NOVELSUncategorized
MUTUM DA DUNIYARSA 12

*_????HASKE WRITER’S ASSO…._*
*_????MUTUM DA DUNIYARSA….!!????_*
_(ya dace ya gyara kansa)_
*_Bilyn Abdull ce????????_*
*_[12…..]_*
…………..Malam Mustafa yadamu kwarai da rashin ganin Jiddah a makaranta, dan da wahala kaga tayi fashi, inhar kuwa tayi washe gari sai kaga k’annenta sunzo sun fad’i dalili, kokuma idan itace tazo tafad’i abinda ya hanata zuwa.
Madina ma ta damu da rashin zuwan Jiddah, gashi ko gidansu bata saniba, dan duk iyakar shakuwarsu k’awancen iya makaranta ya tsaya, sai a yaumane takejin takaicin hakan.
Da aka tashi Malam mustafa yaso zuwa gidansu Jiddah, amma sai wani uziri ya rik’eshi, dole ya hak’ura akan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu.
Saikuma da yamma malam yay kiranshi a waya akan yazo yana nemansa.
Bai samu ganin malam ba sai bayan sallar isha’i, dan ya iskeshi yana da bak’i. Bayan tafiyarsu yasamu gaisawa da malam.
“Mustafa dama akan yarinyarnanne, inaso asamo mana inda mahaifinta yake, dan inason ganawa dashi kafin musan abinyi”.
“To malam, insha ALLAH zuwa gobe zanzo na sanar maka”.
“To ALLAH ya kaimu da rai”.
Washe garima malam mustafa bai samu zuwa wajen Jiddah ba, sai dai binciko Alhaji Zakari dayayi, gidansa da wajen kasuwancinsa.
Duk yanda akai malam mustafa yazo ya sanarma malam.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Jiddah dukta fige a tsaye, da kaganta kasan tana tare da damuwa, Umma takan danne tata