RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

              ????????????

     Biki na ta ƙara to wa, inda ake ta shirye-shiryen bikin daga bangare biyun gaba ɗaya, su kuma masoyan suna ta shan soyayyar su.

.

_jama’a saƙo daga RAUDHA, tana miƙa saƙon gaisuwa tare da katin gayyata wajen masoyan ta, ta ce a gaishe ku matuƙa, bata cire kowa ba, kowa tana gayyatar sa taya ta murnan nasaran ƙwamushe Ray ya zama nata, daga *UMMU DAHIRAH FAN’S GROUP, NAFEESA GROUP NOVEL’S, da kuma *RAUDHA FANS* ???? duk tana gaishe ku, kuma tana gayyatar ku baki ɗaya, har da ma maƙiyan ta masu mata hassadan samun Captain Rayyan._ ????????????

[4/14, 11:23 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

*RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR:* ✍️

_Nafisat Ismail Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*FEENAH WRITER’S ASSO*????

”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*????

*F.W.A????/*

*RAMADHAN MUBARAKH*????????????

2021.

.

*NOT EDITED* ___________________________????

*SEASON FIFTY FOUR*

_______????Dama akace duk abinda aka saka mishi rana dole zai zo, to ga shi bikin su RAUDHA ya rage saura kwanaki ne, sosai Daddy ya ga jama’a a bikin nan, waɗanda suka zo masa daga cikin ƴan uwa, bare shi mutum ne na ƙwarai me kirki da hannun kyauta, shiyasa dangi duk suka taho masa, sabida sun san ba su za su ragu ba, sai dai ma su ƙaru, wasu tun ana kwana huɗu, uku duk suka zo da kayan kwanan su, sai bayan biki su koma, su suke yin komai tare da ƴan aikin gidan, Masha Allah gida ya cika maƙil

Itama Farida tun ana saura sati ɗaya suka zo, daga ita har Suhaib da ya ajiye aikin sa kacokan, don zuwa bikin shalele kuma mafi soyuwa a birnin zuciyar sa

Zuwa lokacin duk shi yake kai ta duk inda take buƙata, duk da dama duk wani gyara da ake mata, har gida ake zuwa ayi mata, Farida ita ta ɗau nauyin komi ake gyara ta ba ni da gyara ba, domin tun sanda aka soma mata gyaran amarcin RAUDHA ta sauya, gaba ɗaya baza ka taɓa kallon ta kace ita ce ba, ta koma hurun aini????????, kamar ka latsa ta jini ya zuba sabida haske da sulɓi da take yi, ga wani ɗaukan idanu da take yi, dayake hasken ta yayi yawa har wani jajja take yi kamar dai zabiya, amma kuma ko ƙuraje bata dashi. Hasken ta me kyau ne, me fizgar mutane zuwa gare ta.

    Bata da ƙawaye ita take yin komi nata, sai ana jibi biki ne Ramcy ta iso, a ranan kuma ƙawayen Ramcy ɗin duk suka zo, dayake sun ce idan bikin ta ya zo a gayyace su duk za su zo, to shi ne fa RAUDHA ta samu ƙawaye da ɗan yawa, ga shi wasu ma da suke chart a cikin Friends ɗin sun ce za su zo mata.

Ranan juma’a 8 ga watan April, dubu biyu da ashirin da ɗaya 2021. Dubban jama’a suka shaida ɗaurin auren *CAPTAIN RAYYAN HASSAN* da Amaryan  sa *RAUDHA MUSTAPHA MAKAMASHI*

Da dare akayi shirin Dinner, inda me kwalliya ta tsantsara wa RAUDHA kwalliyan da ya ɗauki fuskar ta ainun, ya ƙara fito da tsantsan kyawun ta, ba wani karikitai aka cika mata ba, saboda tace ba ta so, shiyasa akayi mata light make-up, aka shirya ta cikin ash colour ɗin gown doguwar riga, rigan fitet ne, domin dai-dai jikin ta ne, amma daga ƙasan gwiwan ta ya buɗe sosai har yana jan ƙasa, me siraran hannu ne, sai wani ƙaton flower da aka saka mata daga hannun damar ta, da net akayi shi, sai kwalliya a gaban rigan da kalan jan zare, sai akayi mata amfani da jan net aka rufe mata gashin ta da ya sha gyara har kafaɗun ta, duk da an tufke mata shi a tsakiyar kanta, takalmin ƙafan ta me tsananin tsini ne sosai, kalan ja tare da pourse ɗin hannun ta

Sosai ta tafi da imanin duk wanda yayi tozali da ita sanda me make-up ta fito da ita, sai haska ta suke yi a photo ana sauri ayi status da ita????. Kuma na san duk aikin WhatsApp fan’s ɗin ta ne.????????

    A lokacin motoci duk sun zo ɗaukar mutane zuwa Shagalin ku restaurant, inda a nan ne za’a yi dinner ɗin. Sai da kowa suka shiga mota suka tafi kafin Farida tare da Ramcy suka rako ta zuwa motan da za su tafi tare da Ray, galleliyar mota ce fara tasha kwalliyan balo-balo

Su suka buɗe mata motan ta shiga ciki ta zauna, sannan suka rufe suka nufi motan Suhaib da zai kai su

Numfashi kawai taja lokacin da ta shaƙa daddaɗan ƙamshin su da ya haɗe ya gauraye waje ɗaya ya ƙara wani sinadarin daɗi, juyowar da zata yi suka haɗa ido dashi dake zaune ƙyam ya kafe ta da ido ko motsin kirki ya gaza yi, saboda ba ƙaramin zauta shi tayi ba, ta ɗauke masa gaba ɗaya nutsuwar sa da numfashin sa, ya tafi wani duniyar da ya kasa tantance a raye yake ko kuwa a mace ????????, hege Ray! Zaka dawo ma duniyar mu ne yanzu. ????, Bari dai ta falla maka mari????

Murmushi tayi ta matso da fuskar ta kusa da nasa, ta hura masa iska

Hakan yasa ya dawo cikin hayyacin sa, har da ajiyan zuciya

Ita kuma sai ta taɓe baki tana matsar da fuskar ta kusa da nashi, tare da gyara zaman ta

“Kin yi kyau Baby na”. Yayi maganar tamkar ana masa dole, nan kuwa tsaban shiga tention ne ???? ya rasa kuzarin sa

Sake kallon sa tayi, suka ƙura wa junan su idanu, sai kuma ta sakar masa murmushi ahankali tace, “kaima kayi kyau Ƙalby, I Love You so Much”.

Lumshe idanuwan sa yayi yana buɗe wa a kanta cike da wani irin farin ciki dake gudana a zuciyar sa, sabida kasancewar yau ɗin na musamman ne a rayuwan sa, Mallakar Abokiyar rayuwar sa. Hannun sa ya saka ya kamo nata wanda suka sha lalle suka yi mata matuƙar kyau, hannun kawai yake kallo

While itama tana taya sa

“Yayi kyau”. Ya sake faɗa ahankali

Murmushi kawai tayi ta kawar da kanta, sai kuma ta lumshe idanuwan ta saboda jin ya haɗe hannayen su waje ɗaya yana faman matsa mata

“Baby kin Yi kyau”.

“I know”. Tafaɗa tana ci gaba da murmusawan ta

“Ina kishin ki”. Ya sake faɗa yana kisses ɗin hannun nata da ya ɗago zuwa bakin sa

Shiru tayi masa wannan karon, tana me sake runtse idanun ta, sosai take jin wani iri a tattare da abinda yake mata, amma kuma baza ta iya hana sa ba, inda so samu ne ma, taji ta a jikin sa, sabida ba ƙaramin son kasancewar hakan take yi ba, duk a sabida ƙamshin turaren sa da ya cika mata hanci, tamkar ta shige jikin sa tayi ta shaƙa..

“Tunanin me kike yi?” Yayi maganar yana shafa fuskar ta

Buɗe idon tayi a kansa, sai kawai suka sake ƙure junan su da kallo, ko wanne na jin son ɗan uwan sa a zuciya..

Tsayuwar motan shi ya dawo dasu hayyacin su, dole suka nutsu suna me mayar da hankalin su kan Suhaib da ya buɗe murfin ƙofan side ɗin Ray, yace masa “ya fito”

Sai da ya sake yi wa hannun nata kiss, kafin ya sakar mata, sannan ya fito, kafin ya zagayo ta side ɗin ta, itama har an fito da ita

A tare suka jera zuwa hole ɗin, masu sauraro bazan iya fasalta muku yanda couple ɗin nan suka haɗu ba, da kuma Shagalin da akayi, amma kuyi tunanin abinda zai faru, ???? kun san halin RAUDHA dai, a bikin nata ma bata ji kunyan yin rawa ba, koda aka ce su fito fili, ita zaƙe wa tayi ta tiƙa rawan ta ba ko kunya, har da riƙe masa hannu, shima da ya ga dai abun ba na yi bane, dole ya ajiye kunya suka bar tarihi a wajen

Yawancin abokan sa na wajen aiki duk sun hallara, har wasan su na soji sai da akayi, a hotel ɗin aka kai su suka sauya kaya zuwa kayan sojoji daga shi har ita, sun yi matuƙar kyau sosai, sai wanda ya gani _(???? nasan ku ma kun gani ai? Tunda babu wacce bata zo Dinnern nan ba, kuma duk na ga inda kuka ɓoye kuna afa shinkafa da nama????????)_ ita rigan da ta saka t.shirt ne blue Black, sai wandon sojoji da ƙaton Combat ɗin su, sannan ta ɗaura hulan kayan a saman kanta, shi kuma yayi shigan kayan nasu ne gaba ɗaya, sun yi mugun kyau gaskiya babu ƙarya, ko kaɗan RAUDHA bata nuna tsoro a wajen wasan nasu ba, duk abinda aka saka ta tana yi, duk da sosai take tsoron bindiga bare Harbin shi, amma wayewan ta ya saka ta ɓoye haka, sannan tana jin cewa ita Matar Soja ne a yanzu, _(????zata yi muku gori ne walle, ku auri soja akwai daɗi auren su ????)_ don haka tsoro be kamace ta ba

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button