A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Wani yammaci ne, Bahijji tafito domin shak’atawa a nan harabar gidan,
Zama tayi akan kujera, tana karatun mujalla, saitajiyo k’amshin turaren Fahad a bayanta,
Juyawarda zatayi sai ta ganshi ya tsura mata ido ita kawai yake kallo,

Ganin da tayimasa yana kallonta yasanyata jin kunya, ta sunkuyarda kanta k’asa

Shikuwa ya zagayo inda yake fuskantarta, yace, “gimbiya barka da hutuwa sarauniyar mata.

Kunyace ta lunlubeta ta rufe fuskarta da jaridar dake hanunta tace ” yawwah yarima Allah ya taimakeka ya kuma tsare mana lafiyarka.

Murmushin jin dad’i yayi, yasamu d’aya daga cikin kojeran ya zauna, suna fuskantar junansu,

Yace “gimbiya Bahijja kinkosan abunda ke tafe dani a daidai wannan lokacin?”

Tayi murmushi tace, ” ranka ya dad’e bansaniba, amma kunnuwana, saurarenka suke, suna jiran suji abunda zaifito daga daga bakinka,

Yayi gyaran murya, yace “Bahijja tun lokacinda nasanya idona a kanki naji nakamu da soyayyarki. a kullum dake nake kwana dake nake tashi a rywatah,
Bahijja kitaimakamun ki karb’i soyayyata, idon kikayimun hkan zanji dad’i a rayuwata.”

Magana yakeyi kanta a sunkuye yake, duk kunya takamata musamman dayace sonta yakeyi,

Ganin tak’i kulashi, yasanyashi sauka daga kan kujerar dayake zaune, ya runsuna k’asa ya tallabo fuskanta da tafin hannunsa, ya tsura mata ido, cikin shauk’in so da k’auna. “Bahijja magana nakeyi amma kink’i kulani, kodai bakya sona ne?”

Kasa had’a ido tayi dashi, sai dai ta kuma sunkuyar da kanta k’asa, tana maijin kunya.

Yace “Bahijja ki amsa mun maganata koda zanji sanyi a rayuwata.

Rufe fuska tayi da tafin hannunta,
Yin hkan datayi saida abun yabashi dariya.

Yace “yanda kike tafiyarda da rayuwarki, Bahijja kike k’ara burgeni, nakejin sonki a rayuwata, Bahijja ilove you.
Ki taimakamun kice mun I love you, yin hkan shizainuna mun nasamu karb’uwa a rayuwarki.

Mik’ewa tayi tsaye, rufe da fuska, tace “
Fahad I love you, I really luv u ,
Tana kai nan taruga a guje tabar wurin

Murmushin jindad’i yabitadashi, tak’ara shiga ransa domin yanason mace mai alkunya.

A hka dai soyayya mai k’arfi tashiga tsakanin yarima Fahad da gimbiya Bahijja.”

A b’angaren prince Adnan kuwa, bayan kwana biyu dayin mgnarsa da Abdullah, saiga Abdullah yakira shi a waya, yake shedamasa dacewa ya binciko masa ko wacece Bilkisu,
Murna yashigayi sukace sai sun had’u a makaranta sauran bayani

A gurguje yashirya domin tafiya makaranta, sauri yakeyi domin yasamu abdullah yafad’a masa wace Bilkisu?”

A makarantar yasame Abdullah a tsaye yana jiransa, k’arasowa yayi a kusa dashi suka tab’a suna kiran sai maxaje,

Prince yace to ya Abdull bani labarin ‘yar matsiyatar nan,
Abdullah yace “wai kasan ko d’iyar waye?”
Prince yace “ina zansani saika fad’a
Abdullah yace to bad’iyar kowa bace face d’iyar matsiyata, kuma talakawa ne, nabugawa a jarida???? don ance ubnta yama mutu, basuda kuwa,daga ita sai uwarta suke zaune a gidansu,
Don hka nake baka shawarar kadaina wahalarda kanka a kan ‘yar matsiyata, kafita daga harkanta kashareta kawai, tunda kafahimci ita bakowa bace,

Prince yayi dariyar mugunta, yace gud story naji dad’in wannan labari Abdullahi.kafin narabu da ita saina nunamata kuskuranta, kuma sai nunamata yanda xata dinga girmama shuwa gabanni, musamman sarakuna, da kuma ‘ya’yan sarakunan.”

UMMU SAFWAN
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR…

????????????????????????????????????????

writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

Page 1⃣7⃣

Gudu yake kamar Zaitashi sama, sai tunanin marin da Bilkisu tayimasa a gaban bainar jama’a

kaiwa sitiyari mota duka yayi ya burxarda da wani iska mai zafi a bakinsa, idanunsa sunkad’e sunyi jajir. Sai gudu yake zubawa a kan titi, ganin gudun dayake ba’a hankanlinsa yakeyinsaba yasanya
Abdullah yayi k’arfin halin yimasa magaba, “don Allah prince katafi a hankali mana, kadiba ga yanda jini yake zuba a k’afarka, duk kawani fita hanyacinka akan wannan matsiyaciyar yarinyar, wai ynxun ina muka nufa ne kabiyo ta wannan hanyar.”?

Betankawa Abdullah ba, sai gudu yake shararawa, Abdullah duk ya tsorata da ganinsa cikin wannan halin.

Sai ganin yayi.
yayi parking a dai dai k’ofar gidansu Bilkisu, waya yad’aga yakira fadawansa, yayi masu kwatancen a inda yake suzo susamesa.

Ya mayarda kallonsa ga Abdullah yace, “yau zannuna mata na i’sa nakoresu a garin nan,kora ta wulak’anci, kuma zan a zabtar dasu har saitayi nadamar marina datayi a gaban bainar jama’a,
Itama zan wulak’antata kamar yanda tayimun a gaban bainar jama’a.

Yana rufe bakinsa saiga fadawa sun iso kowanesu jira yake abashi umurni.
Runsunawa sukayi suna kwasar gaisuwa, kallo yabisu dashi d’aya bayan d’aya, yayi masu nuni da gidansu Bilkisu,
Yace “kushiga gidan nan kufitomun da duk wani abu dake cikin gidan nan, tareda bil adaman dake rywa acikinsa, duk a fitomun dasu yanxun nan.”

Fadawa suka afka gidan, suka tararda jakadiya zaune tana yankan a aifa, sai ganin fadawa tayi gabanta, kallonsu tashigayi cike da mamaki, ita dai tasan ba fadawan masarautarsu bane, tomeye had’insu da wad’an nan fadawan? Tashiga yiwa kanta tambayoyi. Saiji tayi anwatso mata a kwatin kayansu a k’afa, cike da mamaki take kallonsu tana fad’in “lfy”? Meyafaru”? Me mukayumaku”? Basu saurare taba sukaci gaba watso masu kayansu a waje.”

Bilkisu kuwa na makaranta, batasan abunda ke faruwaba. Kuka takeyi, safeenat sai hakuri take bata, gameda abunda prince yayi mata.
Mekewa tayi tsaye cikin yanayin damuwa tace sis zantafi gida kaina ke yimun ciyo, bazan samu damaryin test d’in nanba domin kona tsaya bazan iya rubuta komaiba.

Safeenat tace “sis Allah ya sauwak’e, idon kikaje gida kisha magani. Ynxun da munfito gani nan zuwa naga jikin naki.

Bilkisu tace “to sis ngd saikin shigo.”
Tawuce tatari mai adai2 sahu yakaita gida.
da shigarsu kwanar unguwarsu ta hango mutane, sunyi cincirundo a k’ofar gidansu mamaki tashigayi tana tambayar kanta lfy”? Taka mutane haka a k’ofar gidansu?

K’arasawa tayi domin ganin me kefaruwa, sai ganin kayansu tayi anawatso masu a kofar gida,
Jakadiya sai kuka takeyi tanabada hakuri amma basu saura ra mataba,

Bilkisu nazuwa wurin gaba d’aya kallo yadawo Kanta, ganin fadawan prince tabawa kanta amsar wadda yasanya suyimasu irin wnn wulak’ancin, batabi takan kowaba sai wurin jakadiya tanufa dake durkoshe tanabawa fadawa hakuri,
Durkusawa tayi tad’ago jakadiya tsaye tace “Ammi meye abunbasu hakuri a ciki? Ki kyalesu kawai suyi abunda sukeso.
Tana mgna amma idanunta sun cika da hawayen bak’in ciki.
Yau ita gimbiya Bilkisu itace ake wulak’antawa a gaban bainar jama’a????
Tana rungume da jakadiya suna kuka.”

sai tab’i taji anayi a bayanta, juyawarda zatayi ganin prince tayi tareda Abdullah sunayimata dariyar k’eta.

Kallo tabisu dashi sama da k’asa,
Prince yace ” ni nasanya a yimaku hakan, domin bana muradin ganinku a k’asata, bakeba ko mai kama dake nagani saina sanya ankoreta a garin nan, bareke. Na tsaneki banason ganin fuskarki bare mai kama da fuskarki.

Kallon tsana tabisa dashi, tana mai zubarda hawaye, tace “banada niyar mugunta amma kaine mutum na farko da zansanya a axabtar dashi a zaba mai tsanani,
banada niyar amfani da damata domin wata manufa marasa kyau, amma Kaine mutum na farko dazaka sanyani yin hkan,
Kasani na tsaneka tsanawa mai tsanani. Ka wulak’antamu a gaban bainar jama’a kaima ka saurare naka hukunci gobe.
Tana kaiwa nan Safeenat tafito cikin a dai dai sahu, ganin Prince tsaye tabawa kanta amsar tambayar dazatayi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33Next page

Leave a Reply

Back to top button