LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

Malam Labaran yana da aboki D’an Fulani gurin zuwa kiwo suka hadu dashi,, inda Allah ya had’a jininsu ta kaisu ga had’a yayan su aure Aminu da Amina “yar Dan Fulani itama tana d’auke da irin lalurar Aminu, dake d’an Fulani ma’abocin jin redio ne, ya tab’aji suna fada cewar idan masu irin cutar zasuyi aure su dunga auran jinsu su, nan Labaran ya amunce, ya kuma Sanar da Aminu da Hurera duk suka amunce suna fatan alkairi,, lokacin yayi aka d’aura aure cikin aminci Amina ta tare gidan Mijinta Aminu inda gurinsa yake kewaye da langaga sai dai in zata shiga band’aki take futowa babban tsakar gida,, wata hudu da auran su, ciwon Aminu ya tashi kafin ayi wani yunk’uri ya galabaita mutuk’a jikinsa kamar babu jini ya dashe Tass,, wani makocinsu ya basu shawarar zuwa birni domin a duba shi, to suna cikin shirin tafiya ne, Allah ya amshi Abunsa , mutuwar sa ta girgiza mutane mussaman matarsa Amina tayi kuka har ta gaji ” yan uwa na tasaunta tayi hakuri,, bayan sadakar uku kowa ya watse akabar mutan gida da kewar Aminu mutumin K’warai kenan, bayan sadakar ar’ba’in ne aka gano cewar Amina na da ciki, aikuwa Mai koko ta dunga kula da ita sosai har lokacin haihuwa yazo,, inda Amina ta fara zubar da jini abunda ba a so kenan ko mai lafiya balle mai sikila, hankali a tashe aka d’auke ta sai asibitin birni (Murtala muhamad hospital) ganin tana cikin halin taimako ne yasa suka shiga da ita dakin operation,, suka ce mijinta ya sa hannu aiki za’ayi mata,, Dan Fulani na kuka da rokon Allah ya sanya hannu Labaran ma ya sanya, to tun kafin a shiga da ita ta rasu,ganin cikin na motsi yasa suka shiga da ita cikin gaggawa aka Ciro yarinya mace, mai kama da uwarta.

Cikin halin damuwa nurse ta futo ta sanar dasu halin da ake ciki, sosai suka shiga rud’u da tashin hankali daga bisani suka hak’ura suka barwa Allah, suka karb’i gawar Amina suka tafi domin yi mata suttura, mai koko na rungume da jaririya tana kukan zuciya.


Mai koko ta d’auki son duniya ta Dora shi kan Amina da taci sunan mahaifiyar ta, dama kafin su baro asibitin sun duba ta sosai ko itama tana d’auke da ciwon sikila, Allah mai yadda ya so yarinya lafiyanta Lou sai dai k’ankanta, amma inda ans bata madara me kyau zata murmure.

Malam Labaran bai yi shawara da kowa ba yaje ya sanya gonar shi a kasuwa nan take aka samu mai siya kasan cewar gonar tana da kyau kuma tana da fuska akayi ciniki aka bashi kudinsa, ya nufi asibitin cikin gari duk abubun buk’ata ya siyowa Amina ya siyo mata madara masu kyau, da kaya niki-niki ya shigo gidan, Hurera tai yi mamaki sosai nan ya zauna ya warware mata komai, tace”Malam da kayi shawara dani da baza ka siyar da gonar ka ba” yace”Saboda haka shine mafuta asurinmu ya rufu, Kinga madarar nan tana da tsada idan ba haka ba bamu da kud’in siya, kuma ko d’aukar me shayarwa mukayi dole mu biyata, tace”Hakane kuma to Allah ya rufa mana Asiri,, nan Hurera ta kara k’aimi gurin Sana’a har ta kafu da sanar Koko da safe,, shi kuma D’alha yake sana’ar sai da D’ata goba da mangwaro asirinsu na rufuwa,, Dake ranar lahadi aka haifi Amina yasa Mai koko take ce mata Ladidi shikkenan mutane suka rike suma suke kiranta da Ladidiya,, shekararta uku a duniya Allah ya amshi ran Malam Labaran ciwon kai tafarar daya,, Mai koko nauyi ya kara yi mata yawa, dake jaruma ce, sam bata karaya ba, ta cigaba da neman kud’inta, da kanta ta kai Ladidi makarantar allo tun tana da shekaru hudu,, tana zuwa cikin yara zaka ji gurin ya kaure da kuka Ladidi Duk ta doke su, har wad’anda suka girme ta dokansu take,,Malami ya doke ta tayi masa Allah ya Isa,aikuwa ya dawo wa da mai koko ita yace”Tana hana su karatu in taje dokan yara kawai takeyi ta hanasu karatu gashi in an doke ta tayi Allah ya Isa shi kam bazai iya ba” Mai koko tace”Kaje ai ba kai kadai bane me makaranta na kai ta wata, sai da akayi wata shida tukkuna sannan ta kaita wata makarantar nan ma bata canza zani ba,, tana zuwa makarantar karatun yara ya lalace domin duk gurinta suke komawa suyi ta wasa duk tsawan da malam zai musu basa jinsa. Nan ya fahimci zuwan Ladidi ne jawo haka, tunda da yana iya tankwara su, aikuwa sai ya ware ta a cikinsu in tayi futina yaci ubanta, ita kuma ta zage shi, gashi duk dukan da za’ai mata bata kuka sai dai idonta yayi ja, malam da yaga ba zai iya ba ya tattarata ya mayarwa da mai koko ita,, abunda ta fadawa malamin farko haka ta fada masa,, shekara guda bata zuwa makaranta, sai wasa da yawo kusfa-kusfa D’alha bai tab’a Ankara ba, dake da wuri yake futa baya dawowa sai gab da magariba, ya dawo ya wuce ta makarantar Allo yaga an tashi yana ta daga kai yaga ta inda Ladidi zata b’ullo bai ganta ba, sai yayi tunanin ko ta tafi gida, yana tafiya ya hangota kan katangar wani gida ta mike tsaye tana ta tafiya tana k’yalkyala dariya kanta babu d’ankwali, sai diddigagen gashinta da kwarkwata ta cinye rabi ta bar rabi, duk k’wanta nan burjik!! Kira ya kwala mata”Ladidi”!! Da sauri ta juyo jin muryar Kawunta ta hantsilo k’asa ko a jikinta ta mike da gudu tayi gida,,, girgiza kai yayi ya bi bayan ta.

Sosai ya dunga fad’a Mai koko tace”Ai sai ka d’auke ta ta kaita da kanka ko wace makaranta aka kai ta sai su koro ta saboda tsabar bakin ciki sun tsani marainiyar Allah” Yace”Halin ta ne ya jamata zan kai ta, wata makatanar da kaina Wallahi da kaina zan dunga hukunta ta” Shiru mai koko tayi masa ya gaji ya shiru, ita ko Ladidi na bayan ta tana zumb’ura baki gami harare-harare ta tsane shi tunda kullum cikin takura mata yake. Washe gari da safe D’alha ya sa ta a gaba suka nufi makaranta ya damk’a ta a hannun Malam yace”Gatanan yayi mata hukunci in tayi laifi, kuma ya kula da karatun ta.”

COMMENT VOTE AND SHARE
[9/24, 10:29 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

KU SONI TA ZARCE???????????? NIMA NA NASO KU TA ZARCE❣❣❣IN HAR KUKA KUFCE! ????????A KANKU NI ZAUCE! ???? IN KUNJI????????
????????????????????????????????

I will always saying thank you to my people love you so much,, muna tare insha Allah????

????6

D’alha ya kama hanya yai tafiyar sa, gurin sana’ar sa, tunda malam yayi mata gurin zama cikin yara take ta faman zabga masa harara sosai yayi mamakin yarinyar ko da yake dama yana da labarin ta sosai,, sai ya d’auke kansa kawai yayi kamar bai ganta ba,, ya cigaba da koyar da yara, yarinyar dake kusa da ita ta zura hannu ta mintsina yarinyar ta fashe da kuka, Sai tayi saurin cire hannunta tana kallonsa yana kallonta,, ya gane itace yarinyar ya kira da hannunsa, gurin zama yayi mata,, Ladidi taji haushin haka, tayi shiru tana zumb’ura baki, lokacin tashi nayi yayi musu addu’a duk suka mike sai ta d’auki takalmi wata ta b’oye, to yaga lokacin da ta d’auka, murmushi yayi ya kira yarinyar ganin tana kuka, Ladidi ya kira, taje tai masa k’erere aka yace”Bata takalmin ta” Zumb’ura baki tayi tace”Baya gurina fa” “Naga fa sanda kika d’auka kika b’oye bata kinji ko,, ni nasan kyautar da zanyi miki” Shiru tayi yace”Zan baki alawa” Aikuwa sai ta futo da takalmi da ta b’oye kasan zaninta ta jefawa yarinyar, da sauri ta d’auka ta sa, ta kalle shi, kai tsaye tace”Bani alawar” yace”Dama ba karatu kika zo ba” ? Daga kai tayi” yayi murmushi yace”To don Allah kiyi karatu ki nutsu kinga Kawun ki ya kawo ki kiyi karatu nayi miki alk’awarin bazan Doke ki ba kamar yarda ya fad’a” baki ta tura tace”Ko ka dake ni ba zafi zanji ba” dariya yasa yace”Nasan da haka ai,, shiyasa ma bazan tayar da hankalina ba”. “Ni dai bani alawa ta” fad’a tana Sosa kanta,, Hannu ya zura cikin aljihun sa ya ciro Alawa guda biyu yace”Kullum nayi miki alk’awari zan dunga baki mutuk’ar zakiyi karatu in kin zo makaranta kuma zaki nuttsu ki daina tsokanar “yan uwan ki” Karb’ar Alawar tayi tayi tafiyar ta, ta barshi da baki a sake, girgiza kai yayi ya d’auki allon nata yana dubawa, duk girman ta, tana Alam tarakaifa. Wanda basu kai shekara goma ba ma sun shiga sabbi,, ita tana zaune, haka kawai yake tausayin yarinyar, yana fa yara guda biyar duk kamarta shiyasa in yaga yara na k’uruciya yake musu addu’ar shiriya Wannan shine silar zaman Ladidi a makaranta ko tayi nufin tsokona ko gudun makaranta sai ta fasa saboda alk’awarin alawar da Malam Salihu yayi mata, shi kuma kullum baya fashi, ana tashe zai bata,, gashi Yanzu tayi nisa a karatu ta kusa izu d’aya. Babu laifi tana gane wa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button