RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 31 to 40

Ɗan guntun murmushi Ray yayi a ransa, ya dubi abokin nasa yace, “Suhaib kana nufin wai yarinyan nan ita ce RAUDHA? Ita ce ta koma haka? Wannan tarbiyyan dama kuka ba ta, kana ganin hakan me ɓulle wa ne? Shin wani irin gata ne wannan da kuka nuna mata har ta zama haka?”

Fuskar Suhaib cike fal da damuwa yace, “Dude zauna muyi magana”.

Babu musu Ray ya zauna, kasancewar ya ga damuwa ƙarara a fuskar abokin nasa, shiyasa be masa musu ba yayi yanda yake so

Shima kuma Suhaib ɗin zama yayi a gefen sa.

     Tattaunawa suka soma yi, sun daɗe kafin su gama, sannan Suhaib ɗin ya fito, ɗakin RAUDHA dake kallon na Rayyan ya nufa, sai dai a rufe yake, be yi yunƙurin ƙwanƙwasa wa ba don ya san baza ta saurare shi ba

Ya daɗe anan tsaye a corridor ɗin saman, yana jingine jikin ƙarfen wajen, har sai da ya gaji don kansa kafin ya sauko ƙasa ya wuce ɗakin su.

????????????????????????????????

      Tun daga ranan kuma RAUDHA ta hau fushi da kowa da ke gidan, da zaran ta fita ba ta sake dawowa sai dare

Ko Suhaib ya tunkare ta yana ba ta haƙuri, tare da lallaɓa ta, ko kallo be ishe ta ba, da zaran ma ya same ta a waje tashi take yi ta bar shi

Shi kuwa Rayyan ma basu sake haɗuwa ba, tunda ba ya zama shima agidan sosai, sai dare yake dawowa, kuma idan ya dawo time ɗin ko RAUDHA na wajen yawon ta, ko kuma tana ɗaki.

       Yanzu gaba ɗaya ta maida kanta kullum a buge take, karatun ma ba kullum take zuwa ba, sai ta ga dama.

     Ahaka har aka shafe sati guda, gashi su Suhaib har sun gama shirye-shiryen tafiyan su ƙasan India, sai da ta ga da gaske zai tafi kafin ta dena fushi dashi, don tana ƙaunar yayan ta matuƙa, ba ta son ya tafi tana fushi dashi, zata yi missing ɗin sa sosai.

     A ranan ma da zasu tafi ƙin zuwa school tayi, ita da kanta ta ɗauke su zuwa airport, time ɗin Captain Rayyan yana wajen aiki, sun rigada sun yi sallama tun kafin ya fita da safe.

       Tana dawowa gida wanka tayi ta sauya shigan ta na doguwar riga ????iya gwiwa purple colour, sai ta saka flet shoes ???? baƙi, ta sake fice wa agidan

Direct gidan su Rash ta nufa, acan ta zauna har dare taƙi dawowa gidan, saboda rashin yayan ta, wuni tayi a buge tana ta sharan barci, da daren kuma bata dawo ba suka wuce club

Wajen sha ɗayan dare amma yanda kuka ga rana haka wajen yake, mutane ne birjik maza da mata kowa sai raƙashe wa yake yi, dayake akwai partyn da ake yi ne, that’s why mutanen suka cika, wasu na rawa wasu na zaune suna shaye-shayen su, wasu kuma na harkan gaban su, kowa da abinda yake yi

Ita dai RAUDHA tana cikin ƴan rawa ne sai raƙashe wa take yi, daga ƙarshe ma ita kaɗai aka bar wa filin tana ta rawa, ana mata tafi da ihu, suna sake koɗata tare da mata kirarin dake fasa mata kai, hakan ke sa wa tana sake zaƙe wa abun ta

Gaba ɗaya mazan wajen burin su kawai su je gare ta, domin kuwa ba ƙaramin tafiya da imanin su tayi ba, sai dai Zen da Man tare da sauran abokan su; sun baƙe-baƙe sun hana kowa.

      RAUDHA dake ta faman ihu tana rawan ta bata ma san me ake yi ba, jin ta take yi cikin nishaɗi da walwala, domin babu abinda rawa ke saka ta illa farin ciki, tana ƙaunar rawa fiye da ranta, ko wani irin ƙunci take ciki idan har zata ji kiɗa na tashi sai taji zuciyar ta tayi mata sanyi, wani nishaɗi ya tabaibaye ta.

        Jin an damƙe mata hannu, babu shiri ta tsai da rawan da take yi tana juyo da kanta ga wanda ya riƙe ta ɗin

Idanun su ne suka haɗe waje ɗaya, a take gaban ta yayi wani irin bugawar da yasa ta waro lumsassun idanun ta gaba ɗaya waje, mamaki da tsoro ne ya cika ta ganin Rayyan tsaye a gaban ta tamkar wani zaki, gaba ɗaya ya haɗe fuskar sa kamar be taɓa sanin wani rahma ba, fararen idanuwan sa kuwa sun yi wani luhu-luhu sun yi jazur har wani ƙyalli suke yi

Sosai RAUDHA ta tsorata da ganin sa, domin dai bata taɓa tunanin ko a mafarki zata iya ganin wannan halittan a inda take ba..

Jin ya soma jan ta zai bar wajen da ita, nan ta aro jarumta, cikin tsananin fushin da bata san dalilin yin sa ba ta buɗe baki cikin dashashshiyar muryan ta tace, “How dare you! Da zaka taɓa min jiki da wannan banzan hannun naka? Zaka cika Ni Ko sai na baka kashi?”

Juyowa yayi ya tsaya yana kallon ta, ransa idan yayi dubu to a ɓace yake, sai dai ya san idan har ya biye mata, to, tabbas zai iya kakkarya ta anan wajen.

     Su Zen da basu san lokacin da Rayyan ya iso wajen RAUDHA ɗin ba, tsaya wa kawai suka yi suna mamakin ganin mutumin da sam babu alamun sauƙi a tare da shi, musamman ma yanayin jikin sa ka san ya kai a kira sa cikin zaratan maza, waɗanda ko kallon su kayi sai ƙirar jikin su ya baka tsoron tunkaran inda suke.

Ganin ya ja RAUDHA kiiiiii.. yayi hanyan fita da ita, sai gaba ɗayan su suka yi kansa

Sai dai basu kai ga yin taku uku ba, ya nuna musu bindiga, cikin kakkausar muryan sa me firgitar wa yace, “wlh duk wanda ya sake yin taku ɗaya acikin ku, sai dai uwar sa ta haifi wani”.

Tuni ya juya ya fice ko sake bi ta kansu be yi ba, bare ma ya saurari RAUDHA dake faman yakushin hannun sa tana son ƙwace wa, sai ƙunduma masa zagi take yi.

     Sai da ya fice gaba ɗaya a wajen kafin su Zen sukai waje da gudu, don a tunanin su sace ta yake son yi, amma abun mamaki suna fita suka gansa ya jefa RAUDHA cikin motan sojoji, hakan ya sake firgita su, ai kowa sai ya nufi hanyan tsira ganin hukuma ne da kan su, suna ganin ya ja motan ya bar wajen, su ma sai suka nufa motocin su kowa na ta kansa, don a tunanin su sojojin zasu dawo su da yawa su farmake su ne.

[2/26, 1:34 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

   ????????????????????????

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

????????????????????????????????: ✍️

              ???????????????????????????? ????????????????’???????? ???????????????????? ????????????????.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????

®Ɗ???????????? ???????????????????????? ???????? ????????????????????✓

???????????????????? ???????????????????????? ????????✍️

????????????????????????????: ????????????????????????????????????????????????

         ????.????.????????/

            ????????????????????????

    _Sallah ta ƙwarai, ingantacciya, wadda aka yi ta cikin tawali’u da ƙasƙan da kai, tana haskaka zuciya, ta tsarkake ta, kana tana koya wa mai yin ta tsantsar hanyar Ibada da abubuwan da suka rataya a kansa, waɗanda suka shafi Ubangijin sa, don kuwa ta sallah ɗin ce girma da ɗaukakar Ubangiji za su tabbata a zuciyar sa. Sallah tana sa mutum ya zama sahihi, mai gaskiya da riƙon amana, mai fahimtar abubuwa, mai kunya mai auna kome yake yi, mai yawan kyauta. Tana daɗa nuna masa cewa dai Allah Ɗaya ne, yana kuma jin tsoron sa, yana kuma girmama shi. Ta yin Sallah ne yake inganta rayuwar sa, ya tsarkake zuciyar sa, ya nisanci ƙarya da makirci, zamba, fushi da fariya, gaba, tauye wa mutane haƙƙi, rowa, ƙeta da rashin biyayya, da dai sauran miyagun halaye._

           _Sallah Ibada ce ta zuci da ta jiki. Mai yin ta zai haskaka da harshen Allah. Yin Sallah shi ne babbar alamar cikar imani, mafi darajar hanyoyin Ibada, kuma hanya mafi tabbata ta nuna godiya ga Allah, saboda tarin baiwar da ya yi mana. Yin watsi da Sallah yana nesanta mutum da Allah, ya rasa rahamar Sa da falalar sa da jin ƙan sa._

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button