LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

Halliru ya tsuguna yana goge gumi, Ladidi ta kassara masa rayuwa ta rusa masa jarin sa, yau-yau d’in nan ya d’auko sabon nono duro guda dubu goma sha biyu yarinyar nan ta zuba masa k’asa a ciki,, kewaye shi sukayi suna bashi hakuri wasu na bashi shawarar kawai ya tafi ya fadawa mai gari a bi masa hakkin sa.

Tana tafe tana d’aura zaninta,, gami da kad’e ragowar k’asar dake jikin zanin,, ta gyara d’aurin d’ankwalin ta,, ta cigaba da tafiya fagam-fagam! Ko tsoron dare ba tayi, Tara da rabi na dare, haka ta dunga wuce majalisa ta maza babu abunda ya dame ta,, har ta karya kwana zata nufi gida sai ta canza shawara juyawa tayi ta koma da baya, kwanar gidan kallo ta nufa,, tun daga nesa ta gango matasa sun cika rumfar kwanon ga hasken wuta nan tar! Masu gyad’a da daddafan k’wai da saurarnsu sai cini ki suke,, bayan gurin kallon bola ce,, gashi ba wani dogon gini bane wani gurin ma da langa-langa a ka rufe,, a hankali ta hau kan bolar ta daddafa ta d’ane kan k’aramar katangar,, kanta ta zura tana lek’awa, aikuwa taga matasa sun cika gurin suna zaune kan bainci wasu ma basu samu guri ba, suna tsatstsaye sai ihu! Suke da alama film din ya d’auko dad’i, sosai take zura kanta domin taga wane irin film ne da ake ihu!! Wani saurayi ne ya kare mata da tsahon sa, ji take kamar ta sauka ta zabga masa mari,, ihun da sukeyi yana hana aji komai sai wani take take ji babu alamun k’usha-k’usha,, kunne ta kasa sosai lokacin da Taji wannan saurayin yana magana dana kusa dashi “Gaskiya ina son film d’in nan wallahi, Sharukahn ya iya soyayya , nifa lokacin da ya rungume ta, he da na kusa suma dan dad’i wannan film din yayi kyau wallahi” Dariya d’ayan yasa yace” Ya sunan film din ma”? “Khoch-khoch hotaih” Hahahaha Gaskiya film din yayi ko nawa ake ce zan biya domin in kalle hi”
Ihun!! da suka ji ne yasa suka mai da hankalin su kan Tv,, Ladidi tace”Hegu “yan iska ni da nasan ba na fada bane ma bazan zo b…. Maganar ta ta katse lokacin da Allah ya bata ikon hango akwatun tv an hasko Sharukan da kajol suna soyyaya da rungume-rungume! ” Kan Uba!! Ta kurma wani uban zagi,, tsaki taja tana k’okarin dura kasa tace”Allah wadaran in tsaya in kalli wannan iskancin, nifa shiyasa na tsani wannan Dan film din gwara Salman kan,, yana da mutum ci,, dura tayi k’asa tana Jan tsaki sai mita take da ta sani bata zo ba, inda ta San ba fim din fada bane,
Shiru gurin duk masu saye da siyarwa dake gurin sun tashi,wasu ma har sun soma futowa daga gurin kallon dana film din yazo karshe, ko a jikinta, ta kama hanyar gida fud’un-fud’un,, kamar daga sama, taji an cafki hannuta, ta juya a fusace! Ilu ne ya ke mata wani kallo yana lashe baki. Hararsa tayi tace”Sakar min hannu ko in ci abu ta kazar ka” Ilu yace”Ni kike zagi takand’a” ? Fuzge hannuta tayi a fusace! Ta tsani ya kira da wannan suna wai takand’a, tace”Uwarka ce takand’a bani ba”

Mari ya kai mata, ta kauce da sauri,, hannuta yaja da k’arfi ya na kokarin kai ta wani lungu ta turje tana zagin sa,, yace”Dama neman ki nake ruwa a jallo Dan uban ki, d’azu kin fasawa k’anwata baki ranan kin zage ni ,to yau zaki gane kuran ki” janta yake tana turjewa, gami da durzar k’asa da kafafun ta, duk k’arfin sa sai da ya sare, ya kama haki!! Tace”Sake ni ni ba “yar iska bace”

Yace”Sai ki gayawa wanda bai sani ba, Dan uwarki daga gidan Uwar ki kike shegiya jiki duk jijiya sai k’arfin tsiya”

“Uwarka ka zaga ba tawa ba” tafad’a a fusace! Yace”Au! Baza kiyi shiru ba” ?

“Sai kayi shiru zanyi, kuma wallahi zaka San ka zagi uwata” “To me zakiyi Takand’a” ? yafad’a yana mata dariya ta k’arfin hali, domin duk ya gaji yau ya kara tabbatar da cewar yarinyar ba ita kadai bace,, shamtar sa tayi yana fad’in “Zaga kuwa abunda zanyi yanzu” kafin ya ank’ara ta kwashe k’afafun sa da hannu daya ta zubar dashi a gurin ta falfala da gudu tana shek’a dariya babu ruwanta da dare.

Ilu ya rike bayansa yana rintse ido sosai bayan sa ya bugu da wani dutse ya Dade a kwance a gurin “yan gidan kallo na ta wuce shi a kwance,, cikin takaici ya mike tsaye yana da ya sanin kula Ladidi gashi ta ji masa ciwo a banza.

Mai koko na tsaye a soro cikin tararrabi, k’arfe goma da rabi na dare, Ladidi ba ta shigo gida ba, ta duba ko ina bata nan,, D’alha ya gama fad’an sa ya futa nema,, da ya d’auka abun wasa ne, sai da yaga an gama Taskar labarai, hankalin sa ya tashi, babu shiri ya bazama neman ta,, duk ya duba inda ya dace babu ita, ya nufo gida cikin gajiya da sarewa, zuciyarsa ta raya masa yaje ya duba gidan kallo, hanya ya kama yana tafiya yana addu’a a zuciyar sa,, da tafiyar ta ya gane ta,, b’uya yayi sai da tazo ta wuce sannan ya futo ya bi bayanta, abunda yasa ya b’uya shine yasan halinta in ta ganshi tana iya guduwa,, tana shiga soron gidan yana shiga,, ya sanya k’arfi ya k’wade mata k’eya d’ankwalinta ya fad’i kasa, ta rusa ihu! Wannan karon Iya bata hanashi dukanta ba, fad’i take ” Kara mata ja’irar yarinya gantalalliya ta tayar mana da hankali”

Ladidi ta buga wani uban tsalle ta afka cikin gidan tana kurma ihu!! Kamar Wanda aka kona mata jiki da ruwan zafi,, d’akin Mai koko ta shige ta zura sakata tana ihu! Tun k’arfin ta.

COMMENT VOTE AND SHARE
[9/24, 10:59 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????5

D’alha yace”Gashi kinji daga bakinta ko? can na gano ta ita kad’ai kan hanya tana tafiya ko tsoron dare ba tayi” Mai koko tace”Yanzu dai kayi hakuri mubar maganar sai da safe dare yayi” K’wafa yayi cike da takaici ya yar da abun dukan ya shige d’akinsa. Iya ta sassauta murya tana fad’in”Bude min kofa kinji ko,, bazan bari ya doke ki ba” Ladidi najinta tayi mata shiru,, “Na ce dake ya tafi d’akinsa ki bude min kofa nace ko” Banza tayi mata,, Sauraye sai cizon Iya suke babu abunda take so illa ta kwanta don tayi muguwar gajiya, rarrashin Ladidi take ta bude mata kofa,, k’eme-k’eme tak’i budewa, gyara kwanciyar ta tayi ta lumshe idonta bacci na fuzgarta, tana jin surutun da Mai koko take sam bai dame ta ba,, b’acin rai da takaici suka saka zuciyar Mai koko kamar ta buga gashi ko “yar tabarma babu a tsakar gidan ballantana ta shimfud’a ta kwanta,, ga duhu ga sauro ga danshin ruwa, bata so ta daga murya saboda dare kar D’alha yaji soro ta nufa a hankali ta kwanta kan dogon bainci da masu siyan koko suke zama tana addu’a a zuciyar ta, Allah ya shirya mata Ladidi.

TUSHEN LABARI

K’auyan d’an kunkuru k’auye ne dake cikin jahar kano,, ya had’a da Fulani a ciki amma ba sosai ba,, k’auye ne da yake da albarkar gonaki da filaye gami da manya-manyan bishiyun mangwaro ko ta ina,, Malam Labaran manomi ne wanda yake da gona guda d’aya yake noman d’orawa da gero a ciki,, da Abunda ya dogara kenan dashi yake ci da iyalinsa yake sauran bukatu, yana da mata d’aya da yara biyup
duk maza, matarshi sunanta Furera, mace mai Neman na kanta tunda aka kawo ta gidan Mijinta take sana’oi iri -iri , domin ta dogara da kanta, dansu na fari sunan shi Aminu yana da lalurar sikila sai Dan uwanshi D’alha shi lafiyan sa lau, abunka da k’auye San basu maida hankali gurin ciwon dansu ba, sai dai in ciwon ya motsa masa suyi masa jike-jike su bashi, Cikin hukunci ubangiji ya mike ya cigaba da rayuwa kana kallo Aminu kasan bashi da koshin lafiya tare suke tafiya gona da mahaifin sa,, ko sunje can ma baya iya aikin koma, D’alha ne me karfi,,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button