RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 31 to 40

Shima sai da ya sauko kafin ya kula da ita, dama ya rigada ya fita dawowa yayi, shine yanzu zai koma

Zuwa yayi kan kujerun parlour’n ya zauna, idanun sa akanta amma fuskar sa a matuƙar murtuke yace, “kee?”

Har cikin kanta taji muryan nasa ya tsirga mata, sai dai ko ƙwaƙƙwaran motsi ba ta da alaman yi, idanun ta kafe akan abincin ko ƙyafta wa ba ta yi

Numfashi yaja yana ɗan kawar da kansa daga kallon ta, yaci gaba da maganar sa batare da ya damu da ta’amsa ko kar ta amsa ba

“Kina jina daga yau babu ke babu sake fita a gidan nan, school ɗin ki zaki dakatar dashi har sanda yayan ki zai dawo, sabida ya bani amanar ki, Ni kuma bazan bari kina fita kina yawon ta zubar alhanin an bani amanar ki ba, ya rage na ki, ki bi umarni na ko ki saɓa..” sai ya ja numfashi yana cije leɓe tare da mayar da idanun sa kan ta

Tun sanda ya soma magana tuni ta ɗago kanta ta kafa masa rikitattun idanun ta, a take a lokacin suka sake sauya kala suka rikiɗe zuwa jazur, har wani ƙyalli suke yi

Shi kansa Rayyan ya kasa jure kallon da take masa, don bazai iya tantance wani irin kallo bane, amma kuma sosai kallon ya shige sa, har tsigan jikin sa tashi yake yi.

     Ƙunci da baƙin cikin dake nuƙurƙusan RAUDHA shi ya hana ta yin magana, ga dai shi bakin ta na motsi but ta kasa furta komi, sai kawai gani yayi ta miƙe zumbur ta nufo wajen sa, a tsakiyar parlour’n ta tsaya ta hau cire kayan ta…????

.

_To fa.. meke shirin faruwa?_????????

[2/27, 9:18 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

   ????????????????????????

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

????????????????????????????????: ✍️

              ???????????????????????????? ????????????????’???????? ???????????????????? ????????????????.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????

®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓

???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️

????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????

         ????.????.????????/

.

  ???????????? ???????????????????????? ___________________________????

        ???????????????????????? ????????????????????????

_______???? Zaro idanu Rayyan yayi da tsananin mamakin ta, da sauri ya runtse idanuwan sa ganin ta saki rigan yayi ƙasa, daga ita sai gajeren wando fari ƙal da bra ɗin sa

Shaf ta manta da cewa shi soja ne sai yanzu da ta kalli kayan jikin ta taga irin nasu ne, saboda tsantsan tsanar da take masa hakan yasa baza ta iya juran ganin rigan a jikin ta ba, wannan dalilin ne yasa ta soma kwaɓe wa.

      Ɗaukan rigan tayi ta wurgo masa ajiki, ta ruga aguje tayi hanyan kichen

Rigan ya cire daga fuskar sa yana bin wajen da take da kallo, but a mamakin sa babu ita a wajen, ajiyan zuciya ya sauke da ƙarfi yana damƙe rigan a hannun sa, sai kuma ya saki a ƙasa yana miƙe wa tsaye, yayi hanyan dainning, dama abinda ya zaunar dashi kenan yaci abinci ya bar gidan, sai gashi ya haɗu da abun mamaki wajen birkitacciyar ƴar ƙwayan yarinyan nan, har yanzu mamakin meyasaka ta cire rigan yake yi

Tabbas yanzu ya tabbatar ita ɗin ba ƙaramar sheɗaniyar ƴar duniya ba ce, tunda har ta iya cire riga a gaban sa batare da ta ji kunyan sa ba.

      Yana jan kujeran ya zauna ya hange ta ta fito daga kichen, riƙe da kalanzir cikin galan da ashana a hannun ta, sakin baki yayi kawai yana kallon ta

Rigan tanufa ta ɗauka tayi waje da gudu

Shima sai ya tashi da sauri yabi bayan ta, time ɗin da ya fita tuni ta diddila wa rigan kalanzir ɗin, ta saka ashana ta ƙyasta wa rigan nan da nan ya soma ci

Tsayawa yayi kawai yana kallon ta, Allah ya sa a farandan gidan ta tsaya, kuma daga nan masu aikin gidan ko sun fito baza su iya hango ta ba, in ba sun yo wajajen ba

Hannayen sa ya saka a aljihu kawai yana bin ta da kallo.

        Sai da rigan ta kusa ƙonewa kafin ta ɗago rikitattun idanun ta ta sauke akansa, cikin dashashshiyar muryan ta da tasake shigewa sosai tasoma magana

“Yanda na ƙona rigan nan haka kaima zan yi maka sabida tsananin tsanar da nayi maka, babu wanda ya taɓa shiga rayuwata ya ƙuntata min sai kai, bazan taɓa yafe maka ba sai na kashe ka idan baka fitar min cikin rayuwa ba, na tsane ka kana ji ko, na matuƙar tsanar ka fiye da mutuwa ta, i hate youuuuuuuu! Ta ƙarishe da ƙarfi tana rugawa cikin gidan tare da fashe wa da kuka

Ko motsi ya kasa yi a wajen, idanun sa kan rigan da ya ƙurmushe ƙurmus, sosai yake cikin ɓacin rai da kalaman ta

“Wai yarinyan nan me take ji dashi ne da har take iya kallon idanun sa tana gaya masa magana irin hakan? Ko dan ya ƙyale ta? Tabbas yau zai koya mata hankali, zai saita ta ya dawo da ita hayyacin ta, idan ma ƙwayan ta ke faɗa mata ƙarya zata san wanene aihinin Captain Rayyan”.

Takawa yayi yawuce wajen motan sa, ya shiga yaja yabar gidan.

      A cikin kujera ta shige tasoma rera kuka, sosai take yin kukan har muryan ta ba ya iya fita, sai da kanta yasoma sara mata tana ganin dishi-dishi kafin ta saurara wa kanta, miƙe wa tayi ninyan yi, sai ta hangi HangBag ɗin ta kan kujera, wanda bata san ma ya akayi yazo wajen ta, don jiya bata san inda ta wulla sa ba tun da Rayyan ya ɗauko ta

Jakan ta ɗauka ta zazzage, wayan ta kaɗai ta faɗo, babu komi aciki duk da kuwa ta zuba ƙwayoyi a jakan, but kuma babu a ciki, bata damu da tabi ba’asi ba tasoma neman layin yayan ta, sai dai switch off, ƙin dena Kira tayi har sai da ta gaji don kanta kafin ta saki wayan tana sake fashe wa da kuka

Sai ta miƙe ta saka hannu tasoma share hawayen ta, har da saka bayan hannun ta, gaba ɗaya idanuwan ta da fuskarta sun haɗe sun yi jazur, musamman saman hancin ta, abun ku ga farar mace kamar zabiya

Sai da ta ɗauki wayan ta kafin tanufi

Sama da gudu tashige ɗakin ta, Direct toilet ta faɗa ta sake sheƙa wankan ta, ta fito tayi shirin ta cikin ƙananan kaya, wando ta saka ɗan guntu iya cinyan ta Brown colour, sai ta saka farar riga me shara-shara da zanen layi-layi a jiki, ko cibiyan ta be kai ba, ta ɗaure gashinta a tsakiyar kai da Ribom baƙi, sannan ta zira Hill shoes black

Inda take ajiye kayan zaƙin ta tanufa, ta ciri Chwingum ta ɓare tare da jefa wa a bakin ta, feshe jikin ta tayi da turaruka ko ta ina, sannan ta ɗau HangBag ɗin ta ta fito, yanda take takawan ne tamkar ba ita ba, gaba ɗaya ta saki jikin ta ta koma normal sai taunan Chwingum ɗin ta take yi

So take yi ta nuna wa Rayyan be isa da ita ba, shiyasa ta yanke shawaran barin gidan, kuma baza ta dawo ba sai sanda taga dama.

      Waje ta nufa tashige motan ta taja zuwa bakin Gate, horn ta soma buga ma me gadi, but ko ƙeyan sa bata gani ba, kuma taƙi ta dena sai faman danna horn ɗin take yi tamkar zata ta da gidan

A fusace tafito a cikin motan tanufi bakin Gate ɗin, ganin ƙofan ɗakin me gadin a rufe yake sai taja tsaki, ta nufi Gate ɗin ta saka hannu zata buɗe, sai dai kuma an rigada an garƙame Gate ɗin da kwaɗo, buga ƙofan tayi da hannun ta tajuyo a fusace tana kwaɗa wa me gadin kira, jin shiru kuma tana ɓata wa kanta time sai ta buɗe small Gate zata fice

Sojoji ne su wajen goma a bakin ƙofan taci karo da su, sai taja da baya tana cire ƙafanta da ta taka ƙofan zata fice, da idanu ta dinga bin su tana sake tamke fuska, don a tunanin ta har da Rayyan a wajen ne, duk da zuciyarta sosai ta cika da tsoro

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button