RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

“Ina son ki pretty, ban San ya zan kwatanta miki ƙaunar da nake miki ba a zuciya ta, amma kuma zan so ki bani dama domin nuna miki tsatsan sa a fili, ina fata Allah ya bar mu tare har ƙarshen numfashin mu”.
“Amin Ƙalby”. Tafaɗa tana kallon sa
Murmushi suka sakar wa juna kafin tace, “I love You more than you Ƙalby”. Ta ƙare maganar da jingina a jikin sa
Hannayen sa ya saka gaba ɗaya ya rungume ta yana me sumbatar goshin ta, sun ɗau kamar mintuna biyar a haka, kafin yace, “Pretty ko kina jin barci?”
Ɗago kanta tayi tana kallon sa, kafin ta girgiza masa kai tana cewa, “na yi tunanin yau za mu koma Kaduna?”
Fuskar ta ya shafa yana bata amsa da faɗin, “a’a, Uncle ya ce mu zauna a nan sai zuwa gobe, sabida ba ya son tafiyan dare”.
Gyaɗa kanta tayi tana me mayar da kanta ta sake ɗaura wa a kafaɗan sa
Ahankali ya matso da bakin sa setting kunnen ta ya raɗa mata magana, sai ta ɗago tana kallon sa, suka sakar wa junan su murmushi. Tashi yayi yana tayar da ita, sannan ya ƙarisa bakin ƙofa ya rufe, ya dawo ya riƙe mata hannu suka yi cikin ɗaya daga cikin ɗakunan
Koda suka shiga alwala suka ɗauro gaba ɗayan su, inda ya sauya kayan sa zuwa jallabiya, itama ta sauya zuwa riga da wando na barci, ta saka Hijab suka soma jero salloli, kawai don godiya ga Allah, kamar yanda Ray ya alƙawarun ta, duk randa ya mallake ta a matsayin matar sa, to fa a ranan zai kwana godiya ga Allah ne, duk da sosai yake jure buƙatar sa a gare ta, amma kuma soyayyar da yake mata ya fi rinjaye a zuciyar sa a bisa sha’awar ta, don dai kwana ɗaya kacal zai iya jure wa, ya cije don ganin be mata komi ba. ???? Kaji masoyan asali ????????
Tun suna yi har barci ya soma fizgar RAUDHA, dole ta kwanta a kan daddumar ta soma barcin
Shi kuma ya ci gaba da yi har sai da ukun dare yayi, sannan ya ɗauke ta ya mayar da ita kan gado, yana me zame mata Hijab ɗin, a gefen ta ya kwanta yana ta faman kallon ta yana lazimi, tare da tsarkake Allah da yayi wannan kyakykyawar halittan, RAUDHA tana da kyau matuƙa.
har sanda aka kira sallah, sannan ya tashi yayi nafila, ya tashe ta suka yi sallan asuba, a tare suka koma barcin har zuwa safe.
Sai da Abubakar ya kawo musu breakfast sannan suka tashi a lokacin, shima be tsaya ba ya koma tunda ya gaishe su, saboda aiki zai tafi
Ƙarfe 09:00am jirgin su zai ɗaga, shiyasa suka yi saurin shirya wa suka karya suka baro gidan, suna hawa jirgi sai Kaduna garin gwamna Nasiru El. Rufa’i. Me aiki domin ci gaban al’umman sa. Ba ya bari a ci sai dai a gani a ƙas..
[4/14, 11:24 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
*RAUDHA*
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO*????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
*RAMADHAN MUBARAKH*????????????
2021.
.
*NOT EDITED* ___________________________????
*SEASON FIFTY FIVE*
_______???? Zan iya cewa komi na gidan nan ɗaya yake da wancan, sai dai banbancin colour da kuma haɗuwa, amma tsadan su ɗaya, wannan dai ya fi haɗuwa sosai, akasarin komi fari aka saka mata shiyasa yafi ɗaukar ido da burge wa.
A gajiye suka shigo gidan, don haka sallah suka soma gabatar wa na azahar da asar, sannan Ray ya aiki Drever’n sa don ya yo musu take-away, kafin ma ya dawo har RAUDHA ta soma barci, sabida ba ƙaramin barci take ji ba
Tashin ta yayi yace, “ta zo su ci abinci”.
Daƙyar ta tashi tana ɓata fuska, gaba ɗaya tayi yaushi sabida barcin ya rufe mata ido, zama tayi gefen gadon, ta dafe gadon da hannayen ta tana me lumshe idanun ta
Ahaka Ray ya fito daga Toilet ya sake tarar da ita har barci ya soma ɗaukar ta, ruwan hannun sa ya yarfa mata yana me faɗin, “Baby wake-up mana”.
Buɗe ido tayi ta ɗan kalle sa kaɗan da idanun ta da suka sauya kala, sai ta ɓata fuska tace, “Ka bar Ni inyi barcin don Allah, ba na jin yunwa”.
“Ban yarda ba, ke dai kawai ki ce barci kike ji, amma ba wai ki ce ba kya jin yunwa ba. miƙe kin ga idan kin ci sai ki koma ko?” Yayi maganar yana me lallaɓa ta
Turo baki tayi tana sosa kanta, sai kuma ta miƙe tana nufan ƙofan zata fice
Riƙe ta yayi suka fita Parlour, ya zaunar da ita saman kujera, sannan ya wuce kichen don ɗauko Plate
Jingina tayi da jikin kujeran tana me lumshe idanun ta, har ya dawo ya sake abincin bata motsa ba, shi da kansa ya bata abincin tunda ta ƙi ci, yana ta faman lallaɓa ta, sai daga baya ne ta Ware sosai taci tunda tana jin yunwa
Sai da suka gama yace mata “ta koma ta kwanta, shima fita zai yi”.
Bedroom ta koma ta kwanta akan gado, babu jima wa barci ya ɗauke ta
Shi kuma sai da yayi wanka ya shirya cikin manyan kaya, gezna ne me ruwan kore, amma Light ne, ta sha aiki sosai har da babban rigan ta, sai dai be saka babban rigan ba, ya murza hulan sa mu haɗu a banki, sannan ya feshe ko ina nasa da turaruka, sak ya fito a Angon sa sai ƙyalli yake yi, fuskar sa na fid da annuri, keey ɗin mota ya ɗauka tare da wayan sa, ya matso gadon yayi mata kiss a leɓen ta, sannan ya shafa kanta yana murmushi a ransa yana aiyana abubuwa da dama. Fita yayi ya hau motan sa ya nufi gidan su RAUDHA
A can ya wuni wajen Daddy, har magriba be dawo ba, sai da RAUDHA ta kira sa tana masa shagwaɓan “ya bar ta ita kaɗai” sannan ne yayi haraman taho wa, da zai dawo sai da ya biya ya siya kazan amarcin sa, don yau so yake yi ya zama cikakken Angon sa
Da fara’an sa ya shigo gidan, inda ta tarbe sa tana me rungume sa tana faɗa masa “how much she missed him” kafin ta amsa kayan hannun sa tana me ƙara masa sannu da zuwa har da duƙawa alamun girmamawa
Sosai Ray yaji daɗin tarban nan da tayi masa, har ya kasa ɓoye wa ya janyo ta jikin sa yana cewa, “Baby ashe kin iya tarban miji haka? Gaskiya zan sha mamaki ashe, gaba ɗaya ina miki kallon wacce dole sai na koya mata irin waɗannan abubuwan na kula da miji”.
Kallon sa tayi ta ɓata fuska kafin tace, “kenan kana nufin ban iya ba?”
“No Ina nufin dai abubuwan nan na Hausa wa nake son koya miki”.
Taɓe baki tayi tace, “Ok na gano ka, wai don na amshi kayan hannun ka?”
“Yes ashe kin gane”. Yayi maganar yana murmushi
Turo baki tayi, kafin ta kamo hannun sa tace, “to amshi kayan ka, bazan sake ba”.
Dariya yayi sosai yana son ƙwace hannun sa da take tura masa ledan sai ya amsa, cikin dariyan yace, “sorry Baby, bazan sake ba, wlh suɓutan baki ne, ai na san duk wanda ya koyi ilmi dole zai san wannan, amma kuma..”
“Amma kuma me?..” tayi maganar tana tsare sa da ido
“Bar shi kawai ya wuce, bari in je inyi sallah ana kiran Isha’i, ki je ki ajiye ledan please”.
Bata ce mishi komi ba ta juya da ledan a hannun ta
Shi kuma ya fice zuwa Masallaci.
????????????
A wannan dare ne Ray ya tabbatar wa kansa, RAUDHA cikakkiyar mace ce, ba kamar yanda yake mata kallo ba, be taɓa tunani ko a mafarki zai iya samun ta a yanda ya same ta yau ba, sai ga shi ya sha matuƙar mamaki, har kuka yayi sabida nadaman abinda yayi mata, tabbas yau yayi dana-sani, dana-sanin abubuwan da yayi mata, da kuma sanya zargin ta a zuciya, ba don soyayyar ta tayi masa kamu ba, da tuni ya daɗe da rabuwa da ita, duk a sabida yana mata kallon mazinaciya