RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

Ray ɗin da kansa ya koya mata yanda zata yi Harbin, Yana tsaye a bayan ta, ya riƙe mata hannaye suka saita mutum-mutumin da aka ajiye musu, ta har ba

Sai shewa ake yi sabida yanda komi ya ba da kala, ya burge kowa na wajen.

   A gurguje Please.. Haka dai taron ya tashi cikin ƙayatarwa. gida aka mayar da RAUDHA tunda ba yau za’a kai ta ba, sai zuwa gobe za’a wuce da ita Bayelsa, daga can kuma sai su dawo ita da Ray Kaduna wajen aikin sa, a can aka shirya mata gidan ta uban-uban su, duk da a cikin barikin sojojin ne inda yake zaune, amma kayan da aka zuba mata wayyo Allana, sai mun haɗu acan dai fans, ku waso Ido amma. ????

       Washe gari ƙarfe 09:00am jirgin su ya ɗaga zuwa Bayelsa, tare da Farida da Ramcy suka tafi, sai wasu mata biyu daga cikin dangin Daddy da yace aje dasu

Ray kuma zai taho ne zuwa anjima, don tare za su dawo da RAUDHA.

     Koda suka isa, an yi musu tarba na girma, su kansu sun san cewa sun zo dangi masu karama da waye wa, ko a fuska ka kalle su ka san haka, ko kaɗan ba su da ƙyashi ko hassada a zuciyar su, gaba ɗaya kansu a haɗe yake, bare yanda suke girmama Ammee, komi suna iya mata don ganin farin cikin ta

A family house ɗin su aka soma sauke su, inda aka ware musu ɗaki guda tare da Toilet, aka zube musu abinci da duk abinda za su buƙata, tunda suka sauka Suhaima ta zo ta maƙale wa RAUDHA, sosai tayi farin ciki da kasancewar RAUDHA cikin dangin su, har ta kasa ɓoye murnan ta, sai washe baki take yi tana nan nan da RAUDHA, duk gaba ɗaya ta maƙale mata, ba ma ita kaɗai ba, har sauran ƴan matan gidan, tunda sun kai su uku ne ƴan matan.

       Bayan sallan Asar su Farida suka soma haraman tafiya, shiyasa aka ɗauke su gaba ɗaya aka mayar da su gidan su Ray ɗin, inda Ammee da ƴan uwan ta suka yi musu tarba me kyau, suka mutunta su sosai

Ba su wani daɗe ba, Faruk ya kai su Airport, sai ga RAUDHA tana hawaye sanda za su tafi, gaba ɗaya sai taji ba ta ƙaunar tafiyar nasu, duk da sosai ta ba wa Ramcy tausayi, amma sai Ramcy ta dage tana ta mata dariya, don baza ta manta ba itama haka tayi mata, sai tsokanar ta take yi tana taɓa mata kumatu tana ci gaba da mata dariya

Sai da Farida tace, “Kin ga ƙyale ta dan Allah kar ki ɓaro mana abinda baza mu iya ba, kin san halin RAUDHA da taɓara, yanzu wlh sai ta birkice mana”.

Langaɓe kai Ramcy tayi tana sake kallon fuskar RAUDHAN da yayi caɓe-caɓe da hawaye, ta cika fam ko motsi  ba ta yi

“Allah Sarki my Besty, ki kwantar da hankalin ki yau ɗin nan za ku dawo ai, zuwa da dare zan saka Dear ya kawo Ni, kin ga sai mu sha hira”.

Kallon ta tayi, da ƙyar tace, “da  gaske kike yi?”

Gyaɗa mata kai tayi tana sake ba ta tabbaci

Da haka dai suka bar gidan RAUDHA bata sake wani maganar ba, illa kwanciya da tayi tana hawaye, sai da Ammee ta shigo ɗakin ta rarrashe ta, sannan tayi shiru, inda ta saka ta ta sake yin wanka ta kawo mata wasu tsadaddun kaya na musamman, baƙin less ne, ta saka, riga da zani ne kayan, duk gaba ɗaya daga zanin har ɗan kwalin ɗaura mata akayi, babu wanda ta iya da kanta, sosai kayan suka yi mata kyau, kasancewar ta fara shiyasa baƙin less ɗin ya yi mata matuƙar kyau, gyale aka yafa mata me ruwan Powder, daga saman kanta har zuwa gwiwowin ta ya kai mata, sannan ta saka Hill shoes, Ammee ta fito da ita zuwa parlour’n Uncle, inda yake zaune daga shi har ƴan uwan sa

Sosai suka yaba da tarbiyyan ta, suka saka mata albarka ko wanne fuskar sa cike da farin ciki, haƙiƙa sosai ta shiga zuciyar su, ko dan kyawun ta dole ne ka so ta.

      Wajen magriba Ray ya shigo gidan, har zuwa bayan isha’i ba su haɗu da RAUDHA ba, tunda ita tana ɗaki a kwance, sai da Suhaima ce ta zo shi ne ta tashi suke taɓa hira, a tare suka yi sallan isha’i a ɗakin, inda Ammee ta shigo tace “mata ta kintsa za su tafi da Mijin ta” ta sha mamaki sosai, sabida ganin dare yayi, ai ya kamata ace sai da safe za su tafi, amma kuma bata ce komi ba, ta saka Shadda maroon Colour da aka sake kawo mata, sai dai ɗinkin doguwar riga ne da ya ji aiki sosai daga saman ƙirjin ta kawai, Suhaima tayi mata light make-up sannan ta ɗaura mata ɗan kwalin, irin me Steps ɗin nan, sai ta yafa mata farin gyale a kafaɗan ta, sannan ta ciro mata takalmin ta me tudu me haɗe da jakan sa, kalan Baby maroon Colour, sai ɗan ratsin fari a jiki, ƙasan takalmin kuma baƙi ne.

     Tare suka fito Parlour inda suke murmushi dukan su, kasancewar Suhaima tana faɗa mata yanda tayi kyau ne, wai “Yaya Ray zai zauce idan ya ganta”. Shi ne take murmushi itama tana taya ta

Tunda suka fito Parlour’n ya sauke idon sa kanta, kallon ta kawai yake yi tamkar idanun sa za su faɗo, shima sanye yake da kalan shaddar ta, yayi mugun kyau sosai

Ita ma bata hange sa ba, tunda gaba ɗayan su ne suke zaune a parlour’n, shiyasa tunda tayi musu kallo ɗaya ta ɗauke kanta

Ammee tace mata, “ta ƙariso wajen ta”.

Inda ta zauna a gefen ta, Ammee na riƙe da hannun ta

Su Zannurain sai faman tsokanar ta suke yi suna ce mata “Matar Yayan mu”.

Ita dai sai murmushi take yi

Sai da Uncle ya dakatar da su sannan suka yi shiru, ya soma musu nasiha daga ita har shi ɗin, sannan suka saka musu albarka har Ammee, suka yi musu addu’an zama lafiya har ƙarshen rayuwan su, tare da samun zuri’a ɗayyiba

Gaba ɗaya wajen suke amsa wa, ban da su da suke amsa wa a zuciyar su.

    Har waje suka rako su inda za su shiga mota, RAUDHA da Suhaima suka rungume juna har da hawaye

Faruk ya ja motan, su kuma suna zaune a baya, tunda suka shiga ko motsi ba ta yi bare ta ɗago kai ta kalli Ray ɗin, duk da kuwa tana jin sanda ya lalubo hannun ta ya riƙe gam

Tafiya suka yi kamar na mintuna sha biyar, sai suka tsaya, horn akayi suka shiga wani gida, ashe a nan ɗin za su kwana zuwa gobe su wuce Kaduna, Gidan Ray ne da Uncle ɗin sa ya ba shi, ko da wataran sun zo a nan za su riƙa sauka.

          Sai da suka fito sannan RAUDHA ta ware idanun ta tana kallon gidan, a ranta tana mamakin kenan ba Kaduna za su koma ba? Sosai gidan yayi mata kyau duk da babu wani yalwataccen haske, haraban gidan ba wani faɗi bane, amma zai iya cin motoci kamar biyu haka, sai kuma yanda aka yalwata ko ina da flowers masu ban sha’awa da abubuwan more rayuwa

Sanda suka shiga parlour’n ne, ai sai kallo ya koma sama, domin babu ƙarya, ba ƙaramin kuɗi Daddy ya kashe wajen tsara mata gidan nata ba, ƴar gatan Daddy kenan, gida biyu duk ita kaɗai, kuma an kashe kuɗi ba Ni da kuɗi ba, ɗakuna uku ne da Toilet a cikin su, sai Parlour da kichen tare da store, ko ina yayi kyau matuƙa tunda duk an cika su da kaya masu ban sha’awa, gaba ɗaya babu kayan Nigeria a gidan, shiyasa komi zai ba ka sha’awa da zaran ka kalla.

      Tun a waje suka yi sallama da Faruk ya koma, su biyun suka shigo. Suna shiga ya sake riƙe mata hannu, hakan yasa ta juyo tana kallon sa tunda ita ce a gaba, murmushi suka sakar wa juna, inda ya matso kusa da ita yana faɗin, “alhmadulillah! Yau dai ga Pretty a gidan Captain Rayyan, sai godiyar Allah”.

Murmushi kawai tayi masa, batare da ta ce komi ba idanun ta a kansa

Janyo ta yayi ya jingina ta a jikin sa, sannan suka taka har zuwa cikin parlour’n, ya zaunar da ita yana me zama gefen ta, hannun ta still ya riƙe yana me jan yatsun hannun, ita kuma tana bin hannun da kallo kamar yanda yake yi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button