LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

Cikin mota ya tadda shi yayi cikin-kicin da fuska,, sai kad’a k’afa yake, yana zama cikin motar ya balbaleshi da masifa,, Bash yace”Wai Ubana ne kai da zaka dunga min masifa nafa gaji wallahi abu ya ruga ya faru sai magana ta wuce”, “Ank’i a daina maganar ai kaine babban me laifi a gurina haka kawai ka takura min lallai sai naje gurin,, Bash yace” Da nasan abunda zai faru da ban gayyace ka ba, nasan yau yini zakayi kana tsine min” Tsaki! Yaja yace”Daga yau in zaka je yawon ka kar ka k’ara takura ni dole sai naje,, kaje kayi tayi kai tunda baza ka fasa ba” Bash yasa dariya yana fad’in”Angama ogana, wai ni don Allah in tambaye ka mana”? Ajiyar zuciya ya sauke yace”Ina jinka” . “Me yasa kullum kake takurawa kanka ne? Kace kallon mace ma baka so kayi inaso ka sani wannan tsantsenin naka ba shine zai tsare ka daga Abunda kake gudu ba, na lura fa kallon India film American film baka cika yi ba,, kafi kallon Hausa film mussaman na ” yan k’auye nasu Rabilu Musa d’an Ibro, Allah ya gafarta masa” Kai tsaye yace”Saboda nasan yaya nake shiyasa nake takatsatsan da kallon abunda zai tada min da hankali” Murmushi Bash yayi yace”To wallahi gwara ma ka kadaina takurawa kanka ka tsaya ka mori k’urociyar ka, kallo ne kawai fa, ba aikatawa kayi ba balle kace kana da zunubi” Hakeem yace”Na lura k’aranci ilimin addini yana damun ka Bashir, mu bar wannan maganar, kada rayuka su b’aci don yanzu zan maka abunda bakai zato ba,, kai ma addu’a nake ma kullum Allah yasa ka gane, in sha’awa na damun ka in ka koma gida kayi aure kawai shine mafuta, domin a halin da kake ciki zaka iya fad’awa halaka” Bash yayi shiru yana tab’e baki, Shiko Hakeem driving d’inshi yake fuskarsa a had’e.
WANENE ABDUL HAKEEM?
Abdul hakeem Abbas D’ankaka, matashin saurayi ne d’an kimanin shakaru Ashirin da tara, yayi karatun sa na primary socndry a kano inda ya wuce America can yayi degree d’in shi fannin engineering,, sosai yake da brain inda wani company, nan k’asar America suka d’auke shi aiki ya amunce amma da sharad’in sai ya koma gida ya sanar da iyayen sa, bayan haka kuma sam bashi da ra’ayin zama k’asar saboda lalaewar ta,, mutum ne mai tsantseni baza ka gane haka ba sai ka zauna dashi, amma kallo d’aya kayi masa zaka d’auka wayyaye ne, kan holewa ta duniya saboda yana da bud’add’iyar fuska da iya mu’amula, da fara’a da barkwanci ga shi idanunsa a bude so ke ko yaya ya zauna da kai na minti goma zai fahimcin halin ka, wannan yasa mutane suke masa wani bahagon kallo, Ubangijinsa ne kawai yasan waye shi,
Sun had’u da Bash ne a company shima yazo interview, shine suke abota, tunda Bash yazo k’asar yake yawo gurare, yau sai da yaja ra’ayin Hakeem ya bishi haka ta faru. Bash d’an Sakwatto ne, iyayen sa da “yan uwansa duk suna can da zama,sab’anin Abdul Hakeem, da suke Abuja da zama amma asalinsa dan jahar kano ne.
General Abbas d’ankaka tsohon soja ne da yayi ritaya shekaru goma da suka wuce,, yana da mace d’aya Hajiya Hasiya suna da ” yaya uku rak, biyu maza d’aya mace, Abdul Hakeem ne babba sai Salim sai Salima itace auta yanzu ta gama scondry tana shirin shiga jami’a, Salim kuwa saura shekara d’aya ya had’a HND d’insa , Salim da Salima kamar su d’aya,, suna kama da mahaifiyar su, da ta kasance shuwa fara ce tas sune suka d’ebo kamanin ta, shiko Hakeem Sak mahaifin sa, yana da duhun fata ba sosai ba, kalar fatar shi abun kallo ce, sosai suke girmama shi gami da bashi girmansa, suna gudanar da rayuwar su a tsare babu baragada komai cikin ilimi suke yi
Kwana da yini tayi bata kula Mai koko ba,kamar itace ta doke ta, Mai koko kuwa sai lallab’ata take tana botsarewa, dan kanta ta hak’ura ta daina fushin…. Tsayawa tayi kan Mai koko k’erere tace”Bani kud’in makarantar” ta kalle ta cike da takaici tace”Babu gaisuwa kawai kinzo kin tsaya min aka ina amfanin haka? Wai ke yaushe zakiyi hankali ne”? D’auke kanta tayi tana zumb’ura baki, girgiza kai kurum tayi ta d’auki wani gwangwani da take ajiyar kud’i ta ciro hamsin ta mik’a mata tana fad’in”Gashi ki d’auki goma ki dawo min da canji na” Karb’a tayi da sauri a zuciyar ta tace”Wallahi ko sisi bazan dawo dashi ba, ladan dokan da akai min” Mai koko tace”Allah ya bada me amfani don Allah banda tsokanar yaran mutane” Banza tayi mata ta futa fakam-fakam!! Tun a hanya ta siyi aya jik’akkiya da goro ba, na goma-goma ta kwance d’an kwalin ta ta kulle canjin talatin d’in,,, To yau ranar wanke allo ne domin a sauya rubutu, d’aya bayan d’aya kowa yake biya allon sa, in ya iya sai ya je ya wanke ya kawo wa Malam,, Da k’yar Ladidi ta biya nata Malam nayi mata gyara yace”Gaskiya ki bari sai wani satin sai ki wanke kafin sannan kin iya” hararasa tayi, tace”Ba gashi nan na biya maka, gaskiya ni sai na wanke kamar yadda kowa ya wanke” yace”Ban yarda ba fa” mik’ewa tayi da allon a hannuta taje ta wanke,, kallonta yake cike da mamaki yace”To yau kuwa Wallahi bazan baki alawar ba” Dariya tasa tace”Ka rik’e kayar ka yau ina da kud’in siya, ga gansu ma” tafad’a tana nuna masa inda ta daure, k’wafa kawai malam yake yana kallon ta tana wanke allo tazo ta aje gabansa ta wuce fud’un-fud’un tana fad’in “Kuma dole ai min rubutu”. Malam addu’ar shirya kawai yake mata.
Tare suka jero da Alawiyya yanzu sun shirya basa fad’a, Alawiyya tace” Zo muje gidan muyi kallo, jiya babanmu da yaje burni ya siyo mata tv da vidio” Dariya Ladidi tasa ta daddaki kanta, tana fad’in “Da gaske kike “? Alawiyya tace” Wallahi” Ladidi ta rike hannunta suka kama sauri,,, aikuwa suna isa gidan suka tarar an kunna, yara sun cika gidan sai kallo suke, wani film ne singam fasarar Hausa, Ladidi tayi tsalle ta shiga tsakiyar su,, shikkenan guri ya hautsine daga wani yayi motsi zata buge kansa ta ce ya kare mata,, idan aka zo gurin fad’a, sai ta saka ihu! Ta mike tsaye tana gwadawa, inda tsautsayi ta buge na kusa da ita,, tuni kukan yara ya cika babarsu Alawiyya tace”Kai kashe kallon zanyi Wallahi ya daina dadi baka jin komai sai kuka” Ladidi ta rarrafa gurin ta rirrike mata hannu tana magiya kar ta kashe ta daina, da k’yar babarsu Alawiyya ta hak’ura ,, gurin fad’a kazo Ladidi ta kurma ihu!! Ta kalli Iliya dake zaune gefen ta, tace”Iliya don Allah ya sunan afton nan ya iya fad’a wallahi, hehehehe, kaji har wani take ake masa,, kama b’arawo suburbud’e shi, sa shi a mota oga Singam!!!! hahahahaha ta kwashe da dariya ta koma ta zauna tana sosa kanta jikin ta sai tsuma! Yake,, aikuwa yaran da suke gurin suka rud’u da fad’in “Kama b’arawo suburbud’e shi sa shi a mota Oga Singam!!!!!! babarsu Alawiyya ta dunga dariya tana fad’in “Ladidi sai dai idan baki zo guri ba, ubangiji Allah ya tayar miki da wannan k’uruciyar iya haka”.
COMMENT VOTE AND SHARE
[9/26, 11:14 AM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????LADIDI????????????
????♀????♀????♀K’WADAGA????♀????♀????♀
NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}
ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????
We are here to educate motivate and entertain aur reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM