RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

Sosai a wannan karon take kuka sabida kalaman Daddyn sosai ya shige ta, ta faɗa jikin sa cikin kukan take cewa, “Daddy ku yi haƙuri don Allah”. Abinda take faɗa kenan tana ci gaba da kukan

Hannu Suhaib yasa ya ɗago kanta yana cewa, “haƙurin na meye ne Baby? Allah idan baki dena kukan nan ba zan yi fushi dake, kuma kin san abinda ban taɓa yi ba kenan”.

Hannu ta saka da sauri ta soma share hawayen ta, Daddy na taya ta

Ray dai na zaune yana kallon su, zuciyar sa cike fam da soyayyar ta, tabbas da zai iya haƙura da RAUDHA, da tuni ya bar ta har ABADA

Daddy ya soma tashi ya fice bayan ya ce musu “zai je wajen doctor ne”.

Shima sai Suhaib ya miƙe ya ɗauki waya ya fice batare da ya ce uffan ba, don ya gane manufar Daddy ɗin, shiyasa shima ya miƙe ya ba su wuri

RAUDHA da kallo tabi Suhaib dashi har ya fice, don bata yi tunanin wai fita zai yi ba, sai dai ganin ya fice kawai sai ta bi shi da ido ta kasa cewa komi..

Sunan ta da Ray ya Kira ne, yasa ta dawo da kallon ta gare shi, sai a lokacin ma ta kalli inda yake, shiyasa tayi saurin ɗauke kai da suka haɗa ido, sosai ta ga ya sauya mata saboda raman da yayi. Bata amsa mishi ba illa ɗaure fuska da tayi tana cin magani

Sarai ya lura da sauyawan ta amma hakan be dame sa ba, sai ya tashi daga kujeran da yake ya dawo na kusa da gadon, yana kallon ta yace, “Ya jikin naki Pretty?”

Shiru tayi masa tana sake jujjuya kanta don ko kaɗan ba ta ƙaunar kallon da yake mata, har cikin jikin ta take ji

Shiru ne ya ratsa na ɗan wani lokaci, kafin kuma ya sake buɗe baki yace, “Pretty idan har ban manta ba, ke ce da kanki kika yi min alƙawarin zaki kasance dani a duk halin da kika ganni, don me baza ki yafe min ba? Wlh duk abinda nayi miki a baya, nayi sa ne saboda ƙaunar da nake Miki, ki yarda dani, ina son ki sosai shiyasa ba na son wani abu ya same ki, duk abinda nayi miki a baya nayi hakan ne don ki kintsu ki dawo kan hanya madaidaiciya, amma duk idan na musguna miki, ina koma wa ne abun ya dame Ni matuƙa a rai, sai kuma naga babu hanyar da ya dace illa hanyan da nabi ɗin, duk kalaman da nake faɗa miki, na rantse da Allah, ba ke kaɗai suke ɓata wa rai ba, ina kwana ne da ƙuncin zuciya a duk sanda nayi miki irin furucin nan, sam ina ji ba na kyauta wa, sosai nake azabtuwa, amma kuma Ni duk a gani na hakan shi ne dai-dai, hanyar kawai da zan bi don ganin kin gane gaskiya, Pretty duk da nasan halin ki, na san ke wacece amma wlh ban hana zuciya ta ƙaunar ki ba, ina son ki da gaskiya Pretty! wlh ko da Zaki koma rayuwan ki na baya ne, zan kasance dake Pretty, sabida ƙaunar da nake Miki bazai bari na iya rayuwa cikin daɗin rai ba, ban taɓa son wata ba sai ke, a kanki zuciya ta ta fara soyayya”.

Shiru yayi yana jan numfashi, sai kuma ya ci gaba da faɗin, “RAUDHA ina son ki, a gaban kowa zan fito in sanar cewa ina son ki, kuma ina me alfahri da hakan, ina roƙon ki ki bar komi ya wuce, ki amshe Ni a matsayin masoyin ki a yanzu, zan miki duk abinda kike so in dai zaki yafe min ki amshi tayi na, idan kuma kin ce ba kya so na, wlh zan bar rayuwan ki har ABADA kamar yanda kike so”.

Tunda ya soma maganar nasa, ta haɗa kai da gwiwa a saman gadon tana faman rera kuka a hankali, sosai zuciyar ta ta karye da maganganun sa, “shin meyasa baza ta yafe masa ba?” Shi ne tambayar da zuciyar ta ke ta faman tambayan ta, tabbas tana ƙaunar sa itama, amma kuma bata san meyasa ba, sosai yake ba ta haushi, duk da kaso mafi yawa yanzu maganar sa yasa ta fahimci gaskiya, tabbas so ne, idan ba son ta yake Yi ba, da be mata abinda yayi mata ba, kuma da shi macuci ne a gare ta, tabbas tasan da tuni ya daɗe da cutan ta, saboda ya samu hanyoyi da dama amma be yi hakan ba..

Tashin da yayi ya saka ta dawo duniyar tunanin ta, ahankali ta ɗago kai tabi shi da kallo, har ya kai bakin ƙofa ta tsayar da shi da faɗin, “dakata Malam”.

Cak Ray ya tsaya daga buɗe ƙofan da yake shirin yi, sai dai be jiyo ba yana jiran abinda zata ce

Sauko wa tayi daga kan gadon, ta saka hannu ta share hawayen fuskarta, duk da kuwa ba dena zubo wa suka yi ba, ta taka ta nufi wajen sa, tana ƙarisawa ta saka hannu tayi…

???? _wlh ina shan dariya da team-Ray, wai dama kun san zuciyar sa tana da rauni kuka turo sa wajen RAUDHA? Kun san halin ta ai._

[4/14, 11:22 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

*RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR:* ✍️

_Nafisat Ismail Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*FEENAH WRITER’S ASSO*????

”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*????

*F.W.A????/*

*RAMADHAN MUBARAKH*????????????

2021.

             *HADHISI*

_An karɓo daga Baban Salma Allah ya ƙara musu yarda ya ce, “na tambayi A’ishah matar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, nawa ne sadakin Manzon Allah?” Sai tace, “sadakin Manzon Allah ga matan sa uƙiya goma sha ɗaya da rabi (nashsha). Sai ta sake cewa “shin kasan Nashshu?” Sai yace mata, “a’a”  Sai tace, “rabin uƙiya shi ne darhami ɗari biyar”. Muslim ya ruwaito. Ingantaccen hadisi daga Muslim._

.

*NOT EDITED* ___________________________????

*SEASON FIFTY THREE*

_______???? Hannun ta ta saka ta kamo nashi, hakan yasa ya juyo yana kallon ta, ido cikin ido suke wa junan su kallo, batare da ko wannen su yana ƙyafta wa ba

Sun ɗau tsawon soconni a haka kafin ita ta soma ɗauke kanta tana jan numfashi, sai tace, “I love you”.

Tsaban maganar ta zo masa a bazata be san sanda ya fiddo idanuwan sa waje ba yana kallon ta da tsananin farin cikin da ya fito tun daga zuciyar sa, sai dai ya kasa magana illa kallon ta da yake yi

Jin yayi shiru sai ta mayar da idanun ta kansa, ganin kallon da yake mata sai ta taɓe baki tace, “Ina son ka ba yana nufin na amince zan aure ka bane”. Tana gama faɗar haka ta saki hannun sa ta juya zata koma

Yayi saurin riƙe mata hannun, dole taja ta tsaya, but ta kasa juyo wa illa lumshe idanuwan ta da tayi tana sauraren bugun zuciyar ta

Tako wa yayi ya dawo gaban ta, idanun sa a kan ta da tsananin murna yace, “idan har kina so na, na tabbata zaki iya aure na, kenan kina nufin kin amince dani a matsayin masoyin ki?”

Huro hanci tayi sai dai ta kasa kallon sa, illa shiru da tayi tana haɗiyar yawu

Shi kansa ya lura akwai Magana a bakin ta, sabida yanda take ta motsa bakin tamkar zata buɗe tayi magana. Murmushi yayi yace, “I love You so Much RAUDHA! Ina son ki da yawa wanda baki ma bazai iya furta wa ba, kiyi haƙuri da duk abinda nayi miki kinji?”

Sai a lokacin ta ɗago manyan idanuwan ta ta sake kallon sa, sai tayi saurin ɗauke kai tare da janye hannun ta, ta gifta shi tana faɗin, “Ni fa ba ina nufin zan iya auren ka bane, duk da na faɗa maka wannan kalman, zuciya ta ce ta aiko Ni, but a zahiri baka yi min ba”.

Sosai maganar nata ta ba shi dariya memakon haushi, sai da ya murmusa yana shirin magana, sai ji suka yi an buɗo ƙofan, daga shi har ita juya wa suka yi su ga wanene

Suhaib ne tsaye yana bin su da kallon tuhuma, ganin su cirko-cirko da yayi a tsaye kusa da juna, sai kawai ya saki fara’a a fuskar sa yana faɗin, “Baby kin..”

Saurin katse sa tayi da faɗin, “Yaya Ni dama Toilet zan je shi ne na sauko”. Sai ta juya kuma tayi Toilet ɗin da sauri har tana kanannaɗe skert ɗin ta tun kafin ta isa don ya tabbatar Toilet ɗin take son zuwa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button