LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

DEDIGATED
TO
RAHIMA ALIYU
~ABUJA~

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

23/October/2019

29

Wani uban ihu! Ta kurma Wanda ya jawo hankalin mutane da dama dake cikin gurin ciki kuwa harda General da Salima dake can b’ngaran kayan tea Salima na had’awa, da sauri General ya aje kwalin Milo dake hannunsa domun ya fahimci Ladidi ce take kurma ihu!! Yana zuwa yaga dandazon mutane sun kewaye ta, ga Hakkim a tsaye a kanta yana zazzaga mata masifa tare da zaginta da fada mata munanan maganganu.

Cike da b’acin rai ya k’arasa gurin yace.” Wai me yake faruwa ne? Take wani ma’aikacin gurin ya fara fad’a masa duk abunda ya faru, ya kalli Hakkim ransa a b’ace yace” kan ta aikata haka ka dake ta.? Shiru yayi yana kauda kansa yaso Dady bai zo gurin ba ya wulakanta ta cikin jama’a. Genaral ya kalli jama’ar gurin yace” kowa ya tafiyar sa” aikuwa suka watse daga gurin. Ya kalli ma’aikacin dake tsaye a gurin yace.” Ka ciro mata takalmin da jakar tunda tana so.” Yace.” Angama Alhaji.” Hakkim tsantsar takaici da b’acin rai yasa ya bar gurin a fusace! Dady ya bishi da kallo yana girgiza kansa. Ladidi ya kalla dake zaune a kasan gurin hannunta dafe da kuncinta sai zumb’ure-zumb’uran baki take yace.”gashi nan za’a d’auko miki takalmi ai kina so ko”? Daga kanta tayi ta mik’e tsaye tana buge jikinta General yace.” Duk abunda kika gani kina so anan ki fad’a a d’auko miki kar ki kara saka hannu saboda kar kiyi musu b’arna” d’aga kanta tayi, zuwa yanzu itama ta fahimci wautar da ta. tafka, Bayansu ta bi simi-simi duk jikinta yayi sanyi da ganin yanda jama’a suke kallonta wasu na ta b’oye dariyar su wasu kuwa tana kallonsu suna bude wayoyinsu tasan abunda tayi suke dubawa suna dariya kunya duk ta ishe ta taji takaicin zagin da Hakkim yayi mata cikin mutane.

Salima ce ta dinga zab'ar mata kaya masu kyau da dogayen riguna gami da undis kayan kwalliya mayafai masu kyau da tsada, tsaf suka kammala Dady ya biya kudi Salima ta fara yunk'urin d'aukar kayan General ya dakatar da ita tare da fad'in" ta kira Abudul a waje." Jiki a sanyaye ta tafi yana zaune cikin mota tace Broth Dady na kiran ka" fuskarsa a murtuke yace." Me zanyi masa dallah Malama kauce ki bani guri" da sauri Salima ta bar gurin, tana komawa tace" Dady gashinan" wani ma'aikacin gurin ya k'araso tare da fadin " Alhaji wannan aikin mu ne" ya fara d'aukar kayan yana futa dasu wajan mota suka biyo bayansa Boot ya bud'e masa yana zubawa General ya kalli Hakkim dake faman d'auke kansa yace." Kaje ka taya shi d'ebo kayan mana"

Wani iri yaji a zuciyarsa wai me Dady yake nufi ne? Shi ko General yana sane yake masa haka domin ya k'untata masa ne. A hankali ya futo daga motar ya shiga ciki, su kuma suka shiga motar Hakkim ya dinga futo da kayan yana zubawa a boot zuciyarsa na masa zafi da rad'adi. Sai da sukayi saura sannan ya bar masa ya k'arasa General ya futo da kudi ya bashi, yayi ta godiya ya tafi.

Motar ya shiga ya kunna suka bar gurin, General da ‘yayansa hira suke sosai babu me saka sunan Hakkim a ciki to shima nashi b’angaran yaji dadin haka, sauri-sauri yake suje gida ko ya daina ganin mummunar fuskar yarinyar duk sanda zasu hada ido da ita ta mirror mugun kallone yake raba su da ita.

Suna Isa gida ana kiran sallahr la'asar da sauri ya futo daga motar domin baya so ma wata magana ta had'a shi da Dady din don kar yace ya d'ibi kayan ya shiga dasu ciki.

  Yana shiga parlor dircat bedroom d'insa ya shiga babu wanda ya kula a cikinsu Salim ne yake masa magana da cewar "broth kun dawo kenan"? Uffan be ce masa ba ya wuce ciki." Hjy Asiya tace" butsu kenan mybe sun tafka rigimar shida Dady shiyasa ya shigo yana bugun iska" Yusuf yace." Aikuwa kuma nasan duk akan Ladidiya ne" Salim yace." Aikuwa na lura yarinyar ta shiga ran Dady wallahi   ". Hjy Asiya tace." Ni kaina yarinyar tana bani tausayi sosai na lura shima Dadyn Ku tausayin ta yake ji kasan shi da tausayin tsiya" Yusuf yace "hakane Mama." General na shigowa ya umarci su Yusuf da Salim suje su kwaso kaya cikin mota, suka mike domun cika umarni, daining ya nufa yana fad'in" Zo ki had'a mana abunci mu kwaso yunwa sosai." Hjy Asiya ta mike tana fad'in "ai naga alama gashi wancan sarkin zuciyar ya shigo a fusace kamar zai duke mu." K'wafa general yayi yace." Rabu dashi kinji! Na rasa me ke damun Hakkim wallahi zafin zuciyarsa yayi yawa, Aminatu ya samu Sahad sto ya k'ara duka jama'a suka taro a Kansu." Hjy Asiya ta saka salati tana fad'in " Me tayi masa kuma"? Girgiza kai yayi yace." Ta nuna tana son takalmi to kinsan halin mutuniyar taki da k'auyanci tana k'okarin yi musu barna shine ya yanke wannan hukunci a kanta." Hjy Asiya ta kalli LADIDI dake tsaye tana kumbura kamar zata fashe tace." Zo Amina ke Salima Zo Ku ci abunci." Suka k'araso gurin tare da zama kan kujera. Nan ta hadawa kowa nashi cikin hikima take wa Ladidi Fad'a sosai jikinta yayi sanyi da abunda ta aikata Hjiy Asiya ta kalli Salima tace." Ki nuna mata yadda zata yi amfani da komai ki dinga koya mata abubuwa  burni  ta fara girma kinga ko zaki girme ta da k'adab ne ki dauketa a matsayin k'anwar ki". Salima tace." Insha Allah Mama na dauki alk'awarin yin haka, sai naji ina ma kakarta zata barma na ita." General yace." Ba ke kadai kike wannan tunanin ba Salima."

Haka dai suka ci abunci suna hira , bayan sun gama General ya mike ya shiga bedroom domin yin wanka da sallar  la'asar Salima da Ladidi suma suka shiga cikin wani bedroom Sukayi Wanka tare da Sallah nan Salima ta baje kayan tana nunawa Ladidi yanda ake amfani da komai.

 Magariba kowa ya shiga domin yin sallah Ladidi ta futo parlor taga babu kowa da sauri ta nufi kofar futa, harabar gurin shiru duhu ya fara kawo wa masu gadi duk sun juya baya suna sallah tazo ta bud'e k'aramar k'ofa ta futa, ko ina zata oho!!!!

BINTA U ABBALE

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24

Leave a Reply

Back to top button