RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

Daga shi har Ray da kallo suka bi ta, ko wanne na sakin murmushin da be shirya ba, sai kuma suka jiyo da kallon su ga juna suna ci gaba da murmushin

Suhaib yace, “Allah ya shirye ki Baby, har yanzu kin ƙi ki girma, Aboki na zaka yi aiki duk sanda ka auri Baby a matsayin mata, shawaran da zan baka kawai idan har ta kasance matar ka, to ka haɗa su biyu ka aura ka je dasu gidan a lokaci ɗaya, idan kuma ba haka ba, wlh zaka sha…”

Burum RAUDHA ta fito daga Toilet ɗin, fuskar ta gaba ɗaya a haɗe yake tace, “Yaya To dama wa yace maka zan aure sa? Wlh bazan taɓa zama da kishiya ba, be isa ya haɗa Ni da wata ba, idan ma yasan yana da mata yanzu tun wuri yaje ya sake ta..”

Wani irin dariya ne ya kufce musu su duka biyun

Dole yasa RAUDHA tayi shiru tana faman zare idanu, sai yanzu ta gane katoɓaran da tayi, sai tayi saurin kwaɓe fuska kamar zata yi musu kuka tace, “Ni fa ba ina nufin wani abu bane, misali nake yi idan zan kasance matar sa”.

Suhaib na dariya yace, “to Baby dama wa yace miki muna nufin wani abu? Dariyan ne ya zo mana atare sabida tuna wani abu da muka yi, ko ba haka ba Dude?” Ya ƙare maganar da ɗage wa Ray gira ɗaya

Ray dai tsaban farin cikin da yake ji a ransa, sabida ganin cewa RAUDHA har yanzu tana ƙaunar sa, be iya magana ba illa gyaɗa masa kai da yayi yana ci gaba da darawa

Haɗa idanu suka yi dashi, sai ta banka mishi harara tana yin gaba, ta hau kan gadon tana koma wa ta kwanta, har da juya musu baya

Matso wa Suhaib yayi kusa da shi, ya zungure shi ganin yana ta kallon ta, murmushi yayi masa ya raɗa masa magana a kunne, sannan ya kalli RAUDHAN yace, “Baby bari mu je mu dawo, idan Daddy ya dawo ki ce masa mun shiga cikin anguwa zamu je wajen wani friend ɗina”.

Shiru RAUDHA tayi bata ce komi ba har suka fice, suna fita ta tashi zaune tana tanƙwashe ƙafafun ta, tare da haɗa hannayen ta waje ɗaya ta tallabo haɓar ta, tsira wa waje ɗaya ido tayi tana me afka wa tunani.

????????????????????????????????????????

       Washe gari dole RAUDHA ta matsa aka sallame ta, su ma su Daddy sun ji daɗi ganin yanda ta samu lafiya, shiyasa Daddy shima yace “a sallame su” tunda dama damuwar duk akan Rayyan ne, kuma sun ga ta sauko sosai akan sa.

    Suna komawa gida, Daddy ya Kira Uncle ya sanar da shi abinda ke faruwa, kar ku so ku ga murnan da ya nuna da shi da Ammee, kai gaba ɗaya ma ahalin, har Faruk da yake ƙaunar ta, tunda tuni ya ajiye makaman sa tun sanda ya gane cewa Yayan nasa yana ƙaunar ta, sosai kowa yake farin ciki da wannan haɗi.

     Ita kuwa RAUDHA ko kusa nuna wa take yi har yanzu baza ta iya auren sa ba, kuma sun ci gaba da soyayyar su a waya, domin yana kiran ta tana ɗauka, sai dai ta dinga gaya masa maganganu kenan don dai ta ɓata masa rai, amma kuma be hana gobe idan ya kira ta taƙi amsa wa ba

Shi dai Ray dariya ma abun nata yake ba shi, tamkar dai har yanzu akwai aljanu a kanta, domin wani abun idan tayi, baza ka ɗauka ƴar shekara 24 bane, RAUDHA akwai shirme a kanta sosai.

     Da weekend sai ga shi yayi mata bazata ya zo gidan, sosai a ranta tayi murna amma a fili ta nuna ko kaɗan hakan be burge ta ba, illa taɓe baki da take ta faman yi taƙi masa magana

Daddy na tashi a wajen yace da ita, “wai Pretty ko baki yi murna da gani na bane? Har yanzu kin ƙi ki yafe min gaba ɗaya ko?”

Kallon sa tayi, sai ta ɗaure fuska tace, “ai bazan taɓa yafe maka ba Ƙalby”.

“Why?” Yace da ita cikin sanyin murya

“Sabida nima har yanzu kallon ƴar iska kake min, in har baka dena ba, Nima kuma bazan taɓa amince wa da kai ba, bare har in yafe maka”.

Yace, “wlh nayi alƙwari daga yau bazan ƙara miki kallon haka ba, idan magana makamancin haka ya sake fito wa a baki na, na baki dama kiyi min duk hukuncin da ya dace dani, koda kuwa rabuwa dani ne, wlh Pretty soyayyar da nake miki ya wuce tunanin ki, ko da yanzu zaki koma rayuwan ki na Da ne, to Ni kuma nayi miki alƙawarin kasancewa da ke, bazan taɓa rabuwa dake ba, zan aure ki a haka, tabbas na yarda *SO ƘADDARAR ZUCIYA* ne! ( My new book), soyayyar ki shi ne ƙaddarar tawa zuciyar”.

Kallon sa kawai take yi, amma a zuciya murmushi take yi tana me faɗin, “uhmmm Rayyan kenan! Tabbas zan fi kowa murnan ranan da zaka yi nadama da kira na da kalman ɓatanci da kake yi, zaka sha mamaki wlh”.  A fili kuwa cewa tayi, “Fine”. Tana ɗage kafaɗa tare da karkaɗa ƙafafu

Murmushi ya sakar mata, itama ta mayar masa tana faɗin, “sai yaushe zaka tafi?”

“Kin ƙosa in tafi ne?”

Ɗan zaro ido tayi tana kama haɓa tace, “laa haza haramun”.

Dariya yayi sosai, saboda ba ƙaramin dariya ta bashi ba, itama tana taya shi, gaba ɗaya a nishaɗi suke jin su, tamkar dai an sauya musu wani abu a jikin su, ko kuma sun sauke wani nauyi

Tashi tayi don tayi masa tsiya tace, “to Ni bari in Kira maka Daddyn, tunda dama wajen shi ka zo”.

Langaɓe kan sa yayi yana sakar mata wani shu’umin kallo, cike da sanyin murya yace, “haba Pretty Kar ki yi min haka mana, kin san fa domin ki na zo”.

Murmushi tayi tana cije leɓen ƙasa, itama ɗin ta sakar masa wani kallo da ya kusa zauta shi, har da wulla idanun tamkar zata rufe su ta sake buɗe su a kansa, taku tayi ɗaya zuwa biyu a gaban sa, kafin ta juya tana tafiya cikin yanga, tamkar dai da gayya take masa

Sosai Ray ya rasa nutsuwar sa, yana bin ta da kallo ko motsin kirki ya kasa, har sai da ta ɓace wa ganin sa kafin ya saki wani Gwauron numfashi yana lumshe idanu, babu abinda yake gani sai kyakykyawar surar jikin ta dake masa gizau, “Oh Allah! My beby Zaki kashe Ni!” Yayi maganar a maƙoshi yana jingina kansa sosai jikin kujeran.

      Har Ray ya bar gidan be sake haɗuwa da RAUDHA ba, ƙiri-ƙiri ta maƙale a ɗaki taƙi fito wa, kuma ya kira ta duk taƙi ɗauka, duk da ga wayan a hannun ta tana yin Game, iyakan tayi murmushi ta katse kiran

Hakan ya tabbatar masa da tana ganin kiran nasa, murmushi yayi shima a zuciya yana faɗin, “Dani kike zancen Pretty, zan rama ne ai”.

????????????????????????????????????????

      A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, har ana shirye-shiryen saka ranan auren RAUDHA da RAYYAN, soyayyar su yanzu abun sha’awa ne, kullum suna nane a waya tamkar za su cinye juna, duk weekend kuma sai ya zo mata, ta saki jiki sosai dashi suna gurzan soyayyar su kamar za su haɗiye juna, soyayyar da suka yi a baya ma ba komai bane kan yanda suke yi

An saka ranan auren nan da wata ɗaya, sabida kowa a shirye yake kuma kuɗi ke aiki, shiyasa aka ce baza a saka da yawa ba

Tun sanda aka tsayar da ranan auren nasu, ta kira Zulain ta sanar masa

Sosai ya shiga tashin hankali da alhinin rasa ta da yayi, amma babu yanda zai iya dole sai haƙuri, duk da a lokacin ma tamkar ƙara wutar son ta ake masa a zuciya, dole ya haɗa kayan sa yace musu “zai tafi” tun da dai ya san idan ya tsaya a nan damuwa ce zai illata shi, haka yabi jirgi ya koma ƙasar su tare da ɗumbin soyayyar RAUDHA a zuciyar sa

Shi kuma ya bar Sharifa tare da nasa a zuciyar ta, sosai tayi kuka ranan da ya tafi, ta so ta sanar masa amma ta kasa, sai da ya tafi tayi dana-sani ba kaɗan ba, haka tasha kuka ta gode wa Allah, ga shi kowa ta ƙi ta sanar amsa son da take yi wa Zulain ɗin.

     _To Allah ya kyauta, inda rabon ayi dake ne to, in kuma babu shikenan, mu dai ƴan shan biki ne. ????_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button