RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

A ranan RAUDHA ta haɗa komi nata ta koma gidan Ray, dama acan ta bar Iman, sai ta taho da Aslam. A ranan kuwa kowa sai da ya ga fushin ta, daga yaran har uban nasu, domin gaba ɗaya ta ɗauke wa Ray, ko magana ba ta masa, Iman kuwa duk ɓarnan da zata yi, kamata take yi ta duka kamar jaka, haka ma Aslam, sai ya gama jiga ta da kukan yunwa kafin take kama shi ta bashi nono ya sha, a ranan ma ta sami Ray yana zaune a ɗaki, tace masa, “gwara ya nemo masa abinci, don daga yau baza ta sake shayar dashi ba” haka dai ta ƙarishe haukan ta ta tafi, duk dai neman hanyar da za su yi faɗa tsiya-tsiya take so
Shi Ray idanu kawai ya zuba mata yana kallon ikon Allah, domin wlh tausayi take ba shi tsantsa, har yanzu gani yake yi aljanu ke juya mata ƙwaƙwalwa wani lokacin, domin abubuwan da take yi me hankali kamar ta bazai yi ba, shiyasa ya zira mata idanu, duk hanyoyin da ta ɓullo na tsiyan ta, ba ya biye mata.
A haka rayuwa taci gaba, inda har ta samu ta haihu ɗiya mace, har kuma lokacin ba su shirya ba, domin har yanzu RAUDHA gani take yi duk abinda Mahaifin ta yayi mata a wancan ranan laifin Ray ne, inda be kai ta ƙara ba, babu ta yanda mahaifin ta zai mata abinda be taɓa mata ba
Yarinya taci sunan mahaifiyar Ray, Hansa’u, za su kira ta da Islam.
A taƙaice dai daƙyar Ray ya samu suka shirya da RAUDHA, inda suka koma kamar da, amma da sharaɗin dole za su yi family planning, sai nan gaba za su sake haihuwa, babu yanda zai yi haka ya amince mata, tunda dai yana ƙaunar ta.
Alhmadulillah yanzu komi ya wuce, inda RAUDHA ta soma zuwa makaranta, kuma tana zuwa Company, kasuwanci sosai take yi, a gida da kuma wajen aiki, lokaci ɗaya Allah yasa mata albarka, sai ga shi ta zama wata Hajiya, tuni ta jawo Ramcy cikin Companin, tare suke yin komi, kuma tare suke saka hannun jarin su, itama yanzu Ƴaƴan ta uku ne, duka mata.
Fannin Farida ma yanzu ta koma aikin ta, tare suke zuwa da Suhaib, yanzu yaran su haɗu ne su ma, ban da Haneep da Abdul, yanzu sun ƙara haihuwar me sunan Maman Suhaib, suna ce mata Ummee, sai Meenal Auta, wannan sunan sun saka mata ne kawai saboda suna so, amma ba sunan kowa ba ne.
*TAMMAT BILLAH. ALHMADULILLAH! ALHMADULILLAH!! ALHMADULILLAH!!!*
_Duka-duka anan na kawo ƙarshen littafi na me suna RAUDHA, abubuwan da na faɗa dai-dai Allah ya bani ladan su, abubuwan da na faɗa ba dai-dai ba kuma, Allah na roƙe ka, ka yafe min, albarkacin wannan wata me falala. ????????_
*RAMADHAN MUFEEDA YA IKHWANY.*
*SAƘON NA MASOYA NA NE*
_Bazan taɓa manta wa daku ba, ina alfahari daku sosai, domin idan baku to ba na jin akwai Ni nima, Masoyana ako ina kuke, Ni taku *JIKAR LAWALI* ina ƙaunar ku, Allah ya bar mu tare._
_sai mun sake haɗuwa a sabon littafi na *NAFEESAT RETURN* Nan da bayan sallah. Bissalam._
Share this
[ad_2]