamar da almutsutsai a ciki. Gogan Ku kuwa, cikin zafin zuciya ya mik’e tsaye yana wani irin huci yayi ball da k’afafunta dake kan hanya y ma fuce yana Jan wani mutsiyacin tsaki!! Mtssssssss!! Kallo suka bishi dashi cike da mamaki.Ladidi ta cigaba da sheka dariyar ta har ya futa waje yana jinta. Zama yayi cikin wata rumfa yana sak’e-sak’e yau d’in nan zai bar garin nan. Domin zuciyarsa zata iya bundiga in yana kallon mummunar fuskar yarinyar nan me kama da Aljanu.
17/October/2009
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????LADIDI????????????
????♀????♀????♀K’WADAGA????♀????♀????♀
~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}
ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????
We are here to educate motivate and entertain our reades
JAN KUNNE⚠
Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.
DEDIGATED
TO
RAHIMA ALIYU
~ABUJA~
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????28
Saturday
*19/October/ 2009*
^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^
Girgiza kai kurum Hajiya Asiya tayi saboda tasan halin bak’ar zuciyar yaron nata, shiyasa basa shiri da Dadynsu wani lokacin saboda baud’ad’an ra’ayinsa, wanda shima General din ba baya bane gurin baud’ewa kusan ma shi Hakkim din ya gado.
Ladidi kuwa gyara zama tayi tana kallon ta sai dariya take shekewa tun abun na basu mamaki yazo ya daina basu suka cigaba da hirarrsu nan General din ya sauko daga sama ya same su,ya shirya tsaf da shi cikin manya kaya ya kalli Ladidi yana murmushi yace." Aminatu kallo kike ne."? Cike da farin ciki tace." Eh Baba." Yace." Da kyau yanzu abunda za'ayi shine ki aje kallon muje mu dawo kin jiko." Ladidi tace." To Baba" Mik'ewa tayi idonta akan tv ta kasa daukewa." Hjy Asiya tace." Kuje Ku dawo ai yananan yana jiran ki." Dariya tayi kamar wata shashasha ta bi bayansu General tana waiwayen tv Su Yusuf kallonta kawai suke cike da mamaki.! Buge kanta tayi garin waige ta dafe gushin tana sakin ihu!! Duk suka maida hankalinsu kanta Hjy Asiya tace." Aminatu ho!! ki rage wannan k'auyancin naki don Allah." Ladidi ta fuce tana zumb'ura baki. Tana futa Yusuf da Salim suka kwashe da dariya dama saboda kar suyi a gabanta ne ta fadawa Dady Hjy Asiya itama tasa dariyar tana ta yasu.
Yana zaune gurin hutarwar ya hangi futowar su, tun daga nesa yake k’arewa yarinyar kallo zuciyarsa na sak’a masa abubuwa da yawa a kanta, sosai yake jin zafin abunda tayi mishi farkon zuwan shi gidan. Yana jin wani irin haushin ta gami da k’yamarta domin shi ramar ta ma tsoro take bashi yarinya sai kace muciya sai kai da uban ido kwala-kwala jiki duk jijiya. Saurin d’auke kansa yayi da yaga Dady ya d’ago kansa yana dube-dube aikuwa karaf ya hango shi zaune. Daga murya yayi tare da kiran sunan shi. Ya amsa cike da ladabi ya taso. Ladidi na tsaye hannuta rike da murfin mota ta dinga banka masa harara tana ya mutse fuska duk cikin’yayan General shi kadai ta tsana tunda baya kaunar ta.
Cike da bada umarni General yace.” Ka shiga ka tuk’a mu zamu shiga kasuwa yanzu.” Sunkyar da kansa kasa yayi yana sosa kai kamar munafuki yace.” Dady da ina so in koma abuja ne yanzu shirin da nake kenan wallahi.” Wani kallo General din yayi masa yace.” Ka koma abuja kayi me.”? Kansa ya Sosa yana shirin kirkiro k’aryar da za shirga. General din yace.” Kaga Malam bama son rashin abunyi kawai ka shiga mota kamar yanda nace.ai na gano abunda zai sanya ka koma abuja yau din.” Cike da takaici Hakkim ya bud’e kofar mota mazaunin dravar ya shiga yana jin wani kunci da takaici a zuciyarsa Wato shi ya zama dravar kenan ? Shi da yazo Hutu an mai she shi dravar saboda tsabar bashi da galihu dravar ma na kucakar yarinya ‘yar k’auye me kwarkwata gami da karzuwa, ya zame masa dole ya bar garin nan.domin ya fuskanci Dady ya shirya tsaf! Gurin ganin ya kuntata masa.
Suka hau titi sosai sai gudu yake Ladidi ta tsira da k'arfi tace." Baba kace dashi ya daina gudu nan da yake tsoro nake wallahi."
General yayi saurin kallon Hakkim yace.” Ka kula mana ka rage gudu sai shilla mu kake kamar zamu tashi sama.”
Hakkim bai san sanda ya daki kan motar ba saboda tsabar takaici wato yanzu Dady shima umarni Yarinyar take bashi. General yace.” Kai meye haka kuma? Kai da aka ce ka rage gudu zaka daki kan mota .”
Hankalinsa ya dawo cikin wayancewa ya Sosa kansa bai ce komai ba ya rage gudun da yake yi. Shi ko General ya juya ya cigaba da hirarasa dasu Ladidi wacce Salima take ta zolayarta ita kuma sai zantuka take mata irin na shashanci.
A hankali yace.” Dady mun futo cikin gari wace kasuwa zamu shiga ne.” ?
General yace. ” anya kuwa zamu shiga kasuwa yanzu dubi lokaci 1:00 na rana muje Sahad stor kawai duk abunda ake bukata za’a samu.”
Bai ce komai ba ya juya kan motar zuwa Shahad Sto zuciyarsa na masa zafi DOMIN ya fuskanci Ladidi za’ayiwa siyayya.
Parking yayi inda aka tanada suka futo shi kuma ya gyara zama cikin motar bashi da niyyar futowa.General yace.” Ka futo mu shiga tare mana.” Girgiza kansa yayi tare da fad’in “Dady Ku shiga kawai bana bukatar komai.”
General yace.” Sai ka futo fa domin ni banga amfanin zamanka cikin motar ba.”
Hakkim bai iya musu ba bare ga mahaifinsa sai ya bude mota ya futo kawai yana jin taikacin takura sa da Dady yayi abunda ba halinsa ba.
Suna shiga ya samu kujera ya zaune fuskar nan a murtuke,wayarsa ya Ciro yana latsawa . Dady suka wuce ciki shida su Salima.Ladidi sai K’auyan ci take zubawa sosai jama’ar da suke ciki suka dinga kallonta kamar sun samu TV Dady sunyi gaba shi da Sallma bai San ta tsaya a baya ba, tana hauka ganin wani takalmi me mugun tsini da jakarsa cikin wani glass sai d’aukar ido yake kokari kawai take ta bude glass din ta Ciro takalmin fad’i take.” Yeeeeeh kan uban can kunga wani hegen takalmi kamar jirgin sama wallahi sai na d’auko hi.” Hannunwanta biyu ta sanya tana k’okarin zuge glass din sai wata mahaukaciyar dariya take. Aikuwa kan kice kwabo jama’a sun fara Ciro wayoyinsu suna mata video suna dariya, wata mata tazo ta riketa tana fadin “Ki tsaya mana a zo a bude miki.” Bangaje ta tayi ta fad’i a gurin.daya daga cikin ma’aikatan gurin ya k’araso da sauri yana mata magana, ko kallonsa ba tayi ba ta cigaba da abunda takeyi.
Cikin zafin rai ya k’araso gurin ya juyo da ita a zafafe ya shimfid’a mata wani bahagon mari! Ji kake Tass! Tass! Har sau biyu.
https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????LADIDI????????????
????♀????♀????♀K’WADAGA????♀????♀????♀
~NA~
BINTA UMAR ABBALE
BINTUBATULA????
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LOADING:
{LADIDI K’WADAGA????}
ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????
We are here to educate motivate and entertain our reades
JAN KUNNE⚠
Ban yarda a d’aukar min d’aya daga cikin books d’ina a siyar min ba, duk mai buk’atarsu ya nemi numbar ta, Idan ka/ki siyar min da littafi to wallahi tallahi ban yafe ba, kuma sai mun tsaya gaban Ubangiji kan hakan, hattara!! Masu satar fasaha a kiyaye kowa yaje ya ci gumin sa, ka nemi halak d’inka shi yafi amfani a gare ka.