LADIDI KWADAGA COMPLETE HAUSA NOVEL

Kwanuka da kofuna ne a jere, tun daga cikin gidan har zuwa soro, kowa naso layi yazo kanshi, har da maza a tsatstsaye a waje suna jira a mik’o musu, yawancin su masu wuce wa ne,, shine take d’aura musu a Leda,, duk wannan aikin ita kad’ai takeyi tayi-tayi da Ladidi ta futo ta taya ta tak’i dake yau alhamis babu makaranta, tana cikin daki tana jin haushi, saboda ko yau da safe sai da Kawunta ya kara maganar aske mata gashi, shine take gaba da Mai koko tak’i kula ta,, hayaniyar yara ce tayi yawa kowa yana ganin kamar za’ayi masa zure,,, da sauri ta bankad’a labule ta futo, fud’um-fud’um, kai tsaye hanyar futa ta nufa,, Sam Iya ba taga futuwar ta ba dake ta juya baya,, tana zuwa inda jerin kwanunkan suke, sai ta fara d’ebo na k’arshe tana mai dasu gaba, na gaba ta dawo dasu baya,, ta hargitsa layi,, Iliya yana tsaye yaga kofunsa ya dawo baya yace”Ke Ladidi mayar min dashi inda yake sai da kika ga an kusa zuwa kaina zaki hargitsa layi” kai tsaye tace”Bazan mayar ba” ruk’e k’ugu tayi tana kallonsa,, a zuciye ya nufi inda kofunsa yake yaje ya dawo dashi inda yake,, aikuwa bai gama ajiye shi ba,, ta d’auka tayi wurgi dashi waje,, takaici yasa Iliya kai mata duka, itama ta kai masa,, kafin kace kwabo fad’a ya rincab’e a tsakaninsu,, wata yarinya ce ta futo hannunta d’auke da kwano Wanda yake cike da koko sai turiri yake,an sallame ta,, babu zato Ladidi ta ingiji ta kokon ya kife a jikinta, yarinyar ta kurma ihu!!!”Wayyo Allah na””” Iya ta saki ludayin hannunta da sauri ta nufi soro,, Me zata gani, Ladidi da Iliya ne suke kokawa katitir! Duk da Iliya yake namiji wanda ya girmi Ladidi da shekaru kusan biyar, ya kasa yin galaba a kanta, duka take kai masa ta ko ina tana k’okarin tad’o k’afarsa da tata k’afar, in ka kalleta a lokaci sai ka rantse da Allah ba Ita bace, duk kamaninta sun sauya,sai naushi take kai masa tana cakumar sa,, Mai koko ta rasa gurin wanda zata nufa,, ga Aminoni tana Ihu!!! Koko ya k’ona ta,, ga Ladidiya can tana d’aban albarka.
COMMENT VOTE AND SHARE
[9/27, 5:17 PM] 8k: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
????????????LADIDI????????????
????♀????♀????♀K’WADAGA????♀????♀????♀
NA
BINTA UMAR ABBALE
~®BINTUBATULA????~
MARUBUCIYAR
NANA KHADIJA
YARO DA KUDI
GIMBIYA BALARABA
TSANTSAR BUTULCI
LOODING:
{LADIDI K’WADAGA????}
ZAMANI WRITES ASSOCIATION????????
We are here to educate motivate and entertain aur reades
DEDIGATED
TO
RAHAMA ALIYU
ALHERIN ALLAH YAZO INDA KIKE
NANA AISHATU KADUNA
Hak’ika ina jin dadin comment dinki ubangiji Allah ya bar kauna,Aishatu inai miku fatan alkairi a rayuwar ki????
BISIMILLAHIR-RAHAMANIR-RAHIM
????10
Da k’yar Iya ta taimaka wa Aminoni ta cire rigarta ta goge mata jikinta tana ta faman yi mata sannu, ita ko sai sosa inda yake mata zafi take tana kuka,, baki na rawa Mai koko tace”ina ne yake miki zafi” ? Aminoni ta nuna mata k’irjinta da gefen hannun ta,aikuwa tana dubawa taga gurin yayi jajazur har ya soma tashi, cikin gida ta shige da sauri tana salati,,,,, zuwa yanzu mazan dake waje sunji abunda yake faruwa nan suka shigo suna aikin raba fad’a inda Ladidi ta dunga Kai musu duka tana zaginsu duk girman su kuwa, da yake duk sun san halinta,suka k’yaleta k’okarin su fuzge Iliya da tayi masa rik’on tsauri,, Iliya da ya samu ta sake shi sai yayi waje yana maida nuffashi,, ita ko Ladidi gefe ta koma tana haki! Bakin ta bai mutu ba, tana ta zagin Iliya da masu roban fad’a,, futa sukayi suna mamakin rashin kunyar ta,, bakin kofar ta tsare tana kallon Iliya tace”Wallahi baza a siyar maka da kokon ba, don haka kasan inda dare yayi maka,, bai ce mata komai ba d’auki kofunsa ya tafi,,, cikin takaicin na bata lokacin sa da yayi gashi gidansu duk sun fi son kokon Iya saboda ta iya ga gard’i da tsabta fari tass dashi yana k’amshin citta da kaninfari.
Mai koko ta dawo hannunta dauke da wata roba ta kad’o omo a ciki tazo tana shafawa Aminoni a jiki tana mata sannu, Aminoni kad’a kai kurum take tayiwa Ladidi Allah ya isa babu a dadi domin babu damar ta fada a fili,, rigar Ladidi ta sanya mata, ta dauki kwanon kokon ta zubo mata wani,, har waje ta rakata tana mata sannu,, mutanan dake waje ta tsaya tana bawa hakuri, sannan ta koma ciki, ko takan Ladidi bata bi ba, ta cigaba da sallamr mutane,, haka suka hak’ura da hukuncin da Ladidi tayi musu na farko ya koma k’arshe na k’arshe ya koma baya
Hajiya Asiya na zaune kan kujera tana jiran isowar su,, tayi kwalliya tsab da ita ta shiryawa shalelen ta daining shi kadai kawai ake jira,,, tana jin shigowar mota gidan ta furta Kalmar “Alhamdulilahi, idonta a kofa har suka shigo,, da sauri ya cire hannunsa daga na Salima ya rungumeta yana fad’in” Mamana I miss you!!” Shafa kansa tayi tana murmushi tace”Nima haka my Son nayi kewar ka, sati biyu kacal sai suka zama kamar shekara a gurina” lumshe idonsa yayi yana jin d’umin mahaifiyar sa mai so da kaunar sa,, G.Abbas yace”Idan ya koma can da zama kuma yaya zakiyi gwara ma ki sawa zuciyar ki sauk’i” Hakkim ya zauna hannusa rik’e da nata yana kallon Dady din yace”Wallahi Dady saboda Mama zan iya hak’ura nifa da man bai wani dame ni ba,gwara in zauna a k’asata” Dady yace”Aikin gama ya Riga ya gama tunda kaje ka saka hannu lokaci kawai ake jira”” Hajiya Asiya tace”Tashi muje kaci abunci na mussaman” cike da farin ciki suka nufi gurin cin abunci dukan su..
Bayan ya gama cin abunci part d’insa ya nufa a gajiye ya fad’a toilet yayi Wanka ya futo daure da towol a jikinsa, ko mai bai shafa ba,ya zauna gefan gado yana latse-latse a wayar sa,, kira ne ya shigo yana dubawa yaga babban abokinsa Yusuf d’aga wayar yayi tare da fad’in “Ya akaiyi ne yaro”? D’ayan b’angaran Yusuf yace” Ganin kan hanya nasan dai yanzu all ready kana gida” Hakkim yace”Ina gida hutawa kuma zanyi karkazo ka dame ni da surutun ka na ala tsine” Yusuf na k’okarin kashe wayar yace”Idan nazo kar ka bude min kofa” Kitty!ya kashe wayarsa, Hakkim yasa Dariya yana fad’in”Lallai wannan bai da mutumci ni ya kashewa waya, anyway zai zo ya same ni””” mik’ewa yayi ya d’auko boxer da singlet Cikin kayansa ya saka ya fesa turare ya koma ya zauna inda ya tashi, latse-latse ya cigaba dayi da wayarsa.. Bugun kofa Yusuf yake yana jinsa ya share shi,, kiran wayarsa yayi ya kashe,wato ya rama kenan, Yusuf ya fi minti goma a tsaye sannan yaje ya bude masa kofa,, ya shigo cikin jin haushi yace”Wallahi mugun Dan wulakanci ne kai fa” kai tsaye yace”Waye yace ka kashe min waya, abunda na tsana a rayuwa ta” Yusuf yace”An kashe d’in, dallah kai kowa sai ka gwadawa iko da mulki to ni baka isa ba””Dariya Hakkim yake masa ya bashi hannu suka tafa,, Yusuf ya zauna yana fad’in”To yane akwai labari ne”? Tab’e baki yayi yace”Ni da na dawo ni za’a bawa labari ai” Gyara zama yayi yace”Aiko akwai labari fa””””” kallonsa yayi yana kanne masa ido,, doka ya kai masa yana fad’in”Bana son iskanci fa” Sosai Hakkim yake dariya yana fad’in “Ai nasan zance gizo baya wuce na k’oki labarin ka kullum akan abu d’aya ne,, kan wannan bak’yauyiyar budurwar taka da komai bata Iya shafawa ba”” Yusuf ya b’ata fuska yana fad’in”Bana son iya shege gwara ni ina da budurwa kai kuwa fa,ka tsaya tsoron mata dube ka don Allah gemai-geman da kai to wai in kayi auran ya zakayi da ita”” ? Ya k’arashe maganar yana dariya ta shak’iyan ci,, a kufule Hakkim yace”Uwar ka zanyi da ita d’an iska” dariya Yusuf yake har da kwanciya yace”Kullum sai sweet heart d’ina ta tambaye ka,,wai kazo ta baka kanwar ta” Duka ya kaima sa,, da sauri ya goce yana cigaba da masa dariya”” cikin jin haushi yace”Idan kaje kafad’a mata ni nafi k’arfin k’azamar kanwar ta”” Yusuf yace”Aikuwa zan fada mata wallahi,, kullum in muna hira ko a wayane ina bata labarin ka da yanda kake tsoron mace sai tai ta mamaki ita tana ganin kamar k’arya nake, a wannan zamanin akwai namiji me tsoron mace kuwa,nace ta kwantar da hankalin ta zan kawo mata kai har gida”” hararasa yayi yace”Taje tayi ta mamaki, kuma Wallahi idan baka daina bata labari na,, na rantse maka da Allah har a d’aura auranku bazan jebe”.