RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 31 to 40

     _Martabar sallah ta Kai ma cewa mutum ba ya iya barin ta acikin ko wane hali ya sami kansa. Dole ya kawo ta ko yana tafiya ko yana gida, ko cikin tsoro ko cikin aminci. Allah Ya sa mu dace._

.

  ???????????? ???????????????????????? ___________________________????

        ???????????????????????? ???????????????????????? ????????????????

_______???? Sanda ya jefa ta cikin motan sai da kanta ya bugu sosai da jikin kujera, hakan yasa ta dafe kanta tana me fashe wa da kuka, yunƙura wa tayi don ta tashi amma ta kasa, dole ta dakata domin kuzarin ta yadawo, tana runtse idanun ta tana ci gaba da kukan ta

Shi kuwa tuƙin sa kawai yake yi be damu da kukan nata ba

Daƙyar ta samu ta ɗago daga kwancen da take ƙasan kujera, a fusace tasoma ƙoƙarin buɗe ƙofan don ta fice, amma kuma ya rigada ya saka luck, dole ta dakata tana sake fashe wa da kuka cike da hasala, idanun ta ta sauke akansa da suka cika da ruwan hawaye, cikin kuka da ɗaga muryan ta da ba ya fita tace, “kaii ɗan tasha ka sauke Ni in fita, wai meye haɗina da kai ne? Me na tare maka? Uban wa ya aiko ka ka ɗauke Ni?”

Rayyan be da alamun kulata sai ma ƙara Speed da yake yi, danne ɓacin ransa kawai yake yi don ba ya so ya nuna masa ainihin wanene shi a yanzu

Ita kuma shirun da yayi mata yasa ta sake fusata, ta miƙe a ƙufule ta hantsala gaban motan, babu wata-wata tasoma ƙoƙarin murɗa sitiyarin motan, nan da nan motan ta fara tambal-tambal akan titi, Allah yaso dare ne sosai babu ababen hawa, da tuni sun yi hatsari

Duk yanda ya so ya tsayar da ita wajen riƙe mata hannayen ta, but ya kasa, dole ya ja wawan burki a tsakiyar titin, wanda yaja RAUDHA tafaɗo jikin sa suka gwara kai

Gaba ɗayan su sun ji zafi, musamman RAUDHA da sai da numfashin ta ya ɗauke na wucin gadi, sabida azaban da taji sai da tariƙa ganin taurari suna gifta mata, kasancewar ta bata saba shiga wahala ba, bata ma san shi ba a rayuwan ta

Shi kuwa Rayyan duk da zafin da ya ziyarce shi, sai yaji gaba ɗaya ya ɗauke sakamakon runguman da RAUDHA tayi masa, sai kawai tunanin sa ya tsaya cak yana sauraron wani irin baƙon yanayin da ya ziyarce shi, ga shi tarigada ta kanainaye shi, ta tusa kanta cikin ƙirjin shi ko motsin kirki bazai iya ba

Wani irin numfashi yaja wanda ya dawo da RAUDHA duniyar mutane

Dasauri ta ɗago kanta tana kallon shi, wanda hakan yasa idanun su suka faɗa cikin na juna, zaro idanu tayi ganin fuskarta kusa da nashi, sai tayi saurin duba inda take ɗin da har ta samu kusanci dashi haka, ganin ta akan jikin sa ai babu shiri tayi wani irin zame wa takoma kujeran me zaman banza, tana mayar da hannun ta saman kanta da har yanzu yake mata zugi, take ta runtse idanun ta tana me sake fashe wa da kuka

Da kallo yabi ta dashi tamkar wani soko, ko kaɗan ya kasa kataɓus bare wani muhimmin tunani

Idanunta ta ɗago da suka yi jazur ta sauke kansa, wani irin kallon tsana take aika mishi dashi wanda bata taɓa yi wa wani mahaluki ba, zuciyarta sai ta farfasa take yi, haka ma jinin jikin ta, ji take yi tamkar ta shaƙe shi ta kashe shi ko zata dena jin raɗaɗin da ke baƙuntan ta.

Juyawa tayi ta buga ƙofan don ta buɗe, sai dai har yanzu akwai luck, jijjiga ƙofan ta hau yi tamkar zata ɓalla, sai buga wa take yi amma ko alamun motsi ba ya yi

“Wlh idan har baka buɗe ƙofan nan ba, sai na kashe ka! Sai na maka kisan gilla”. Tayi maganar a tsananin fusace jajayen idanun ta akan sa

Kallon ta kawai yake yi yana nazartan ta, so yake yi ya gano ainihin abinda ke ranta domin dai yarinyan abun mamaki ne da ita, shi gani yake yi ko tasha ƙwayan nata ne ta bugu, don haka be sake bi ta kanta ba yayi wa motan keey yaci gaba da tafiya

RAUDHA kuka ta fashe dashi ganin be kula ta ba, itama sai bata sake yunƙurin yin wani abu ba, ta lafe a jikin kujeran tana ci gaba da kukan ta, jira kawai take yi taga inda zai kai ta, da abinda yake shirin yi, idanun ta a rufe suke, bata sake buɗe su ba sai da taji tsayuwar mota, ɗago kanta tayi tana kallon inda suke, a mamakin ta sai taga sun dawo gida ne, juyawa tayi wajen sa, amma kuma shi tuni ya fice a cikin motan

Jin an buɗe inda take ne, tayi saurin juyowa tana kallon sa

Shine tsaye ya haɗe giran sama da ta ƙasa, fuskar nan babu walwala yace, “fito”.

Ko motsi taƙi yi, sai ma ɗauke kai da tayi tana sake matso hawaye

Hannun sa ya saka ya finciko ta waje, jan ta yasoma yi zuwa ciki, amma ita kuma tana tokare wa baza ta je ba, tare da bugun hannun sa akan ya sake ta

Dole ya saka mata ƙarfi ya ja ta ciki, suna shiga ya jefar da ita kan kujera, ya koma ya rufe ƙofan da keey, dawowa yayi be ce mata komi ba ya haura sama.

    Dasauri ta tashi ta biyo bayan sa tana zagin sa da gaggaya masa maganganu, amma ko ta kanta be yi ba ya rufe ƙofan shi

Ajikin ƙofan ta zube tana dukan ƙofan tana kuka tana faɗa masa “yazo ya buɗe ta takoma inda ta fito”. Tamkar mahaukaciya haka takoma sai bugun ƙofan take yi taƙi ta haƙura, kuma bakin ta yaƙi yin shiru.

Sai da takai har gabanin asuba a zaune a wajen sabida jaraba, ita bata dena kukan ba kuma bata dena surutun ta ba

Shi Rayyan ma har yayi barcin sa, don be san ma tana yi ba.

Rarrafa wa tayi tashige ɗakin ta, akan kujera ta kwanta tana sauke ajiyan zuciya, nan da nan barci ya ɗauke ta kasancewar shi ne fal a idanun nata, amma taurin kai da naci ya hana ta sararawa kanta, da takalmin a ƙafan ta tayi barcin ta.

      Bata farka ba kuwa har ƙarfe biyun rana, a lokacin da ta tashi sosai kanta yake mata ciwo sabida kukan da tasha jiya, idanun ta ma daƙyar take iya buɗe su, fuskarta gaba ɗaya ya yi jazur tamkar tattasai, musamman wajen idanun ta, kasancewar sun kumbura sunyi luhu-luhu

Miƙe wa tayi daƙyar tasoma cire kayan jikin ta, wanka tashige ta hau zuba ma kanta ruwa tun daga saman kanta, ta jima a tsaye ruwan na dukan ta idanuwan ta arufe ruf, sai da ta soma jin dama-dama sannan ta hau yin wankan, bayan ta gama tafito ɗaure da towel ajikin ta, gaban dressing mirror tazaun bayan ta jona socket ɗin handrayer, ta hau busar da baƙin gashin ta da ya kwanta a bayan ta, tana yi tana kallon kanta a mirror, fuskar ta ko alaman walwala babu, kumburin da yayi har yanzu be ragu ba, har ta gama zuciyarta a cinkushe take, miƙe wa tayi ta isa gaban Sip ɗin kayan ta tabuɗe ta soma ciro kayan da zata saka, cikin sauri take shirin ta sabida yunwan dake azalzalan ta

Biri da wando me siraran hannu ta saka, kalan sa tamkar kayan sojoji haka yake, sai dai wannan ya cika duhu sosai, amma kuma suna amfani dashi sojojin, dayake me haɗe da Socks ne shiyasa bata tsaya saka takalmi ba tafita da gudu, Direct ƙasa tanufa tayi wajen dainning

An jera abinci da alamu yanzu ma kukun ya gama, domin da ta buɗe coolarn abincin sai faman tururi yake yi

Zuba wa ta hau yi cikin Plate, ta saka spoon ta soma ci kanta a ƙasa, ko ɗago kai ba ta yi, abincin kawai take aika wa bakin ta, wanda idan ta kai ɗaya sai ta ɗau sokonni kafin ta sake kai wani.

Ray ne ya sauko daga saman da kakin sojojin sa ajikin sa, sosai suka yi masa kyau suka sake haska farar skin ɗin sa, tare da ƙawata ƙaƙƙarfan ƙirar jikin sa, wanda kallo ɗaya idan kayi masa zaka san Jarumin namiji ne na bugawa a jarida.

     Takun takalmin sa yasa RAUDHA ta ɗago kai, kallo ɗaya tayi masa ta mayar da kanta ƙasa, sai dai ta kasa ci gaba da cin abincin illa juya cokolin da take faman yi aciki

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button