RAUDHA 1-END

RAUDHA Page 51 to 60 (The End)

Hannu Daddy yasa ya riƙe mata hannu, gaba ɗaya zuciyar sa ta gama karaya da tausayin Ray ɗin, yace, “Baby kin ga ya ba ki haƙuri, ko menene yayi miki ki yafe masa kinji? Babu kyau riƙo, bare shi da ya durƙusa gaban ki ya nemi yafiyan ki, na tabbata babu wanda zai fi shi son ki”.

.

_to Fans muna cikin tsaka me wuya MASOYAN RAYYAN, wani amsa kuke tunanin RAUDHA zata ba su? shin zata amince ta yafe masa ko kuma a’a? Kuna dai jin kalaman ta._

[4/14, 8:14 AM] نفيسة أم طاهرة: ????????????????????????????????????????

????????????????????

????????????????????

*RAUDHA*

????????????????????

????????????????????

????????????????????????????????????????

*MALLAKAR:* ✍️

_Nafisat Ismail Lawal Goma._

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*FEENAH WRITER’S ASSO*????

”’®Ɗaya tamkar da Dubu”’????✓

*JIKAR LAWALI CE*✍️

*Wattapad: UmmuDahirah*????

*F.W.A????/*

*RAMADHAN MUBARAKH*????????????

2021.

.

*NOT EDITED* ___________________________????

*SEASON FIFTY TWO*

_______???? Hannun ta ta zame daga na Daddy, ta tashi da gudu tabar ɗakin tana sake rushe wa da wani sabon kukan

Daga Daddy har Ray dake hawaye bin ta suka yi da idanu har ta fice

Daddy sosai jikin sa ya sake sanyi matuƙa, har ya kasa ma yin magana, illa shiru da yayi yana afka wa duniyar tunani

While Ray, shima ya kasa koda jirga wa ne, illa lumshe idanuwan sa da yayi yana sauraron bugun zuciyar sa da ya sauya, ba ya jin zai iya jure rashin RAUDHA a tare dashi, yana matuƙar ƙaunar ta, ya rigada ya saka ta can cikin zuciyar sa, kuma fitan ta zai yi wuya a gare sa, tabbas yana ji a jikin sa muddin ya rasa ta zai iya shiga wani hali, shi kansa be san iya adadin ƙaunar da yake mata ba, kuma be san meyasaka soyayya tayi masa muguwar kamun nan ba..

    Muryan Daddy shi ya katse masa tunanin sa, yace mishi “ya je insha Allahu idan RAUDHA rabon sa ne, zai same ta, shi kansa yana goyan bayan ya kasance miji a gare ta”.

Sosai Daddy ya ƙara masa ƙwarin gwiwa, kuma ya ce mishi ya dage wajen bata haƙuri, insha Allahu shi ke da nasara, shima zai taya sa roƙon ta 

    Rayyan yaji daɗin kalaman Daddy, haka yayi masa sallama ya wuce Kaduna, sai dai a ƙasan zuciyar sa tunanin RAUDHA ne maƙil, amma babu yanda zai iya tunda yasan hakan sai ya faru.

              ????????????

    Fannin RAUDHA kuwa abu yayi tsamari, gaba ɗaya ta hana kanta sukuni, ko kaɗan taƙi sauraren Daddy da maganar, da ya faro zancen zata soma mishi kuka akan “ba ta son sake jin maganar Rayyan”. A cikin kwana biyu sai gata ta zabge sosai sabida damuwar da ta saka wa kanta, sosai take wahaltuwa da rashin Ƙalby ɗin ta, ita kanta ta san zai yi wuya ta jure rashin sa, tana mishi mahaukacin son da baki ma bazai iya fasalta shi ba, soyayyar sa ya rigada yabi jinin jikin ta, duk yanda ta so ta manta shi a ranta, ta cire sa ta goge sa gaba ɗaya a babin rayuwan ta, tayi rayuwa tamkar ma bata taɓa sanin sa ba ta kasa, dole ciwo ya kwantar da ita

Daddy gaba ɗaya hankalin sa ya tashi sosai, tausayin ɗiyar sa ya cika masa zuciya, sai dai taurin kanta yasa tana wahalar da kanta bayan tana da maganin matsalan ta, Doctor ya samo mace tana kula da ita a gida, da abun yayi tsamari dole aka wuce da ita asibiti, abu kamar wasa sai ga RAUDHA magashiyan tana jinya me tsanani har da su ƙarin ruwa, damuwar da ta saka a ranta ya haifar mata da ciwo me tsanani

Dole Daddy ya kira Suhaib ya sanar masa da komi, a ranan sai ga shi ya iso, sosai hankalin sa ya tashi ganin ƙanwar sa ta rame matuƙa, tausayin ta sosai ya kama shi, ba ma ita kaɗai ba har Rayyan, domin yasan cewa shima yana cikin wani hali koda be sani ba, tun farko ya gane Rayyan na ƙaunar ta, amma be taɓa tunanin shi ke bibiyan ta har suke wannan soyayyan ba, Allah Sarki Rayyan, ya so kiran sa ya sanar masa abinda ke faruwa da RAUDHAN, sai kuma yaga wani sabon tashin hankalin ne zai ɗaura masa, dole ya zauna rarrashin ƙanwar tasa, yana faɗa mata “ta amince da Rayyan, ta yafe masa domin samun kwanciyar hankalin su gaba ɗaya, domin yasan cewa shima yana nan cikin tashin hankali fiye da yanda take ciki”.

Kuka ta fashe dashi tana kallon sa tace, “Yaya Ni bazan iya rayuwan aure da shi ba, infact ma ban taɓa saka wa a raina zai iya zamo min abokin rayuwa ba, Yaya kasan yanda na tsane mutumin nan duk a sabida abinda yayi min a baya? shi ne ya koya min tsanar sa, kuma ba na jin tsanar nasa zai iya goge wa a raina, domin wlh ji nake yi tamkar in kashe sa abaya saboda tsanar da nake mishi, but yanzu ba na jin haka saboda ya ragu sosai a raina, amma hakan ba wai yana nufin zan iya rayuwan aure da shi bane”.

Riƙe hannun ta yayi yace, “meyasaka Baby baza ki bar komi ya wuce ba? Kar ki manta Dude ya zuƙuna ya baki haƙuri, duk ƙimar sa da mutuncin sa ya ajiye gefe, a matsayin ki na ƙanwar sa ya duƙa a gaban ki ya baki haƙuri, meyasaka baza ki yafe masa ba uhm? Idan kin ce kin tsane sa ai kuma kina son sa tunda kin Yi soyayya dashi”.

“Yaya ai ban san shi ɗin waye ba shiyasa na so shi a rashin sani, amma yanzu ba zan iya auren sa ba, zan iya rayuwa da kowa ban dashi”.

Yace, “Baby idan har zan samu ki yafe ma Dude ɗina ki aure sa, to wlh nima zan duƙa a gaban ki domin nema masa alfarma, don Allah Baby ki yafe masa”.

Da sauri ta riƙo hannayen sa da yake shirin tashi ya duƙa mata, kuka sosai ta fashe da shi tana faɗin, “me ye haka Yaya? Me zaka yi don Allah?”

“Duƙa miki zan yi domin ki yafe ma Aboki na, Baby Yana matuƙar ƙaunar ki, domin nasan haka tun ba yanzu ba”.

Kuka taci gaba da yi batare da ta furta komi ba, dole ya zauna rarrashin ta tunda yasan matsalan ta yanzu, doctors ma sun CE a dena saka mata damuwa

Daƙyar ya samu tayi shiru, be sake mata maganar ba har Daddy ya dawo

Ganin yanda ta ɗan saki jikin ta sosai sai hankalin su ya kwanta.

     Washe gari sai ga Rayyan, ba su san waye ya sanar masa ba, sai ganin shi suka yi a Hospital ɗin, lokacin ma RAUDHA tana barci ne

Daddy yace, “Captain wa ne ne ya sanar maka muna asibiti ka zo?” Sai kuma ya juya akalan tambayan sa ga Suhaib yana cewa, “ko kai ne?”

“No Daddy ba Ni bane, ban ma yi tunanin sanar masa ba”.

Murmushi Ray Yayi yace, “Daddy duk abinda zai samu RAUDHA, wlh ina ji a jiki na! kuma duk halin da take ciki ina sane da komi, Daddy ƙaunar da nake mata bazai bar Ni kwanciyar hankali ba in har ba na bibiyan rayuwar ta”.

Daga Daddy har Suhaib sosai yai matuƙar ba su tausayi, barin ma ganin yanda ya sauya duk ya faɗa, ga tarin ƙasumba da ya bari a fuskar sa ko gyara ba ya samu, kamar dai ba shi ne ɗan gayen nan ba

        Ita kanta RAUDHA sai da zuciyar ta ta karye da kalaman sa, hawaye suka soma sintiri a fuskar ta, sabida tunda ya shigo muryan sa ya doki kunnen ta ta farka, ta rasa meyasa zuciyar ta ta kasa yafe masa, duk idan ta tuna abubuwan da yayi mata sai taji babu daɗi a ranta, duk da tana son ya fe masa amma kuma kasancewar akwai maganar soyayya a tsakanin su, sai ta ji sam ba ta ƙaunar ta yafe masa, da ace haka kawai ne dole zata yafe masa..

    Maganar Suhaib ne ya dawo da ita duniyar tunanin ta, inda yake tambayar ta “meyasaka take hawaye?”

Ita bata san tana hawayen ba ma, sai kawai ta fashe da kuka

“Mene ne kuma na kuka Daughter? Me aka yi miki? Ke kenan kullum ba kya gajiya da kuka? Kin san abinda doctor yace miki ki dena saka damuwa a ranki, gaba ɗaya kin tsangwami kanki, kin ƙi kiyi abinda ya kamata, kuma kin san duk abinda ya same ki tamkar mu ya sama, damuwar da kike ciki mu ma muna cikin sa gaba ɗaya”.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button