RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

Atamfar ba wata me karikitai bane, gaba ɗayan ta me ruwan silver ne, sai akayi zane-zane a jikin ta ƙalilan da kalan fari da blue, wanda sosai ya ɗauki white skin ɗin ta, yayi mata mugun kyau, ga shi ɗinkin kamar dama an gwada ta, skert ɗin ya zauna mata ɗas a jikin ta, da akwai tsagu ta baya har zuwa kusa da gwiwar ta, sai rigan kuma me collar akayi mata da hannun link, amma wajen ƙirjin ta zuwa bayan ta duk net aka saka mata blue colour, sai hannun ma na net ne, illa wajen link ɗin da aka zizara atamfar, sannan collarn shima da atamfan akayi mata, rigan itama ta zauna mata ɗas gunun sha’awa, tare da fito mata da kyakykyawar ƙirar jikin ta
Sai dai matsalan kuma ta rasa yanda zata yi ta ɗaura ɗankwalin, ga shi tana son ta ɗaura ba ta son saka wani abu a kanta, dole ta ɗauki waya tayi kiran Saude, ita ta samu ta ɗaura mata me Steps ɗin nan, gashin ta ya zubo ta tsakiya, sai ta yafa farin gyale a gefen kafaɗan ta na dama, hohoho Fans thinks about yanda RAUDHAN ku tayi kyau, amma Ni idan na faɗa dole zan rage wani abu aradun Allah kuwa
Tana cikin zira Hill shoes ɗin ta ne, wayan ta ta soma ƙara, ta ɗauka tana murmushi don tasan ko waye ne
Sanar mata yayi ya iso, sai tace, “bari zata aiko a wuce da shi masaukin sa”.
Daga nan ta ajiye wayan, taci gaba da sanya takalmin, kasancewar me igiya ne, sai da ta gama sannan ta miƙe batare da ta ɗauki wayan nata ba ta fito daga ɗakin, Direct Block two ta wuce inda a nan ne aka sauke Ray
Da shigan ta ƙayataccen parlour’n dake ta faman tashin ƙamshi saboda gyaran da ya sha na musamman, sai ta hange sa can saman kujeru kansa a ƙasa yana latsa waya, yana sanye cikin ɗanyen shadda me ruwan ƙasa, da hulan sa zanna bukar
Sai da gaban ta yayi muguwar faɗuwa saboda kawai ganin sa da tayi, amma sai ta daure ta soma taka wa a hankali cikin tafiyan ta me tsananin burge duk mahalukin da ya gani
Abun mamaki! yawan kusantan ta da shi yawan jiyo daddaɗan ƙamshin turaren sa, wanda tuni ta rigada ta san waye mamallakin turaren, ko barci ta tashi idan har aka tambaye ta ƙamshin waye wannan? Zata buɗe baki tace na Rayyan ne, amma sai kuma bata damu ba, don ko kusa zuciyar ta bata taɓa kawo mata tunanin shi ɗin zata gani ba, shi ne wanda suke soyayya a waya ba.
Ta iso tsakankanin kujerun inda sosai a wannan lokacin turaren nasa suka yi mata muguwar shiga hanci, a zuciyar ta tana me mamakin “me zai kawo sa nan bare har turaren sa ya cika wajen?” Sai kawai ta haɗa idanu dashi sakamakon ɗago kansa da yayi yana kallon ta
Wani irin zaro idanun ta waje tayi, ido cikin ido suke kallon juna, bakin ta na rawa tace, Kai!.. kai me kazo yi nan?”
.
_Hhhh to tambaye shi dai? Shin me zai faru? Ga RAUDHA ga Captain Rayyan sun haɗu?_
_comment ɗin ku kaɗai zai saka nasan kuna son ci gaba, idan kuma ba haka ba, mu haɗu bayan sallah idan Allah ya kai mu da rai da lafiya insha Allahu._
_Love You Fans._
[4/12, 8:23 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????
????????????????????
????????????????????
*RAUDHA*
????????????????????
????????????????????
????????????????????????????????????????
*MALLAKAR:* ✍️
_Nafisat Ismail Lawal Goma._
*بسم الله الرحمن الرحيم*
⚖
*FEENAH WRITER’S ASSO*????
”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓
*JIKAR LAWALI CE*✍️
*Wattapad: UmmuDahirah*????
*F.W.A????/*
*RAMADHAN MUBARAKH*????????????
2021.
*HADHISI*
_An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar Allah ya ƙara musu yarda, daga Manzon Allah tsira da aminci su tabbata a gare shi ya ce, “kada wani mutum yayi nema akan ɗan uwan sa, har sai ya bar wannan neman kafin shi ya nema, ko kuma idan ya bashi izni.” An ruwaito daga Bukhari da Muslim. Ingantaccen hadisi daga Bukhari._
.
*NOT EDITED* ___________________________????
*SEASON FIFTY ONE*
_______???? Murmushi ne ya suɓuce a kan kyakykyawar farar fuskar sa, sai dai be iya cewa komi ba illa kallon ta da yake yi
While itama ta kasa ɗauke idanun ta kansa, sai dai a wannan lokacin sosai fuskarta ta kumbura da ɓacin rai, cike da fushin da bata san na mene ne ba tace, “ba’a gaya maka nan ɗin inda zan ajiye baƙo na bane da zaka zo ka zauna?”
Sai kuma ta juya tana kwaɗa wa Saude kira, taku ɗaya biyu tayi ta tsinkayi muryan sa yana faɗin
“Pretty ki bar wahalar da kanki mana, Ni ne Ƙalby ɗin ki”.
Cakk ta tsaya tana juyo wa gare sa, ido cikin ido take kallon sa but ta kasa magana, sai kai komo da zuciyar ta ke yi wajen bugawa da ƙarfi
Murmushi ya sake yi yace, “nasan zaki yi mamaki da jin kalamai na, but ba abun mamaki bane, na shirya tsab don bayyana miki Ni ne wanda kike soyayya dashi batare da kin san ko waye ba, Pretty Ni ne Ƙalby ɗin ki, wanda kike matuƙar ƙauna da..”
Tsayar dashi tayi ta hanyar ɗaga masa hannu da faɗin, “ya ishe ka da Allah Malam”.
Sake ware idanun ta da suke ɗigar hawaye tayi a kansa, wanda tun soma maganar nasa suka soma kwaranya. Sosai laɓɓan ta suke rawa but ta kasa furta abinda ke ranta, illa wani irin ƙunci da ya tokare mata maƙogwaro, juya wa tayi da sauri tayi hanyar fice wa parlour’n da gudun ta
Da sauri Ray ya tashi tsaye yana faman kwaɗa mata kira, amma ina tuni ta fice.
A tsakankanin farandan benen ta zube ƙasa ta hau rusa kuka, domin ko kaɗan baza ta iya kai kanta inda take son zuwa ba, saboda rawan da ƙafafun ta suke yi, gaba ɗaya jikin ta ma rawa yake yi tamkar an jona ta da shocking, ko gaban ta ma ba ta iya gani sabida hawayen da suke kwaranya cikin idanun ta, har wani jiri-jiri take ji Coz tuna maganganun sa dake dawo mata cikin dodon kunne, wani irin yawu take haɗiya tana jan numfashi tamkar zata shiɗe, daƙyar ta iya buɗe bakin ta daga laɓɓan ta ta furta “Noo! Ƙarya yake yi! Ƙarya ne! Bazai.. ba..zai taɓa za..ma shi.. shiii..” Lokaci ɗaya numfashin ta ya ɗauke sabida wani irin mahaukacin ja da tayi masa.
Dai-dai lokacin da ta ƙarisa sulale wa ƙasa, a lokacin ne kuma Daddy ya buɗo Lifter ya hange ta, Sunan ta ya kira da ƙarfi ya nufo ta cikin tashin hankali
A lokacin shima Ray ya fito a firgice ya tarar da abinda ke faruwa
Daddy na kallon sa yace, “taimaka Captain, taimaka min, Baby ba ta numfashi”.
Cakk Ray ya ɗauke ta suka yi Lifter da sauri, suna sauka ƙasa suka fita waje, Daddy na kwaɗa wa Drever’n sa kira, nan da nan ya ƙariso, dama ba nisa yayi ba tunda yanzu ya sauke sa
motan aka shigar da ita, Ray ya shiga mazaunin Drever, Daddy kuma na zaune da ita a baya suka yi Hospital.
Suna zuwa babu ɓata lokaci aka amshe ta, aka yi da ita emergency word, inda anan likitoci suka soma ba ta taimakon gaggawa
Daga Daddy har Rayyan an kasa samun wanda sai zauna, sai kai komo suke yi ko wanne zuciyar sa da tunanin da yake yi, shi shaf Daddy tunanin sa be kawo masa ya tambayi zuwan Ray ɗin ba, ta ɗiyar sa yake yi hankalin sa duk a tashe.
Fitowar likitan da yayi jagora Wajen duba RAUDHAN, yasa gaba ɗaya suka dawo dogon tunanin da suka afka, suka nufe sa da sauri suna tambayan sa “shin ta farka?”
Likitan kwantar musu da hankali ya soma yi, kafin yayi musu bayanin “babu abinda ke damun ta, sun yi nasaran dai-dai ta numfashin ta sabida suman da tayi, dama abinda ya kawo hakan, sakamakon shiga ruɗu ne da tayi”.
Daga Daddy har Ray nannauyan numfashi suka sauke sabida jin abinda likitan ya faɗa, ko wanne cikin su na faɗin “alhmadulillah”