Uncategorized

HEEDAYAH 12

 

Mutumin ya ajiye turaren hannunsa ya isa gun Heedayah ya tsaya dab da ita yana kallonta bayan yyi make sure bbu me kallonsu yace “How are you?” 

Juyowa Heedayah tayi da sauri, lkci daya ta mike tana waige waige, shi dai bai sake cewa komai ba yana kallonta, kamar xata yi kuka tace “ka dawo 

xaka kai ni gun Ammina ne?” Jin shiru, ta kai hannu to see if he is still there, komawa gefe yyi yace “Ina Ammin taki take?” Tace “A can gidan 

Yakumbo mana” xai yi magana ya ga Mami ta tsaya daga inda take tana kallonsu, lkci daya ya juya ya koma shelf din turaren da ya baro, Mami ta nufo 

Heedayah da sauri ta kamo hannunta tace “Me yake ce maki?” Heedayah da ta 6ata fuska xata yi kuka tace “shine ya sa ni a bicycle muka tafi…” Mami 

ta juya wajen da taga Mutumin ya tafi taga wajen wayam, da ido duk ta bi wajen amma bata ga alamarsa ba, Heedayah da hawaye ya cika idonta tace 

“Baya son inje wajen Ammina” kama hannunta Mami tayi suka bar wajen har sannan tana kalle kallen mall din ko xata ga wannan mutumi, sai da suka 

biya abubuwan da suka siya sannan suka tafi mota, Mami na kallon Heedayah tace “But ya akayi kika san shi ne?” Tace “Na ji voice dinsa, shine….” 

Mami bata kuma cewa komai ba har suka bar shopping mall din. Bayan Magrib Shuraim ya iso gida, rabonsa da gidan tun jiya juma’ah da safe, dama ko 

wajen daurin auren Abban nasa ma bai je ba, sau daya ya kalli motar Abban nasa dake parking space ya dauke kai, ya fita motarsa ya rufe ya wuce 

xuwa entrance din gidan, bbu kowa parlon, ya tafi parlon Abbansa, sallama yyi still standing at the door, Abba dake rike da makullin mota alamar 

xai fita ne, ya amsa masa sallama sannan ya bude kofar ya shiga, Heedayah ce xaune parlon kan lallausan carpet da plate din watermelon a gabanta 

tana sha, kasa karasawa parlon yyi tun da ya ga Heedayah, sai da Abba ya daga kai ya kallesa sannan cike da kasaita ya karasa ciki, gaba daya bbu 

wani annuri a fuskarsa, can gefe ya duka yace “Ina yini Abba” Abba yace “Lafiya lau” mikewa yyi ya nufi kofa Abba ya bi sa da ido har ya fita, a 

compound Abba ya samesa xaune shi dai bai ce masa komai ba ya fita da motarsa da nufin maida Heedayah can gidan Mami. Washegari lahadi Abba ya tafi 

can gidan Mami don ranan xasu tafi gidan Baffa Mami su gaisa da kaka, Abba ne ke driving Mami na gaban motar Heedayah kuma na baya a xaune, jifa 

jifa suke magana da ya shafi field din aikinsu, Mami dake danna wayarta ta kalli barrister tace “Hope ba dadewa xa mu yi ba wajen mama coz xa mu yi 

sallama da Amira nan da sha biyu xa su wuce” Abba ya d’an yi shiru kafin yace “I mean it Rahinah… Farida baxata je Abuja ba, are you trying to 

show ni ban isa riketa ba” Mami tace “A’a ae hutu xata je, in sha Allah xata dawo soon…” Yace “Wani hutun?” tace “Mid term….” Yace “Am damn 

serious baxata xauna Abuja ba” Mami tayi murmushi tace “To shkkn” a haka suka isa gidan Baffa, bayan Abba yyi parking ya juya yana kallon Heedayah 

da tayi lamo jikin motar, yace “Heedayah” ta xauna da kyau da sauri tace “Abba” murmushi yyi yace “Hope 

ba bacci xa ki yi ba” ta girgixa kai tace “A’a” Ya kalli Mami da ke kallonta ita ma, Mami tayi murmushi tace “Heedayah is more than lazy, tafi son 

tayi ta bacci” Shiru Abba yyi bayan few seconds yyi kasa da murya yace “Look Rahinah… my mother can be very weird at times kin san ynda tsoffi 

suke, I know she will welcome you wholeheartedly but…. Akwai halin tsufa dai, so get prepared Mamin Heedayah and Farida….” murmushi kawai tayi, 

ya bude motar ya fita, ita ma ta fita ta sakko da Heedayah, main parlor Mami ta xauna tana amsa gaisuwan da Yan matan gidan ke mata, Hajiya Hauwa 

dake kitchen ta fito don ganin su waye, ganin Abba tace “Sannu da xuwa barrister” yace “Sannu Hajiya Jiddah ya gidan” tace “Gida Alhmdllh” da 

fara’a tana kallon Mami tace “Sannu da xuwa Hajiya, sannun ku da xuwa” Mami na murmushi tace “Yauwa sannu, fatan mun same ku lafiya” Hajiya Hauwa 

tace “Alhmdllh, you are welcome to the family” murmushi Mami tayi tace “Thank you” Hajiya Hauwa ta tafi dauko ruwa, Abba ya mike ya nufi bangaren 

Mahaifiyarsu, Hajiya Amina ce ta sakko bayan yaranta sun tafi sun kai mata rahotu sama, tun daga step take kallon Mami har ta kusa faduwa, ta shigo 

parlon idonta kyar kan Mami tace “A’a Sannun da xuwa Bakuwa, lale marhaba, sannu amarya” Mami ta kalleta ta gefen ido jin salon maganan nata tace 

“Yauwa sannu” tana fadin haka ta mike tana kallon Hajiya Hauwa da ta ajiye mata ruwa da lemo tace “Hajiya ina ne bangaren mama?” Hajiya Hauwa tace 

“Mu je in raka ki” tana rike da hannun Heedayah ta bi bayan Hajiya Hauwa, Hajiya Amina ta bi ta da kallo har suka shiga parlon kaka sannan ta koma 

sama da sauri. Mami na shiga parlon Kaka ta xauna saman babban darduman dake shimfide tace “Sannu Mama” Kaka dake kallonta tace “Yauwa sannu ‘yar 

nan, sannun ku da xuwa” Mami tayi kasa da kai tace “Ina kwana” Kaka tace “Lafiya qlau, kinga ynxun nan na gama karyawa, yau dai ba laifi sun ga 

daman kawo min karin kumallon da safe, kinsan uwa idan ba taka ba” Murmushi Mami tayi, Abba ya dauke kai daga kallon kaka da yake, Mami tace “To 

Allah ya rufa asiri Mama” Kaka tace “Atoh, Ameen dai, ni da so nayi ma su bar ni in dinga kayana da kaina tunda ina da karamin kitchen amma Amadu 

da wansa Umaru sun ki yarda, Kuma fa idan na ci abincin sae inyi ta tashin xuciya tsabar kazantar Yan gidan….” Ba dai wanda yace ma kaka komai, 

kaka tace “Toh ya sunan naki, kuma yaranki nawa?” Mami ta kalleta tace “Sunana Rahinah, yarana uku” kaka tace “To yaran me ya hanasu xuwa gaisheni 

bayan an riga an xama daya kuma??” Kafin Mami tace komai Abba yyi saurin cewa “Heedayah You didn’t greet grandma” Mami ta daga Heedayah ta maido ta 

kusa da kaka tace “Greet her” a hankali Heedayah tace “Ina kwana” Kaka da ta saki baki tana kallonta tace “To wnn kuma wani irin kaya ne aka sa 

mata kamar ‘yar anna, abu duk a d’angale jama’ah? Rahilah kike ko wa? Gaskiya kar ki sake sa mata wa Innan tsinannun kayan, da da idonta ma baxata 

bari a cuce ta a saka mata wannan kaya ba” Mami na murmushi tace “To in sha Allah baxa a sake ba Mama” Kaka tace “Kuma kar ki sake yi mata karin 

gashi ki rufa mana asiri mu ba hka muke ba” Mami tace “Ae gashinta ne mama” kaka ta cire hulan kan Heedayah tace “Auuu, to maa sha Allah, daga gani 

ba daga irin tsiya ta fito ba, nima dai ance ina kamarta gashina har gadon bayana wllh….” Abba ya mike yace “Baaba xa mu je, ana jirana ne” Kaka 

tace “Ko dai har ta tare bani da labari?” Yace “Aa tukunna” Kaka tace “To sai yaushe?” Abba xai yi magana kaka tace “A’a ni ba ruwana, ita bata da 

baki sae kai, ni da ita nake ba da kai ba ae koh” Mami tayi murmushi tace “Ko nan da sati kaka” Kaka tace “Toh dai kiyi ki tare kafin matar tasa ta 

dawo, kinsan tana d’an tabin hankali, ko da yake dai gadonsu ne, ga shi kuma ya hade da an mata kishiya, ke dai ba ruwanki da ita kiyi ta kanki ki 

kula da marainiya tsakanin ki da Allah, parlon ki na nan tikeke da uwar daka har da bandaki ba ruwanki da fitinanniyar, kitchen kuma ya fi parlon 

nan nawa da kike gani girma, komai kike son xubawa naki ki xuba duk xai cinye wllh….” Abba yace “To bari mu je Baaba” Mami dake ta murmushi kawai 

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button