ZAINABU ABU HAUSA NOVEL

ZAINABU ABU HAUSA NOVEL

Nasir yasamu yaji sauki sosai tunanin wayarshi yafara dakuma saudat yamatsu yakoma gida yadsuko wayarshi gashi momy ba bari zatayi ba.

Acan gidan nasu, saudat takira wayar Nasir gata abude amma ba,a dauka ba ranta inyayi dubu yabaci zama tayi batada aiki se kuka gashi kowane lokaci seta gwada number shi ta ,,tayarda hankalin iyayenta ,,batasan gidan suba hakadai tahakura

Kwanan su Nasir daya a gidan momy suka nufi gida da isarsu Nasir ya wuce part dinshi Zainabu ma ,haka wayarshi yafara dubawa miss calls yagani samada 40zaro ido yayi kana yafara neman number saudat kira daya kamar jira take ta dauka muryarta alamun taci kuka ta gaji ,kana tace mekyau ina kashiga muryar shi me kamada na mara lafiya yace mekyau banida lpy nakusa mutuwa ????nikuwa nace Nasir anji maza..

Shagwabe fuska tayi kana tace dady na yace katuro iyayenka ,yunkurawa yayi dakyar yace ,mekyau nafada miki daga asibiti muke kimin hakuri anjima zankiraki saudat bahaka taso jiba amma tayi hakuri tunda soyaiyyar Nasir tarufe mata ido.

✍️Mom Islam ceee????

ZAINABU ABU
????????????
{Me tagwayen suna.}

 ????????????

STORY &WRITING BY ZAINAB HABIB {MOM ISLAM .}


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com

BISIMILLAHEER RAHMANIR RAHEEM.

DOCTOR ALLAH YABAKI LADA

MAMAN USWAD Allah YARAYA ZURI,A

PAGE 19

_______Nasir yaji sauki sosai,harya fara zuwa aiki. Saudat ce tama tsamai akan ya turo iyayenshi, yau dai ya gaji yayi mata alkawarin inya tashi daga gurin aiki ze wuce ta gidansu. Bayan yamma tayi misalin karfe 8:pm, gidan su ya zarce sunata hira da iyayenshi harda dady, momy ce ta miƙe ta fita Nasir ne ya kuma matsawa kusa da mahaifinshi kana ya ce “Dady please ka fahimce ni dan Allah ” dadyn besan inda Nasir ya nufa ba, ya ce kayi min bayani ban fahimci me kake cewa ba .

Nasir ne yace ” dady aure nake son yi.” Nasir seda ya tsorata ganin yanayin dady amma daga ƙarshe dady yace ba komai, Allah yasa hakan shi yafi zama alkairi murna fal zuciyar Nasir. Momy ce ta shigo, dady ya ce ” zo kiji abinda ɗanki yazo dashi, Nasir ne ya sunkuyar da kanshi kana momy ta kasa kunne tana saurarar dady, cewa tayi “ina jinka alhaji.”

Magana ya fara “ɗanki ne yazo min da maganar karin aure.” Momy ce take jin abin kamar a wasa ta ce “bangane ba, kana nufin wai aure zekara? To indai ya ƙara zuwa da makamanciyar wannan maganar ban yafe….”

Dady ya rufe bakin momy kana ya ce ” gaskiya ba zamu takura mai ba ,yanada damar auran mata huɗu mutukar zeyi adalci a tsakaninsu.”

Momy ce hawaye na zuba a idanunta kana ta ce “;auran nashi wata biyu, wannan abin kunya har ina?. Son zuciya kenan.”

Dady ne ya ce shifa ba wai yana nufin baya son Zainab bane, a’a kawai dai yana son ƙara auranne. Momy ta fahimci dady yana goyon bayan Nasir, hakan yasa ta ja da baya tasan indai dady ya faɗi magana to babu sauyi ,jiri ne ke dibar ta, bango ta dafa ta nufi bedroom ɗinta kwanciya tayi akan gadonta ,tana tunanin marainiyar Allah.

Bayan tafiyar ta dady ya kalli Nasir ya ce “yanzu se:me ya rage?”

Nasir ne ya ɗago da kansa kana ya ce “dama iyayenta ne suka ce in turo iyayena”

Dadyne ya ce “karka damu zuwa yaushe zamu je?”

Nasir ne ya ce ” gaskiya basu faɗa ba.”

Dady ya ce ” to kace musu jibi zamu zo insha Allah” duk wanda yaga dady yasan ƙarfin hali kawai yake yi .

A yau ne dady suka shirya shida wani amininshi zuwa gidan iyayen Saudat anyi musu tarba ta arziki sun tattauna saboda sun san juna sosai, dadyn Saudat da sauran yan uwanshi suka ce ai yabkamata ayi mai gaba ɗaya a wuce gurin, dukiyar aure aka yanke musu dubu dari haɗi da kuɗin gaisuwa, da ganan suka wuce gida. Tunda aka yi wannan maganar ta auran Nasir, momy ta rage kulawar da take bawa dady shima dadyn ya fahimci hakan be nuna mata shima ƙarfin hali yake yi ba.

Zainabu duk wannan hidimar da ake yi bata da labari, sedai tunda Nasir yaji sauki ya koma inda yake a da dama bata damu da kulashi ba shi yasa ta daina sawa kanta damuwa in kaganta bazakace tana da matsala ba saboda tayi kiba gashi takuma ƙara kyau .

Akwatuna taga anata shigowa dasu cikin gidan bata tsaya kallon suba ɗakinta ta wuce, ta ɗauki wayarta tana chart, Nasir ne ya kwala mata kira daga kafada tayi alamar ko ajikinta kana tace “inka matsu kazo ko menene yau kuma kake nemana oho? “

A fusace ya shigo ɗakin yana faɗin ” ina ta kiranki dan baki da kunya shine kaki amsawa ko?”

Hararshi tayi kana ta ce “gani mezan yi maka?” ɗaurewa yayi kana ya ce ” kizo Palo ina jiranki” bata kawo komai a ranta ba ta miƙe tabi bayanshi akwatuna ta gani set goma sekuma biyar a gefe. Nuni yayi mata da biyar ɗin yace “ga akwatunan ki nan”

Bata fahimci me yake nufi ba ta ce ” bangane me kake faɗa ba”

Tsawa ya daka mata kana yace ” aure zanyi to, kinga akwatin amarya kinga naki.” kyalkyalewa da dariya tayi kana tace “cewa zaka yi yar uwa zaka samo min, kai wlh nayi farin ciki dama na gaji da zaman kaɗaita”

Nasir abinna Zainabu ya bashi mamaki yaji ance mata na da kishi, to shi yaga Zainabu bata nuna komai ba, kenan ita kuwa tanabta murna ze ɗauki akwatunan, ta ce “ka barshi zan dauka, ai kayi me wuyar” diban ta fara yi daƙyar take ɗauka tana tafiya tana murna. Nasir ne ya dibi sauran ya wuce dasu gidan momy.

Tunda yavshiga gidan yaketa kwada sallama amma babu wanda ya amsa se yar aikin gidan da take kaiwa da komowa ya tambayeta ina momy?. Durkusawa tayi kana tace “tana ɗakinta kiran wayar ya shiga yi amma ba’a ɗauka ba, momy tana jin shigowar Nasir taki fitowa.

Kai tsaye hanyar ɗakin ya nufa kana yayi sallama. Momy ce ta amsa, durkusawa yayi ya gaisheta, fuska babu walwala ta amsa kana tace ” me kazo yi min ka ficemin daga ɗaki bana son ganinka.”

Nasir ne yayi kamar ze fashe da kuka yace “momy ki yafe min dan Allah, akwatuna na kawo kizo ki gani.” Momy kuwa tashi tayi tai ficewar ta.

Mom Islam cee✍️

ZAINABU ABU
????????????
{Metagwayen suna.}

 ????????????

STORY &WRITING BY ZAINAB HABIB {MOM ISLAM .}


AREWA WRITER’S ASSOCIATION


????{Arewa ginshiƙin al’ummah}????


https://www.facebook.com/104534761033461/postsarewawritersassociation@gmail.com
https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.

BISIMILLAHEER RAHMANIR RAHEEM.

DOCTOR ALLAH YABAKI LADA

MAMAN USWAD Allah YARAYA ZURI,A

PAGE 20

_______momyn ficewa tayi ,Nasir ne yatashi jiki babu kwari yanufi hanyar fita,megadi yasa ‘yakwaso kayayyakin yashigo dasu yagama zamanshi momy bata dawo ba dole yatashi yanufi mota ,jiyakeyi duniyar tayimai kunci ga sayayyar saudat ,data rufe mai ido tuki yakeyi amma hankalin,shi a tashe ikon Allah ne yakaishi gida besami Zainabu a Palo ba kai,tsaye dakinshi yanufa kwanciya yayi a Bed dinshi kana yashiga sabon tuna ni .

Ansa ranar bikin Nasir ,basa,son bikin yadauki lokaci sati uku 3weeks akasa murna gurin saudat ba,acewa komai tafi angon zumudi shirye shirye sukeyi amma duk wanan hidimar Nasir beta ‘ba fadawa saudat yanada aure ba saboda bedauki auran na Zainabu wani abu,ba .

Zainabu dukda tasan aure Nasir zeyi amma bata d`aga hankalin taba ,tana zaune tana kwaliya taji wayarta na ringing duba mekiran tayi momy tagani dasauri tadauka,tace Aslamu Alaikum,,momy yakike momy ce tace Zainab kina lpy “lpy Lou momy naji muryarki ta sauya ne Allah yasa lpy karfin hali momy tayi kana tace Zainab lpy nake gobe kizo gidanmu kid’an di’bo kayanki Zainabu hankali a tashe tace. Momy ko intaho yanzu a,a momy tace mata sukayi sallama tanufi kitchen taliya tadora me kifi da kayan lammbu bayan tagama girkin ta dibo a plet tanufi dakinta yunwace ta ,tayarda Nasir gashi tunda yatashi yaji gidan ya game da kamshin girki, kitchen yanufa yahau bude tukwane tukunyar da Zainabu tadafa taliya yabude babu komai aciki saboda iya cikinta ta dafa dakinta yanufa yasamu tanacin abinci hankalinta a kwance batada damuwa ka’rasawa yayi kusada inda takecin abincin ko kulashi batayi,ba sa sauta murya ,yayi kana yace haba zeey kinbar mijinki najin yunwa kinyi adalci kenan .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Leave a Reply

Back to top button