RAUDHA Page 31 to 40

Su kuma shigowa suka yi ciki ko wannen su da bindiga a hannu
Ɗaya daga cikin su ne yace, “Ma’am ki koma ciki sabida an ce kar mu bari ki fita”.
Bata saurare su ba, tayi hanyan fita tana son raɓa su ta fice
Wanda yayi maganar yace, “Ma’am ko ba kya ji ne? Ki koma ciki tun kafin mu ɗau mataki akan ki, domin Oga ya ba mu dama idan kika yi mana taurin kai mu harbe ki”.
Ko kallo basu ishe ta ba, duk da kuwa ranta idan yayi dubu to ya ɓaci, har fuskarta da ya so ma dawowa normal ya canza kala
Kare ƙofan suka yi, har da rufe wa
Dole taja ta tsaya tana bin su da kallo tamkar idanuwan ta zasu faɗo ƙasa, sai dai kuma yanda zuciyarta gaba ɗaya ta cinkushe ta kasa musu magana, duk da kuwa aranta akwai tsoron su but ta danne
Ganin tana neman musu taurin kai, sai ogan cikin su ya saita bindiga akanta ya harba gefen ta
Ai tuni ta tsure ta kurma mahaukacin ihu, duk da kuwa muryan ta ba ya fita, jikin ta na rawa tayi hanyan gidan a guje
Hakan sai ya ba su dariya, suka hau yi suna bin ta da kallon sha’awa, sai dai gargaɗin Rayyan a gare su yafi komi illa a gare su idan suka saɓa masa
Ogan na su ma har da sake harba bindigan sabida shaƙiyanci
Daga inda take tana jiyo dariyan da suke mata, hakan sai ya sake tunzura ta ta ɓarke da kuka, bata tsayar da gudun nata ba sai da tashige ɗakin ta ta faɗa kan gado ta sake fashe wa da kuka, kuka sosai take yi tana hargitsa gadon tare da banga wa Rayyan zagi ta uwa ta uba, sai kuma ta miƙe zumbur tanufi drowern da take ajiye ƙwayoyin ta ta buɗe, babu komai aciki gaba ɗaya an kwashe. Fridge ta nufa da sauri shima ta buɗe don ta ɗauki wine, amma nan ma babu komi sai drinks da aka zuba mata
Nan ta haukace ta soma ihu tana bige-bige tana kiran sunan Rayyan, tamkar mahaukaciya haka ta koma gaba ɗaya sai da ta hargitsa ɗakin, hannayen ta sai zubar da jini suke yi sabida har Centre table sai da ta fasa, kuka take yi kashirɓan har da majinu, sai da ta gaji don kanta tazube a ƙasa ta kifa Cikin ta da kanta a ƙasa sai ajiyan zuciya take yi, gaba ɗaya ta gama hargitsa gashin kanta.
Bata san iya awannin da ta ɗauka ahaka ba, ko motsin kirki taƙi yi, tunda ta kafa kanta bata sake ko motsawa ba, illa numfashi da take sauke wa akai-akai.
Zumbur ta tashi sabida jiyo kamar an buɗe Gate, bakin window ta nufa ta yaye labulen, hango Rayyan da tayi cikin mota ya fito sai tayi saurin nufan ƙofa tafice da gudu
Time ɗin da ta kai cikin parlour’n, shima ya sawo kai ciki, da kallo ya bi ta sabida ganin ta a hargitse, ga hannun ta dake bushe da jini
Duk da yayi mata kwarjini tare da cika mata ido but hakan be sa ta dakata daga abinda tayi ninya ba, da gudu ta sheƙa gun sa, babu tsammani yaji ta shaƙo wuyan rigan sa ta kai ma fuskar sa nushi
Ba don Allah ya sa ya kau da fuskar ba, sai ta same shi, da tsantsan mamakin tsageranci irin nata ya cafke hannun ta gam, haka ma ɗaya hannun da ta kawo zata buga masa
A zuciye tasoma zagin sa tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta, idanun ta sai zubar da ruwan hawaye suke yi
Ko motsi ya gaza yi illa riƙe tan da yayi gam, danne zuciyar sa kawai yake ƙoƙarin yi sabida yanda yake jin ɓacin rai da irin zagin da take masa, tunda yake a rayuwa babu wanda ya taɓa masa cin mutunci, but wannan tsagerar yarinyan ƴar tatsitsiya tana gaban sa tana zagin sa, sai kawai ya lumshe idanun sa jin hawaye na son zubo masa, yawu kawai yake haɗiye wa sabida tsantsan ɓacin rai da baƙin ciki
Lokaci ɗaya ya buɗe jajayen idanuwan sa ya aza kanta, da hannu ɗaya ya matse hannayen ta gam tamkar zai karya mata su
Azaban da ya ratsa RAUDHA tuni ta dena buzge-buzgen da take yi da zagin na sa, kuka ta fashe dashi tana ƙoƙarin zame wa ƙasa da son ƙwace hannun ta, but ya ƙi saki
Jan ta yayi zuwa cikin parlour’n ya jefar da ita, sai da kanta ya bugu da kujera
Ƙara ta saki tana dafe tsakiyan kanta
Ya daka mata tsawan da sai da ta ɗago rinannun idanuwan ta ta aza kansa
Tamkar zaki me farautar namomin dawa haka ya koma mata, idanunsa gaba ɗaya sun juye, sai jijiyoyin kansa da suka fito raɗo-raɗo, cikin kakkausar amon murya yace, “keee! har kin isa kin kai matsayin da zaki ci kwalan riga na? Kina da hankali kuwa?”
Sai kuma ya matse bakin sa yana nuna ta da yatsa, at the same time ya ɗauke hannun sa tare da dunƙule wa ya kai wa iska naushi
“koda yake ƙwayan ki ne ke faɗa miki ƙarya har kike tunanin yi min rashin kunya ko? Shashashan yarinya ƴar ƙwaya sauran maza ballagaza! Idan kina taƙaman ke ƴar iska ce me bin ko wani banzan na miji, Ni Ni Rayyan Hassan!”
Ya nuna kansa yana sake ware idanuwan sa akanta, cikin fushi da ɗaga murya yace, *”NA FI ƘARFIN KI HAR ABADA,* na wuce da sanin ki, ba na harka da sauran maza, baki da abinda zaki iya burge ni, idan kina so ki haɗa gwanji dani ki je ki soma samun tsarkin Musulunci, sannan ki tsarkake ƙazantacciyar jikin ki sai ki dawo ki sake taɓa ni, jahila mara ilmi mahaukaciya, tirrrr dake!”
Ya tsit ta miyau gefe ya nufi sama da sauri
Cusa kanta tayi tsakiyar cinyoyin ta tana wani irin kuka tamkar ana fid da ranta, kalaman sa kawai suke mata yawo a cikin ƙwaƙwalwa, take ta ƙwalla ƙara ta ɗauki flowern dake saman Centre table ta rotsa shi akan table ɗin, nan da nan suka tarwatse har flowern, zafi da ƙuncin da take ji cikin zuciyarta yasa ta ɗauki kwalban ɗaya ta soma yanka hannun ta don samun rage raɗaɗi, but babu abinda yayi mata illa baƙin ciki da ƙunci dake nuƙurƙusan ta, ji take yi tamkar ta haɗiye zuciya ta mutu, har wani ɗaci-ɗaci take ji a maƙogwaron ta, idanunta gaba ɗaya sun kaɗa sun yi jazur har wani kore-kore suke yi sun daɗa ƙanƙance wa, kuka kawai take yi tana faɗin “ta tsane shi”, ko kaɗan ba ta jin zafin yanda take yanka jikin ta kamar yanda take jin raɗaɗi a zuciyar ta, wani irin tsantsan tsanan Rayyan ke ƙara wanzuwa a cikin zuciyarta a ko wani socond, yana bi ta magudanan jinin ta yana aika mata ta jijiyoyin jikin ta
Ko ta ina sai da ta yayyanka hannayen ta, sai zubar da jini suke yi, tamkar mahaukaciya haka ta miƙe tana jefar da glass ɗin tayi upstairs tana layi, ɗakin ta ta shige tanufi bakin gadon ta ɗauki wayan ta, ko kaɗan bata damu da yanda jinin ta ke yawo yana zuba tamkar an kunna famfo ba, burin ta kawai ta dace da kiran yayan ta
Numban sa na ƙasan waje ta lalubo ta kira, but be ɗaga ba har sai da tayi masa two missed call sannan ya ɗaga, jin muryan yayan ta a dodon kunnen ta sai ta saki wani marayan kuka tana kiran sunan sa
Wlh bazan iya fasalta muku tashin hankalin da ya shigi Suhaib ba, gaba ɗaya ya rikice ya kiɗime da jin kukan ƙanwar ta sa, musamman yanda ya fahimci tabbas tana cikin wani mawuyacin hali
Numfashi kawai take ja kafin ta samu jarumtar haɗo kalmomin bakin ta
“Ya..ya, ya.. yA! Na tsane shi na matuƙar tsa..nar sa fiye.. da mutuwa na, yaya bazan taɓa barin.. sa ba, sai na kashe sa wlh.. da hannu na zan kashe sa, me yake taƙama dashi meye yafi Ni dashi? Y..a..ya..ya I want to be a SOJA.. becouse.. becouse…”
Sai ta fashe da wani irin kuka me tsuma rai, cikin rawan baki tace, “zannn nuuna masa be fi.. ƙarfi na.. ba… Dai-dai nake daa..shi, INA SON ZAMA SOJA YAAYA”.
[3/16, 2:45 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????