LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

WANNAN SHINE TOSHEN LABARI

Da Asubah D’alha ya futo da niyar zuwa massalaci, da cocilan a hannunsa yana haskawa, sai ya ga Mai koko na k’okarin saukowa daga bainci da alama itama tashin ta kenan, Cikin mamaki ya tsaya yana kallonta yace”Iya me kike anan”? Shiru tayi masa ta mike tana Sosa jikinta, yace”Da alama nan kika kwana meye dalili”? Cikin b’acin rai tace”Wannan ja’irar yarinyar ce ta rufe min k’ofa jiya babu yadda banyi ba ta bude min amma tak’i”D’alha mamaki sosai yake yace”Tak’i bude miki k’ofa me makon ki min magana shine zaki kwanta a soro cikin sauro Iya sai kinje zazzab’in cizon sauro ya kama ki”? K’okarin shiga cikin gidan take tana fad’in”Kai dai magana ta wuce, ai kayi tafiyar ka” Gyad’a kai kawai yayi ya wuce yana mamakin son da Iya takewa Ladidi wannan son shi a ganinshi cutar wa ne, domin shi yake k’ara lalata yarinyar. Har yaje massalaci yan sak’e-sak’en hukuncin da zai d’auka kan Ladidi domin ko me Iya zatayi sai ya doke ta ya rantse. Bayan an idar da sallah sun futo,, Halliru mai Fura ya tsaida shi suka gaisa,gani yayi Halliru na sha masa kunu yace”Malam Halliru lafiya ko” ? Halliru ya sauke ajiyar zuciya yana fad’in”Idan kaji kira daga mai gari kar kayi mamaki” Cikin mamaki D’alha yace”Me ya faru” Rai a b’ace Halliru ya kwashe duk abunda ya faru ya fad’a masa,, innalillahi wa’innailahi raji’un shine abunda D’alha yake ta Nanatawa yace”Don girman Allah Halliru kayi hak’uri wallahi in banda ka fada min ban san abunda yake faruwa ba, itama Iya ina tabbatar maka da cewar bata sani ba kayi hakuri don Allah kar ta kaimu ga zuwa gurin mai gari, wannan tonan asiri ne”

Halliru ya sha kunu yace”Inyi hakuri kamar yaya? Kana nufin in zauna bani da abinyi kome? Na fada maka fa yarinyar nan duk jarina ta rusa kaje ka tambayi Mutari me nama zai fada maka komai” D’alha ya kwantar da murya yana fad’in “Duk baza ta kaimu ga haka ba,, yanzu ya kake so ayi” ? Kai tsaye D’alha yace”Kawai mu raba asara Ku bani dubu biyar ni nayi muku lamani” D’alha ya tsaya yana tunani daga bisani yace”Shikkenan insha Allahu zamu San abun yi ka kwantar da hankalin ka”

Halliru ya saki fuska yana fad’in “Shikkenan sai na jika”
Sallama sukayi kowa ya kama hanyar gida.

Lokacin da ya isa gida, Mai koko na tsaye gaban wata k’atuwar tukunya da duguwar muciya a hannunta tana ta aikin motsa koko ga kwanuka har an fara layi,, kai tsaye d’akin ta ya nufa, sam bata yi tsammanin dokan Ladidi zai yi ba,, sai ihun ta kawai ta ji da sauri ta jingine muciyar ta shiga dakin da sauri,, tana fad’in “Au!! Dama dokan ta ka shigo kayi ko D’alha? Can na hango Ladidi k’arshen gadon k’arfen Mai koko sai ihu!! Take kurmawa babu ko k’wallon hawaye, D’alha ya zage k’arfi yana ta labta mata bulala,ya ki cewa komai,, Tace” Shikkenan kashe ta tabi iyayen ta, tunda kak’i ka saurare ni” yana haki! Yace”Da kin san abunda yarinyar nan tayi to da kin bani gudumawar abun duka” Cikin fushi tace”Kome tayi bazan bada abun duka a illata ta ba, ni dai nace ka daina dukanta in dai ni na haife ka” D’alha ya yar da abun dukan yana haki! Cikin b’acin rai yake warware mata abunda ya faru, sosai itama ta jinjina al’amarin, amma don k’arin abun haushi sai cewa tayi”Yo ai da ka k’yale shi yaje ya fad’uwa mai gari sai me, dan yaje, dubu biyar dai insha Allahu za’a bashi, ai k’imar mutum tafi kudi shi kud’i suka dama da zai zugo ka kazo kana dukan marainiyar Allah”
D’alha yace”Ko yau ta k’ara sai na doke ta, in ta kama ma in sa ta a mari sai in daure mata k’afafu sai inga k’afafun yawo”
“Tunda kai ai haka akayi maka sai ka daure ta magani” Mai koko tafad’a cikin takaici,futa yayi a fusace! Ta mai. da hankalin ta kan Ladidi dake ta faman sosar jikinta wani gurin har ya kwailaye, amma saboda dauriya da kafiya gami da jarumta ko kwalla babu a idonta k’ema gadas, sai da sunyi jajazuri! Tace”Kin kyauta kinji ko, aini kam bazan miki baki ba sai dai i n nema miki shiriya a gurin Allah idan kuma wani, shad’ainin ne yake sanya ki wannan Ibilicin to sai yayi magana mu sulhunta dashi, Allah ya bashi hakuri” tana gama maganar ta ta futa daga dakin domin ta fara jin hayaniyar yara a tsakar gida.

Ladidi ta jima kan gado Tana Sosa jikinta dole fatar ta kwaile mussaman cinyar ta duk tayi rud’u-rud’u da duka, saukowa tayi daga kan gadon ta d’auki zaninta ta daura. fuskarta a murtuke ta d’auki dakkaken gawayi wanda suke goge bakinsu dashi, ta futa tsakar gida,, can bakin rijiya ta nufa ta d’auki buta ta zub ruwa nan bakin rijiyar ta tub’e wandon ta tayi futsari, ta fara durzar bakinta da gawayi, ranta a mugun b’ace, duk yaran da suke mata magana tana jinsu tayi musu banza.

Al’wala ta d’aura ta shige d’aki, Ladidi duk k’injin ta tana sallah in lokacin ta yayi.Ko kwantawa tayi ta manta ba tayi ba, to lokacin ta nayi zata rama haka takeyi tasan lokotan ko wace sallahr farillah.



FLORIDA

Ta k’asar America,, had’and’un samari na gani zaune gurin shak’awa,, tsakiyar su lemu ka ne, masu sanyi da wani irin cin-cin wanda yaji madara da kayan had’i, suna ci suna hirarsu irin ta abokai, gefe guda kuma turawa ne suke ta sha’anin su, kai harda bak’ar fata ma, “yan k’asashe daban-daban kowa sai cin karansa yake babu mai damuwa da kowa, da yawa daga cikin su babu kayan arziki ajikin su, daga su sai wani tsinkakken wando wanda ya shige musu matse-matsi da tsinkakkiyar briziyya Wanda bata gama rufe musu nonowa ba duk gasu nan a waje, da gudu suke tsalle suna fadawa cikin ruwa suna dariya. Hakeem ya d’aga kansa yana kallon su,, fuskar sa a had’e yace” Dube su don Allah banzaye dasu sai nuna tsaraicin su suke, ashe dama abunda ya sa ka dame ni kenan kana so kazo ka kalli tsaraici, abunda Allah ya hana, haka kawai ina zamana cikin rufin asiri ka takura min sai nazo mun futa d’an iska kawai” Dariya Bash yasa yace”Kai don Allah fad’i gaskiya dai Yanzu ganinsu bai d’ebe maka kewa ba?, nifa wallahi dama da biyu nazo gurin nan,, so nake kafin mu koma in bawa idona hakkin sa” Cikin taikaici Hakeem yace”Kai wannan ya dama Wallahi nifa in ga mace cikin hijabi yafi min mutumci nama fi jin sha’awar ta akan in ga tsaraicin ta, don Allah tashi mu bar gurin nan” Ya fad’a yana mik’ewa tsaya,, mik’ewa Bash yayi yana fad’in”Ka dai fad’i gaskiya malam wa zaka nunawa ustazanci” banza yayi masa ya fara tafiya, wata beb ce ta futo daga cikin ruwa da gudu, daga ita sai d’an mitsitsin wando babu ko brziyya ta d’anshi, babu zato suka fad’i k’asa.

COMMENT VOTE AND SHARE
[9/25, 5:40 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation

????????????LADIDI????????????
????‍♀????‍♀????‍♀K’WADAGA????‍♀????‍♀????‍♀

NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~

MARUBUCIYAR

NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI

LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}

ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????


We are here to educate motivate and entertain aur reades


DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU

BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM

????7

A mutuk’ar fusace ya hankad’e ta ta fad’i k’asa ya mik’e tsaye da sauri, cikin zafin zuciya! Ya damk’o wuyanta ya dunga rafka mata marika, lafiyyayu. Da sauri Bash ya k’araso gurin gami da fuzge yarinyar daga hannun shi yace”Lafiyan ka kuwa hana Hakeem, wannan wane irin zafin zuciya ne, ai tunda ka kawo kanka gurin nan kasan haka zata faru”‘ Cikin b’acin rai yace” Dallah Malam rufe min baki,kai me yasa ba tai maka ba sai ni? Saboda ni ta raina,ko an fad’a mata cewar d’an iska ne ni, kamar ka, da zata zo ta rungume ni” Yarinyar tana tsaye hannunta dafe da kuncin ta, sosai taji zafin marin da yayi mata, idanun ta sunyi ja sosai,, tace”Don nazo in jiyar da kai dad’i shine ka wulak’anta ni, a idon mutane,, kasan ni ko wacece kuwa”? Banzan kallo yayi mata yace”Rufe min baki ko in zo in k’ara miki wani, ko ke wacece bai dame ni, ke kika shiga gona ta, meye ruwan ki dani zaki zo ki samin najasa a jiki” Cikin takaici tace”K’arya kake kace bakasan mace ba, wannan idon naka da yake a bude, saboda kayi min yasa yana kusance ka” Cike da takaici ya kalle ta sama da k’asa yace”To ni bakiyi min ba, shashashar banza kawai baki da Abunda zaki rud’e ni dashi, ko kina musulma d’iyar Hausa Fulani kina aikata ashararan ci, ina jiran hukuncin da zakiyi,, Sunana Abdul Hakeem Abbas D’an kaka” Ya zura hannunsa cikin wandon jins d’insa ya ciro wani k’aramin kati ya wurga mata, yace”Wannan katin shi zai nuna miki duk inda nake, ina sauraron ki” yana gama fad’in haka ya bar gurin a fusace! Bash ya kalle ta, tana tsiyayar da hawayen bak’in ciki, girgiza Kai yayi baice komai ba ya wuce, cikin zuciyar sa yake fad’in “Baki san wanene Hakeem ba shiyasa kika aikata masa haka, ya san halin mutumin shi, da tsantse ni, baya son abunda zai had’a shi da wata mace mutuk’ar ba halalin sa bace.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24Next page

Leave a Reply

Back to top button