RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

Wannan ranan ta zo masa a matuƙar farin cikin da bazai taɓa manta ta a kundin rayuwan sa ba, ya kuma sake neman yafiyan ta sosai, tare da nuna mata nadaman sa
Dama wannan ranan take jira, kuma ga shi ya zo mata yanda take so, yau Mijin ta zai dena mata kallon ballagaza har a cikin zuciyar sa, ko da be nuna ba, tayi imani da Allah duk da yayi mata alƙawari, da ace ba haka ya same ta ba, dole sai ya riƙa kallon ta da abun, kuma hakan zai iya kawo saɓani a auren su, abinda yasa ta sake amince wa da auren sa, saboda ta nuna masa kuskuren sa, ta san cewa da ta aikata Zina kafin auren su, to, baza ta taɓa amince masa da auren su ba, domin kuwa ta san zargi shi zai riƙa yawo cikin auren su.
Alhmadulillah zaman auren su suna gina ta ne ta santsan kulawa da nuna tattali da soyayya, Ray ya dage yana ta gurzan Angon cin sa yanda yake so, hutun sati biyu aka ba shi a wajen aiki, kullum yana gida be fita ko ina, yana liƙe da Matar sa har sai da ya cinye kwanakin nan, sannan ne ya soma fita, kuma kullum duniya aika wa yake yi ayi musu take-away, sai daga baya ne aka turo Saude don ta riƙa mata aiyukan gidan, shiyasa RAUDHA babu abinda take yi yanzu sai zaman hutu da kuma tattalin mijin ta, duk hanyar da tasan zata faranta masa tana yi sosai matuƙa, duk da a yanzu tana buƙatar koyan girki itama don ta riƙa mishi, sabida ta san ladan da ake samu, shiyasa take kwaɗayin komi na gidan ta ace ta iya, a sannu- a sannu Saude take koya mata wasu abubuwan, irin su gyara gado da kunna Kuka gas, da dafa ruwan zafi, coz tunda take bata taɓa shiga kichen da sunan girki ba, bata ma san yanda ake kunna Kuka gas ɗin ba, sai yanzu da ta soma koya. Alhmadulillah tana ɗan gane wa kaɗan, duk da kasancewar ta me saurin gane abu, amma kuma sosai take shan wahala, domin sanda aka soma koya mata gyaran gado, sai da aka shafe wajen sati biyu ana abu ɗaya, daƙyar ta samu ta iya, idan kuma tayi dole sai ka gane ba gwana tayi ba.
Shi Ray dariya yake yi duk sanda ya zo ya tarar ana koya mata irin waɗannan abubuwan, wai kamar ta har shara sai an koya mata, to riƙe tsintsiyan ma ba yanda ake yi take yi ba, to ana haka ne ta soma ciwo gadan-gadan, faraɗ ɗaya ciwo ya kamata me tsananin gaske, wanda har sai da aka dangana da asibiti, duk a tunanin su ciki ne, amma kuma abun mamakin ba shi ne ba, kawai ciwo ne dai take fama dashi, daga tace ciwon kai, sai ta ce cikin ta na mata ciwo, to duk dai ba’a yi tunanin wani abun bane, haka ake kula da ita, tsawon sati ta ɗan samu sauƙi kafin suka koma gida
A ranan da suka koma kuma, sai ga shi cikin ta ya murɗe mata da ciwo me tsananin gaske, lokaci ɗaya jini yayi ta zuban mata
Hankalin Ray ya tashi tsantsa, haka ya sumgume ta sai asibiti, abun mamaki da al’ajabi, wai ɓari tayi, su kan su likitocin sun sha mamaki, domin kuwa basu gano tana ɗauke da ciki ba, amma kuma sai ga shi ciki suke gani tayi ɓari
Hakan da Daddy yaji, sai kawai tunanin sa ya basa tabbas akwai matsala, dole su dangana dana Islamic, ko za’a iya gano abinda ke faruwa. Malamin da suka nema mata magani a baya shi suka koma masa, kuma shi ya basu magani a wannan karon, domin ce musu yayi, “tabbas har yanzu akwai aljanun nan suna bibiyan ta, kuma sun yi alƙwarin sai sun cutar da ita, kuma su ne suka ɓoye cikin, daga ƙarshe suka zubar mata, domin su ne suke saka ta ciwon nan, dole sai sun tashi tsaye da yin addu’a da neman magani, ta hakan ne kaɗai za a iya tsira daga kaidin su”.
To tun daga ranan, ba su zauna ba, an ci gaba da nema wa RAUDHA magani, sannan itama tana yi sosai, tana kiyaye duk abinda zai jawo su gare ta, sallan dare kuwa tun bata saba ba, idan Ray ya tashe ta su yi, har yanzu ta saba, tare suke raba dare suna ibadan Allah, sai ga shi har azumin Litinin da Alhamis idan ta samu iko tana yi
Alhmadulillah sun ga sauyi sosai, domin lafiya yanzu babu abinda ke damun RAUDHA tunda ta samu wannan cikin, bata ƙara yin ciwo ba, har sanda ya soma girma suka soma zuwa awo
A lokacin ne kuma Ramcy ta haihu ɗiya mace, zo ku ga murna wajen RAUDHA tamkar ita ce ta haihu, musamman yanda ranan suna suka bata bazata, yarinyan taci sunan ta RAUDHA, tayi farin ciki tsantsa har da kukan ta, tabbas ta san cewa Ramcy na matuƙar ƙaunar ta, baza ta taɓa yin ƙawa kamar ta ba, duk da a yanzu ta zame mata ƴar uwa rabin jiki.
Abubuwan da akayi a sunan RAUDHA, da suke kiran ta, Little RAUDHA, ba ya faɗuwa, Daddy, Suhaib da kuma Ray, sun Yi bajinta sosai a sunan nan, babu abinda basu yi ba, duk abinda ake wa ƴar gata Ramcy da ɗiyar ta sun samu, ita kanta RAUDHA abun da tayi ba a magana.
Wata huɗu da haihuwar Ramcy, itama RAUDHA ta haihu ɗiya mace, yarinyan sak Mahaifiyar ta, tamkar dai tayi kaki ta tofar, sai dai ita bata da irin hasken nan jawur tamkar zabiya irin na RAUDHA, hasken ta irin na Ray ne. Ranan suna taci sunan Maman RAUDHA, wato Ruƙayya suna kiran ta Iman.
Rayuwa kenan, sai ga RAUDHA da ɗiya, tamkar dai ba ita ba idan kuka duba rayuwan ta na baya, sai ga shi itama ta samu wacce zata riƙa wa faɗa, domin dai yarinyan tunda ta soma wayau halin ta ya bayyana tamkar RAUDHA, ko kaɗan ba ta ji yarinyan, ga taɓara kuma baka isa ka hana ta ba, tana da taurin kai irin uwar ta, don har ta ƙere ta tunda akwai ta da zuciya, yanzu da za su yi mata faɗa, ta dinga kuka kenan har sai ta kwana tana naci, kuma baza ta ci abinci ba saboda ita a ganin ta sun ɓata mata rai, gaskiya Rayyan da RAUDHA suna fama da Iman, sai dai nema mata shiriya suke wajen Allah, tare da dage wa wajen sun ga sun bata tarbiyya me kyau.
Shekarun ta huɗu cif, RAUDHA ta sake haihuwa, wannan karon namiji ne, inda ya ci sunan Uncle, wato Hassan, suna kiran sa da Aslam. Watan shi bakwai sai ga RAUDHA da wani cikin, nan RAUDHA ta haukace “wai baza ta ƙara yarda ta haihu yanzu ba”. Tun Ray na lallaɓa ta har dai ya gaji ya kai maganar wajen Daddy, shima Daddy duk rarrashin duniya yayi mata akan ta bar cikin, amma ina ta ƙi, wai bata san zancen ba, tunda a lokacin so take yi ta koma school, sannan tana son soma aiki a Companin Daddy da ya buɗe domin ta, ƙaramin Company ne irin kayayyakin mata na kwalliya, da suturu, har da na ƙananan yara duk akwai, kuma nan ba da daɗe wa ba ake son kawo injina waɗanda za su iya haɗa kayayyakin a Companin, ba sai an je ƙasashen waje an siyo ba, tunda dama daga can ake kawo komi, kyauta Daddy ya danƙa mata, inda aka saka wa Companin sunan Ta, *RAUDHA M.M Company.*
Ƙarshe dai sai da suka yi faɗa sosai akan wannan maganar, RAUDHA fa sosai ta tubure sai ta zubar, har tayi yaji ta koma gida
Ran Daddy be taɓa ɓaci ba akanta, sai wannan karon, amma kuma sai ya danne yayi mata nasiha tare da nuna mata illan yin hakan, amma tamkar zuga ta ake yi, har Suhaib sai da ya zo musamman ya bata haƙuri ta koma gidan ta, ta haifi cikin ta, ganin dai rarrashin bazai mata ba, dole suka nuna mata ɓacin ransu, kuma Daddy yace, “muddin ta bari cikin nan ya zube, ko ba da sanin ta bane, wlh sai yayi mummunan saɓa mata, daga ranan zai cire hannun sa a komi nata”.
Ba ita kaɗai ba, har ta Suhaib yayi mamakin furucin Daddy, amma kuma babu damar magana tunda tuni ya bar wurin da ɓacin rai.