RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 31 to 40

Hannu ta saka ta ɗauki wayan ta buɗe ta soma karanta wa:

“`”Soyayya abar girmamawa da tarairaya ce, ko kusa kada kiyi tunanin cewa soyayya ƙarya ce, sam ba ƙarya bace, domin tana da asali da tushe ko nasaba mai girma daga mahaliccin kowa da komi. Kiyi tunani Pretty”.“`

     Ta maimaita wannan ɗin a ƙalla sau uku, so kawai take yi tayi tunani irin na masu hankali but ta gaza, sai ta ajiye wayan ta sake gyara kwanciyar ta, sai dai wannan karon bata rufe idanun ba, ta tsira wa jikin bango idanu tana me afka wa tunani akan sanin “wai shin menene so? Sannan wanene wanda yake turo mata saƙon nan? Sannan me yake nufi dasu ne?” But ko kaɗan zuciyar ta bata taɓa mata tunanin ta kira Numban ba, ko kuma taji wanene, domin bata buƙatar hakan.

      Ahaka har barci ya ɗauke ta bata sani ba.

.

_Plz more Comments, more typing.. ku ƙara yawan Comment domin jin daɗina._

[3/16, 3:40 PM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

   *RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR:* ✍️

              _Nafisat Isma’il Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*

 

???????????????????????? ????????????????????????’???? ????????????????????

“`®Ɗaya tamkar da Dubu“`????✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*????

         *F.W.A????/*

.

  *NOT EDITED* ___________________________????

        *SEASON THIRTY THREE*

_______???? Yanzu RAUDHA gaba ɗaya ta dena fitowa ko ƙofar ɗakin ta ne, kullum tana ɗaki komi na ta a ɗaki take yin sa, kuma tayi hakan ne duk sabida nesan ta kanta daga haɗuwa da Rayyan, duk da some time yana shigowa har ɗakin ta ya duba ta, amma ko kallo be ishe ta ba, duk maganar da zai yi baza ta kula sa ba har ya fice, sosai ta tsane sa fiye da komi da kowa dake duniya, musamman yanda Rash ta kira ta; ta sanar mata sun soma Exams, tayi yunƙurin sake fita but bata samu dama ba, wannan dalilin ne yasa ta sake tsanar sa a ranta, duk son ta da karatu gashi tana ji tana gani wani banza ya hana ta fita, a ranan kwana tayi kuka, kuma ta rufe ƙofar ta har tsawon kwanaki taƙi ta buɗe, duk bugun da Rayyan zai zo yayi ma ƙofan tana ji, amma ba ta buɗe wa kuma ba ta kula sa, haka zai gaji yabar wajen, kuma be daina tura mata saƙo ba na kalaman soyayya, tun tana ɓata time ɗin ta tana karanta wa har ta dena

Yanzu ta kai ko sallah ma da take yi ta dena da daɗe wa, tuni ma ta manta cewa ana sallah, idan tana jin ƙunci sai ta kunna music a ɗakin ta ƙure ƙara, hakan ke saka take samun nishaɗi a zuciyarta, sabida yanzu ko yayan ta ta dena ɗaukar wayan sa har yanzu fushi take yi dashi.

     Ahaka rayuwan taci gaba, har yanzu wajen sati biyu kenan da tafiyan su Suhaib, an samu an yi wa Haneep aiki a ciwon dake cikin sa, tun sanda suka isa can da kwana biyu, yanzu haka zuwa nan da Three weeks ake son sallaman su, kuma alhmadulillah ciwon da yake fama dashi shima ana neman magani, kuma suna ganin sauƙi ba kamar da ba.

      Sanda suka cika kwanakin dawowar su, ana gobe ya kira Rayyan ya sanar masa, sai dai a time ɗin ma Rayyan kwana biyu kenan ba ya nan, a ranan shima zai dawo.

      Lokacin da ya dawo wajen ƙarfe 10:00pm. Ne na dare, ya so ya shiga yayi wa RAUDHA albishir ɗin dawowar Yayan ta, sai kuma yaga hakan be dace ba tunda dare yayi, sai ya bari sai gobe.

      Ɗakin sa ya wuce, wanka ya soma yi da ya shiga, ya saka jallabiya fara ya hau gabatar da sallan isha’i da be yi ba.

          ????????????

      RAUDHA a time ɗin tana tsaka da barci, sai ta hau mafarkin da ta saba yi a kwanakin baya, ga ta a ƙaton baƙin jeji da manya-manyan halittu masu ban tsoro, wannan dai macijin da ya saba bin ta yau ma shi yabi yo ta, su kuma sauran halittun suna sakin wani irin gurnani da dariya me tsananin sautin da ya mamaye ilahirin jejin..

A dai-dai nan ta farka tana kurma ihu, gaba ɗaya komi dake faruwa a mafarkin sai da ya dawo mata ƙwaƙwalwa, hakan ya haddasa mata mugun tsoro har take ganin tamkar ga macijin ya biyo ta a gaske, dama ga ɗakin yayi duhu tana jin ihu, ai aguje ta dira daga kan gadon tayi hanyan waje cikin firgice wa.

         A haukace ta burma ɗakin Rayyan, sai ganin ta kawai yayi ta faɗo kansa tana wani irin kuka, hankalin ta ba ya jikin ta, kawai faɗi take yi, “ya tamaike ta za su cinye ta, ga sunan sun biyo ta”.

Nan hankalin Rayyan yayi mugun tashi, ya riƙo ta da take ƙoƙarin shigewa jikin sa, magana ya so ma mata yana faɗin, “tayi shiru babu abinda ya biyo ta”. Amma ina ko jin sa ba ta yi, duk ta gama rikicewa jikin ta sai faman rawa yake yi

Hakan da ya gani sai ya saka ta a jikin sa ya rungume ta, ya soma tofa mata addu’a, don tunanin sa ya bashi mafarki tayi ta tsorata ainun

Ya daɗe yana mata addu’a bata dena kuka da iface-ifacen ba, daƙyar ya samu nutsuwar ta ta soma dawowa jikin ta

Duk da ta gane a inda take yanzu, but ta gaza motsawa bare ta fito daga jikin sa, illa sake shige masa da take yi tana ma tsar hawaye, har yanzu tsoron be bar ta ba

Numfashi Rayyan yaja kafin ya soma ƙoƙarin raba ta da jikin sa yana faɗin, “RAUDHA tashi ki je ɗaki kinji? Babu abinda zai same ki mafarki kika yi”.

Memakon haka sai ma fashe masa da kuka da tayi, tana sake shigewa jikin sa akan baza ta je ba

Shiru kawai yayi yana tunanin wannan sangarta irin na yarinyan nan, ga dai ta da shekaru, amma kuma babu hankali, har yanzu jin ta take yi tamkar yarinya, yaran ma sun fi ta sanin abinda ya kamata, shi fa gaskiya bazai iya barin ta ajikin sa ba, haka kawai taja masa matsala

Hannu ya saka ya finciko ta ajikin sa yana miƙe wa tsaye

Ai itama zumbur ta miƙe ta nufe sa tana sakin kuka me ban tausayi, don sosai ta tsora ta da abinda tagani a mafarki yau, gani take yi duk idan ta jirga zata sake ganin mugayen halittun nan ne, ji take yi tamkar macijin nan na biye da ita, idan ta motsa zai cinye ta 

Ganin zata sake tabaibaye sa, sai yayi saurin matsawa yana cewa, “RAUDHA ki nutsu mana, ba kya ganin Ni ba muharramin ki bane? Yayan ki kaɗai kike da damar mishi haka amma ban da Ni”.

Kuka ta sake fashe mishi dashi tana sake bin shi, ta shige jikin sa, don ko kaɗan bata ma fahimci me yake nufi ba

Guntun tsaki ya ja yana bin ta da kallo, duk da yana tsananin jin tausayin ta amma ba zai yarda da wannan naniƙen ba, iska ya fesar daga bakin sa kafin ya kalle ta yace, “mu je na raka ki ɗakin ki to”.

Maƙe kafaɗa tayi ita baza ta je ba

“To yanzu ya kike so in Yi dake? Kin san dai bazan zauna ki naniƙe Ni ba ko?”

Idanu ta zuba mishi, sai shima ya tsaya yana kallon ta, sosai ya shagaltu da kallon ta, yayinda itama ta kasa ɗauke idanun ta a kansa

Tsawon mintuna kafin ita ta lumshe idanuwan ta, tana sake ƙanƙame sa a jikin sa

Ɓoyayyen numfashi ya sauke kafin yace, “to je ki kwanta a nawa gadon ko?”

Buɗe idanu tayi ta sake ɗaura su a kansa, sai kuma ta maƙe kafaɗa

“To ya kike so in Yi dake, ahaka kike so mu kwana?”

Shiru tayi masa tana sake gyara ƙafafuwan ta sabida gajiyan tsayuwa

Tafiya ya soma yi zuwa bakin gadon, ya janye ta daga jikin sa ya zaunar da ita, sannan ya juya da zummar rufe ƙofa da tabar sa a hangame, sai jin ta yayi ta sake ƙanƙame sa ta baya ta fasa mishi kuka, jikin ta na matuƙar rawa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button