A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Ahankali tamike ta isa wajen tatsaya, a tsakiyar filin, ido yayo kanta kowa kallonta yakeyi,
Sannan M.C yacigaba da magana,
Yace “muna da sharadin duk wadda yafito Wurin nan to munsan tabbas ya yarda da kansa,

don haka munada sharad’i?

      Sharadin shine duk abunda akkace mutum yayi saiyayi ko kuma acishi tarar (70, 000 N) 
          Ya maida kallonsa a Bilkisu   Yace "gimbiya kinyarda,?

Ta maida kallota ga safeenat,
Safeenat tad’aga mata kai alamar tace ta yarda,
Bilkisu ta kalli mc tace “nayar da Dan kudi bama tsalata bane, nan fa aka d’auki kuwa,

yace
sharadi na biyu, programs nafarko dole sai kinyi abunda akkace kiyi, idan bakiyiba zaki biya Tara,
Ko kuma a fansheki, ma’ana kuma wani daga cikin masoyanki subiya maki,

 Tana tsaye ankabawa safeenat wani farin kyalle,

akkace ta daure mata fusaka da farin kyallen,

Ya kuma bada umurni akkan cewa duk namijin da yafito tsakar fili,
yacire ta kalmensa ya ajiye a kusa da ita,

bayan sun kammala ajiyewar,

Sai MC ya kalli Bilkisu dake tsaye d’aure da fuska,
Yabata umurni dataduk’ ta d’auki talkami d’aya cikin tallakamin da aka ajiywmata a gefenta,

Nanfa tashiga gewaye tana lalaben inda talkaman suke,
can ta canki wani takalme,
tamik’awa MC sannan aka bude mata fuskarta,

                  MC yashiga diban k'afafun mutanen dake tsaye tsakar filin dan ganin ko takallemen waye ta cinka,      Nan aka kasoma dibon k'afa ashe na yarima adnan ne tadauka, aikuwa mutane na fahimtar hakan suka suma  kuwa, 

    M.C yayi gyaran murya yace, "Bilkisu da Adnan kawai yakeso ya gani a tsakar filin,

Zaharaddin yyi bak’in cikin rashin d’aukar takalmensa dabatayiba

MC yace a saurara, za’a sanyawa Bilkisu da Adnan wak’a domin sutaka rawa,

Adnan yaji dad’in hakan,
Ita kuma tad’auki niyar cewa Adnan bazai tab’a kada itaba,

bata iya rawaba amma takawa takeyi cikeda k’asaita saida ta tabawa kowa sha’awa amma banda zaharaddinka,

Sai programs na k’arshe,

     M.C yace anason Adnan yayiwa Bilkisu kiss harna tsayin 30minut,

nanfa hall yayi tsit don kowa sonyakai yaga yanda hakan zata kasance

adnan yyi murmushin jin dad’i,
Yasoma lasar baki da gyaram kwalar Rigarsa za,asha banza,

Adnan yasoma matso Bilkisu naja baya, MC yace “wait Prince bara nak’irga goma idan bata yardaba zamu cita tara,
idan kuma akwai mai fan sarta toh am waiting, nanfa yafara k’irga d’aya Bilkisu naja baya prince nabiye da ita har da ta kai karshen bango, Prince nabiye da ita,

          Datagade ba sarki sai Allah sai tayi tsaye, ta kulle idonta tana jiran taji saka mako abunda prince zaimata,

Shi kuma har yaruk’o hannunta, yaji ance na nafansheta, nan take prince yayi saurin waigowa domin ganin waye ya katse masajin dad’i, sai yayi arba da Zaharaddin a tsaye yana murmushi, nanfa yaji kamar yamutu amma sai ya yamutsa fuska alamun ko ajikinsa

Amma taciki naciki nan dai akaci gaba da programs daga bisani aka tashi kowa yawatse.

              safeenat ce takeyiwa  Bilkisu dariya tana fad'in "yau wata datasha lebo, 
  Bade ta kulataba sai harara databita da ita, tareda fad'in  " Allah yafishi,

safeenat tace bawani anaso ana kaiwa kasuwa, ai koke bakiji dadiba itade batace mata uffanba

  Suna fitowa Zaharaddin yabiyo bayan bilkisu suna tsaye yanamata k'orafi akan cewa danmi bata dau takalmensaba?"

Magana yaji anayi a bayansa yaji anafad’in “akanmi zata d’auki takalmenka tabar na mijinta?’

Nan suka juya gaba d’ayansu dan ganin mai yin magana,

Zaharandin ya kallesa yace ‘toh kai kuma miye naka nabiyomu a Nan Adnan?”

Prince yayi murmushi yace “nabiyoka ne domin inyimaka kashedi a kan karabu da Bilkisu domin nikad’ai nakeda ita, banason inason abu naga wani na Sonsa, Dan haka kakiyayi kanka,
ko nasanya a b’atar min da kai, b’acewa ta har abada,

Domin kadaina ganin kanka wai d’an minister ne,
kod’anda shugaban k’asane kai zan iya sanyawa a b’atarmun da kai.

Bilkisu tayiwa prince kallon sama da k’asa “tace kai malam yimun shiru,
wacece matarka?’
Allah yatsareni danazama matarka,
Tanuna xaharandin tace, “kaga wannan shine mijina,
Wanda ya amsheni a hannun azzalumi irinka,

         Tun Kamin ta iyar da maganarda takeyi saiji tayi an watsamata mari,

Ta dafe kunci
Tace “kamareni?” akan nace bana sonka?” toh nafad’a nace bana Sonka Adnan,

shikuma abunda yatsana a rayuwarsa kenan ta duniya,
bilkisu tace bata sonsa.

Nan Yadinga kallonta idonsa yarik’ed’e yayi jajir,
ya hango shatin hannusa,
a inda yamareta ya kwanta mata akan kyakkyawar fuskarta,

Ta kuma kallonsa ido cike da hawayeTace “nace bana sonka zata kuma yin magana yad’aga mata hannu alamar tayishuru yajuya zaitafi idanunsa surikid’e, sunyi jajir sai zubar da hawaye yakeyi,
Zai wuce kenan saiganin sukayi ya yanke jiki ya fad’i k’asa a some,
nan take Abdullah yayo Kansa suka tallabesa aka sanyashi a mota suka nufi asibiti dashi,

Hankalin Bilkisu duk yatashi sai zubarda hawaye takeyi,

zaharaddin yace akan wannan jakin zaki tada hankalinki?”
yama mutu mana,
shiyasa lokacin dayayi hadari naso yamutu,

kenifa saboda kiyayyar da nake masa yasan, natura akad’eshi a mota mufuta, Domin tun farko bana sonsa,

 Bilkisu  tabishi dawani    kallo wadda saida ya firgitashi,  sannan ta d'aga masa hannu tace 

Ya i’sa zaharandin, dama kai azzalumine maci amana?”
Ashe zaka iya kashe rayuwa?”
kuma d’an uwana?”, toh bara kaji daga yau kada ka kuma yimun magana natsaneka, bana sonka banason ganinka azzalumi kawai, nan ta tohfa masa yawu tawuce.

          Koda aka i'sa asibitin prince besan inda kansa yakeba,

Likitoci tai makon gaggawa suka basa,sannan akakira sarki yazo han kalinsa a tashe yashigo asibitin,yana tambayar ba,asin abunda ke faruwa ga prince, nan sunkace suma basu saniba gani kawai sukayi ankawosa,

Nan likita yayi sarki magana, akan cewa yana son ganinsa, suna shiga yafayiwa sarki bayani kamar haka,
“zuciyar Adnan ce yake keson bugawa saka makon wani abu dayake so baisameshiba Don haka ayi saurin basa abunda yakeso, idan bahaka ba, zai iya rasa rayuwa.

Sarki natsaye yana saurarem likita, yana yimasa bayani, gaba d’aya hankalinsa baya jikinsa saboda tashin hankali,
Marmartaba yayi lilita godiya yafito, cike da mamakin meye prince yakeso hkan Wanda besamuba haryake neman narasa rayuwarsa,

Bilkisu kuwa gaba d’aya hankalinta yatashi da ganin fad’owar da prince yayi
Aguje tashiga napep tabi motarsu prince a baya, sai kukatayi tana mai tausaya masa halinda yashiga a kanta,

A harabar asibitin me napep d’in ya ajiyeta,
Aguje tak’arasa d’akinda aka kwantarda prince d’in, tura k’ofa tayi tashiga.”

✍????writing by
Ummu
safwan✍????
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR….

????????????????????????????????????

  Writing by
     Ummu
       Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

page 5⃣1⃣ 5⃣2⃣

Hango Prince tayi a kwance cikin mawuyacin halin, sai wani numfashi yake fitarwa, kamar ransa zaifita,

Kuka tafashe dashi, tanufi gadonsa,
Cikin yanayi mai bantausayi,
Ta durk’usa dai dai gadonsa, tana kuka,
Ta rikomasa hannu taga baya motsi,
Ta kurma I’hu, wadda yaja hankalin likita tareda maimartaba sukayi saurin shugowa d’akin, suka tararda ita sai girgiza prince take tana kuka, tana fad’in

“Dan Allah Adnan karka mutu wlh inasonka,
Katashi a d’aura mana aure, nadad’eda fahimtar kyakyawar niyarka a kaina, inasonka Adnan kai kad’ai nakeso,pls Adnan katashi karka mutu kabbarni,

Adnan dake kwance cikin mawuyacin hali, wanda ko iya motsi bayayi,

Yanajin sautin kukan Bilkisu nayimasa yawo a kannen,
Bud’e idonsa yayi, ya d’aga hannunsa ya rik’o hannun Bilkisu ya rik’esa gam,
Yanda bazata kuncemasa ba,
Ya mayarda idonsa ya rufe, hawaye na zubar masa a gefin fuskarsa,

Bilkisu Tashiga share masa hawaye a fuskarsa,
Tana fad’in pls Adnan karka mutu kabarni wlh inasonka,
Karka mutu kabarnu sai munyi aure mun hayayyafa,

Likita da Maimartaba sai kallon mamaki suka bisu dashi,
Fahad da Bahijja ne suka turo k’ofa suka shigo,
Suka tarar da Bilkisu a kusa da Adnan sai share masa hawaye takeyi itama tana kuka,
Kuma idonsa a rufe, amma hannunsa rik’e da hannun Bilkisu, kamar Wanda za’a kwace masa ita a gudu,

Fahad yakai dibansa ga maimartaba yace
“Abba me likita yafad’a gameda abunda kedamun Adanan?”

Abba ya maida kallonsa ga Fahad yace ” doctor cewa yayi,
Zuciyarsa zata iya bugawa, har yakaida rasa Rayuwarsa idan ba’abashi abunda yakesoba,

Maimartaba ya dafa Fahad, cikin yanayin bantausayi,
Yace Fahad nayi mamakin maganarda likita yafad’amun a kam Adnan,
Nidai a iya sanina Ku uku ne Allah ya mallakamun a rayuwata a matsayin ‘ya’yanah,
duk daga cikinku bbu wadda yatab’ata Neman wani abu najin dad’in duniya yarasa a wurina,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33Next page

Leave a Reply

Back to top button