RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

“Za ku iya shiga ku duba ta, in yaso daga baya sai muyi magana”. Cewar likitan yana murmushi

“Ok thanks doctor”.

     Ɗakin suka nufa, Daddy ne a gaba Ray na biye dashi a baya, har bakin gadon suka ƙarisa, inda Ray ya tsaya daga jikin gadon, Daddy kuma ya zauna akan farar kujeran Robber dake jikin gadon, ya riƙe hannun RAUDHA da idanun ta ke rufe ya kira sunan ta, “Daughter kina jina? Ya ya jikin naki?”

Shiru RAUDHA tayi duk da kuwa tana jin shi ɗin

Cike da damuwa Daddy ya sake cewa, “wai me ya faru ne lokaci ɗaya kika sume Baby? Me ke damun ki Baby na kiyi magana kinji? Meyasaka ki ruɗu?” Sai kuma ya sauya akalan tambayan ga Rayyan da cewa, “kai ne kake gidan, shin kasan abinda ya faru ne? Ni dai nasan na bar ta lafiya but sai na dawo na tarar da wannan tashin hankalin”.

Sake runtse idanu RAUDHA tayi jin saukar muryan Ray a kunnen ta, hakan ya tabbatar mata da cewa ba mafarki ne take yi ba, gaske ne Ray shi ne Ƙalbyn ta, shi ne wanda ya zo gidan su a matsayin Ƙalbyn ta, sai kawai ta fashe da wani irin kuka me ban tausayi

Sosai Daddy ya sake shiga tashin hankali, nan da nan ya ruɗe yana tambayan ta abinda ke faruwa

Shi kuwa Ray runtse idanun sa yayi yana jin babu daɗi a ransa, shi kaɗai yasan me yake ji a ransa, tashin hankalin da yake ciki baki ma bazai iya fasaltuwa ba, dauriya kawai yake yi da abinda yake shirin faruwa dashi

Daƙyar Daddy ya iya rarrashin ta, duk da ba shiru tayi ba, amma yanzu ta buɗe idanun ta, ko kallon inda Ray yake bata yi ba, tace wa Daddy “ita a sallame su, ba ta son zaman Hospital” 

Yanda tace ɗin haka Daddy ya aiwatar, ya saka Ray Kiran Doctor ɗin ya basu sallama.

    Ana sallaman su suka fito, Ray shi yaja motan su kuma suna baya, RAUDHA ta kwanta a jikin Daddy sai ƙananun kuka take yi, duk rarrashin da Daddy yayi mata taƙi haƙura, sosai ranta yake tsananin suya, baƙin ciki da ƙunci duk ya cika mata zuciya, har yanzu a ranta tana jin kamar mafarki ne take yi, idan ta farka zata tashi taga babu Ray a tare da ita, but da ta ɗaga idanu take sauke su a kanshi, sai ta sake jin wani baƙin ciki ya kanainaye ta, hakan ke sawa lokaci ɗaya sai ta sake fashe wa da wani sabon kukan

Sosai wannan abun da take yi ya so ba wa Ray dariya, duk da yana cikin damuwar me zai faru a soyayyar sa, but hakan be hana sa murmusa wa ba.

       Suna isa gida, ta buɗe murfin motan tariga kowa yin gaba, Daddy na kiran ta but sam taƙi tsaya wa

Koda suka shiga parlour’n babu ita, hakan yasa suka zauna inda Daddy Ke tambayar Rayyan “zuwan nasa na bazata”

But shi dai Ray murmushi kawai yayi, don be san me zai ce mishi ba

Ɗaya daga cikin ƴar aikin su, da ta kawo musu Drinks ne, Daddy ya tambaye ta da cewa, “ko da suka fita baƙon RAUDHA ya zo ne?” Tunda a tunanin sa dai be rigada ya ƙariso ba, Maybe fitan su ya zo, su kuma ba sa nan

Cikin girmamawa take sanar masa da “Ray ne baƙon nata, kuma sun sauke sa tun ɗazu”

Da mamaki Daddy ya kalli Ray yace, “Captain maganar ta gaskiya ne?”

Cike da kunya Ray ya duƙar da kansa tare da amsa mishi

Farin ciki ne ya mamaye Daddy yace, “You mean Kai ne Ƙalbyn Baby, but taƙi sanar mana? Kaima haka? A cikin ku babu wanda ya sanar mana kuke ta ɓoyan soyayyar taku? Kai abu yayi kyau Masha Allah. To Ina muku fatan alkhairi, Allah ya tabbatar mana da mafi alkhairin sa”.

“Ameen Daddy”. Ray ya amsa cike da farin ciki shima a zuciyar sa, sabida ganin Daddy kansa yayi farin ciki da zamowan sa Saurayin Ɗiyar sa

“Amma to ta tafi ta bar ka anan? Ai sai ta zo taji da kai ko? Ko dayake gidan ba baƙon ka bane”. Daddy yafaɗa yana dariya

Shima Ray dariyan yayi, but ya kasa cewa komi

“Tashi mu je saman, sai in Kira ta”.

Tashi Ray yayi, suka haura sama, a parlour’n da ta shirya don tarban shi suka shiga, Daddy ya saka me aiki ta zuba masa abinci, sannan ya saka ɗaya daga ciki ta je ta kira RAUDHA. Har ta tafi kuma, sai ya ce “ta bar shi” shi ya tashi ya je kiran ta

Ray dai na zaune ya tasa abinci gaba, sai dai ko cokali ɗaya ya kasa kai wa bakin sa, hankalin sa kacokan yana ga RAUDHA.

                   ????????????

Da farin ciki a fuskar sa Daddy ya ƙarisa ɗakin RAUDHA, but sai dai a yanda ya ganta ne hankalin sa yayi ƙololuwar tashi

Tana zaune a ƙasa, ta ɗaura kanta saman kujera tana ta riskan kuka, har da majinu

Da sauri ya ƙarisa wajen ta cikin tsananin tashin hankali yake tambayar ta abinda ke faruwa, duk ya ruɗe yana ta faman taɓa jikin ta yaji ko wani abun ne ke damun ta

Cikin kuka ta ɗago kanta tana kallon sa da jajayen idanuwan ta, tace, “Daddy RAYYAN ya zo gidan nan ne yau?”

Cike da mamakin tambayar ta yace da ita, “Ya zo mana Baby, ba ke kika gayyace sa ba? Kuma ya zo, yana nan a Parlour. Lafiya me ke faruwa ne?”

Kuka ta fashe da shi, idanun ta akan Daddyn tace, “Daddy kenan yana nufin shi ne Muhammad ɗina, shi ne wanda nake soyayya da shi?”

Sai kawai Daddy ya saki baki yana kallon ta, sai kuma yace, “baki san haka bane Daughter kike tambaya na? Ina ce ke kika gayyace shi ai?”.

Girgiza kanta tayi, kafin tace, “no Daddy ba Ni ba CE, Sam ba shi ne wanda nake so ba, ya yaudare Ni ne, Ni ba shi nake so ba, wlh bazai taɓa zama Ƙalby na ba”.

Sai kuma ta saka hannu ta riƙe masa nasa

“Daddy please ka farkar da Ni wannan mummunan mafarkin da nake yi, mutumin da na tsana shi ne zai zame min Mijin da na ke fatan aure? No impossible”.

Daddy fa duk ya kasa gane abinda take nufi, dole ya saka hannu ya ɗago ta, yana jinginar da ita jikin sa ya hau rarrashin ta

“No Daddy bazan dena kuka ba, har sai na tabbatar da cewa ƙarya ne zancen nan, Daddy zuciya ta zafi take min”. Ta ƙare maganar da saka hannun ta tana dafe ƙirjin ta, yayinda idanuwan ta suke kwararar da hawaye sosai

Sosai Daddy ya ruɗe, ya rasa yanda zai yi da ita, dole ya miƙe ya fita ɗakin, sai ga shi ya dawo tare da Rayyan, cikin tsantsan damuwa yake kallon Rayyan ɗin yake tambayar sa da faɗin, “Captain wani abun ne ya faru da kai da ita, na kasa fahimtar me take cewa, ka faɗa min tsakanin ku?”.

Cike da sanyin murya Ray ya soma sanar masa da komi, idanun sa kan RAUDHA da ta kifa kai take ta rusa kuka, tamkar ana yankan naman jikin ta, duk da muryan ta ba ya fita amma sosai ta dage take kukan

Shi kansa Daddy sai da jikin sa yayi sanyi da abinda Ray ya sanar masa, sosai ya tausaya wa Ray ɗin, to abun tausayi mana, tunda ga shi yana soyayya but ashe ita wacce yake yi dan ita, ta kasa amsar shi a zahiri, sam ba shi ne take so ba

Zama Daddy yayi ya soma rarrashin ta, amma taƙi shiru

Ray dai tsaye yayi yana kallon su

“Baby tunda kin ce ba kya son shi meye to ya rage? Kiyi shiru mana kar ki saka wa kan ki ciwon kai”. Daddy ya sake faɗan haka yana saka hannu ya soma share mata hawayen

Cikin dishewar muryan ta da ya ƙara shige wa, don daƙyar ma yake fita, har katse wa maganar nata yake yi tace, “I Hate him so much Daddy, na tsane shi sosai fiye da kowa Daddy, ko da zan zauna babu aure ne Daddy bazan taɓa auren sa ba, ba na son sa Daddy”. Ta ƙare maganar tana dage wa tare da fashe wa da kuka

Daga Ray har Daddy babu wanda yaji daɗin kalaman ta, musamman ma Ray da har hawaye sai da suka zubo masa, ahankali ya tako zuwa wajen kujeran da suke, ya zuƙuna gaban ta, cikin hawaye yace, “Please RAUDHA ki taɓa zuciya ta ki ji yanda take harba wa da ƙaunar ki, duk socond ɗaya kullum ƙaunar ki sake wanzuwa take yi a raina, na jima ina dakon soyayyar ki a raina, na jima RAUDHA, don Allah gani a gaban ki, ki amince da soyayya ta RAUDHA, ina matuƙar ƙaunar ki, kuma ba na tunanin akwai wanda zai so ki fiye da yanda nake son ki, Ina matuƙar matuƙar ƙaunar ki RAUDHA, ke ce kika yi min alƙawarin baza ki taɓa bari na ba,”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button