A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Writing by
Fareeda
Bashir✍????
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR……

????????????????????????????????????????

     writing by
          Ummu
             Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

Page 3⃣2⃣ 3⃣3⃣

A haka suka cikagaba da zama da prince a makaranta babu be kula wani daga cikinsu,
Abu d’aya yake damunta dashi a kullum idan suka had’u sai yayi mata wani kallo nasama da k’asa sannan yacije baki yayi tafiyarsa, abun yana bata mamaki amma bata kulashi.”

Seefana tace “sister naga mutumin naki kwana biyu nan ya daina kulaki?” Kodai yaga baya iyawa da fitinarki ne?” Domin kema idan yayimaki bakyaleshi zakiyiba,

Bilkisu tayi dariya tace ” nasan bazai barniba domin inaji a rayuwata da kwai abunda yake shiryawa, domin nasan halin Adnan sarai baya barin bashi,

Wayar da kecikin jaka ta d’auki ruri, ita takatse masu maganar da sukeyi da safeenat,
Sauri bud’e jakarta tayi domin tasan Abbantane ke kiranta domin ringing d’insa daban ne tasanya masa,
Takara wayar a kunnenta tare dayin sallama ta gaidashi cikin fara’a dajin dad’i,
Abba shima cike da farin ciki yake amsa gaisuwa gimbiya Bilkisu,

Bayan sunk’are gaisawar Abba yake shaida mata da tashigo mota gobe yana son ganinta akwai maganar da yakeso yayi da ita,

Bilkisu tayi mamaki sosai take tambayarsa Abba lafiya kuwa?”
Ina Ammi nah take?”

Yayi murmushi yace “Ammi ki lafiyarta k’alau gata a kusani, taja wani dogon ajiyar zuciya,
Tace Abba bata wayar mu gaisa naji muryanya,

Abba yamikawa Ammi waya suka gaisa, sannan zuciyar Bilkisu tayimata sanyi,
Tace “insha Allah gobe zamuyi asubanci mutafo tareda fadawa gaba d’aya,

Abba yace “yawwa gimbiya Allah yayi maki albarka, yakawoki lafiya, tace “Amin Abbana sukayi sallama,
Bayan ta k’are waya da Abbanta,
takira fadawa take shaida masu gobe su zama cikin shiri yola zasu tafi, kuma tafiyar safe take buk’ata suyi, su tabbatar da sunwake motocin da zasuyi tafiyar dasu,
Suka amsa mata da angama ranki ya dad’e,
Takashe wayarta tasanya a jaka,

Takai dibanta ga Safeenat tace “sister gobe fa yola zantafi Abba yana nemana amma ina ganin kwana d’aya zanyi saboda munkusan fara jarabawa,
Safeenat tace “sister Allah yakaiku lafiya ya kuma dawo dake lafiya,
Bilkisu ta amsa da “Amin.”

Ashe duk maganar da sukeyi a kan kunnen Abdullah da yazo giftawa ta wurin yaji Bilkisu na waya, tana fad’in to Abba insha Allahu gobe da sansafe zamuyi asubanci mutafo tare da fadawa.”

Ai kuwa Abdullah yaja gefe d’aya ya tsaya inda bata iya ganinsa saida ta kammala wayar,
Har maganar da sukayi da Safeenat duk a kan kunnensa, ya fahimci gobe yola zata tafi kenan?”
Aikuwa yashiga jin dad’i domin bazai yarda ba dashi za’atafi baza’a barshi garin Kano ba,

Juyawa yayi ta bayanta yayi tafiyarsa gida yashiga harhad’a kayansa gobe sai yola, domin ba zai yardaba k’afarsa k’afar fadawa ko a but ne ya amince a sanyashi a tafi dashi yola,

Wasa wasa Abdullah beyi barciba Allah Allah yake safiya ta waye masa yagansa a mota sunmik’i hanyar yola,.

Dakyar yasamu asuba tayimasa tun kafin mahaifinsa ya fito zuwa masallaci Abdullah yarigashi fitowa rataye da jakar kayansa yayi saurin bud’e gida yanufi masaukin fadawa,

Yana isa k’ofar gidan ya tarar da motoci Jere har basa k’irguwa, sunbi layi alamar ba’a jima da gama wankesu ba,

Yakai dibunsa a gaba d’aya motocin saida gabansa yafad’i,
A zuciyarsa kuma yace “Alhamdulillah Ashe inada Rabin zuwa masarautar su Bilkisu,

Yadiba gabas da gamma gudu da arewa bega alamar mutum ko d’aya ba,
Ya fahimci cewa suna masallaci sallah sukeyi,
A can ya hango wata mota rab’e gefe d’aya ya rataya jakar kayansa yanufi motar yayi tsaye, ya kai dibansa a cikin motar yahango rubar ruwan faro,
Yabud’e murfin motar ya d’auko robar ruwan yayi arwala ya tayarda sallah a bakin motar, domin da zarar yashiga masallaci to kafin yafito suna iya tafiyarsu subarsa,

Bayan ya k’are sallah ya bud’e murfin motar yayi shigewarsa gidan baya rungume da jakar kayansa,
ya d’au minti biyar a motar, saiyaji zafi yayi masa yawa, yashiga zuge glass d’in motar domin iska yashigo masa,

Aikuwa anan take sanyin asuba mai had’e da iska mai dad’i yashiga ratsashi, dama besamuyin barci jiyaba,
Abdullah yasaki baki da hanci sai kwasar barci yakeyi rungume da jakar kayansa.”????

Gimbiya Bilkisu ta shaidawa fadawa cewa da zarar sun kammala sallar asuba zasu wuce,
Haka kuwa suna k’are sallah kowannesu ya shiga motarsa suka nufi gidan Bilkisu domin d’aukarta suwuce.
Koda suka isa gidan Bilkisu tareda jakadiya har sun kammala shirinsu tsaf suka fito sukashiga mota suka d’au hanyar.”

Abdullah nacan cikin motar mutane yasaki Baki da hanci sai kwasar barci yake harda yawun barci????

Saiji yayi ankwankwasa murfin motar a zabure ya farka cikin gigin barci yake fad’in ankawo yolar?”????????

Bud’e idonsa da zaiyi yayi arba da wani k’aton soja bak’i sed’ik dashi dawani k’aton ciki idanunsa jajir,sai wani huci yake, ya kai dibansa ga Abdullah yace “ubanwaye yashigo dakai cikin motanah?”

Abdullah sai da cikinsa ya d’uri ruwa, yafito cikin motar ya maida idonsa a k’ofar gidansu fadawan yaga bbu motocin da yagani d’azun har sunyi tafiyarsu yola kenan, yad’ora hannu a kai ya kurma ihu,
Soja narik’e da kwalar rigarsa yana cewa “yakama b’arawo cire belt d’in wandonsa yayi yana neman zugawa Abdullahi shi, Abdullah saibada hakuri yake gashi bayada wuyar sakin fitsari,
Aikuwa soja na d’aga belt daniyar zugawa Abdullah, sai ga fitsari yadinga zuba a wandonsa???? yarik’e belt d’in, mutane ne suka zagayesu suna tambayar abunda ke faruwa aikuwa Abdullah yanasamun sa’ar soja ya gantsaramasa cizo a hannu soja yakwatsa ihu, yasaki Abdullah ya yana diban hannunsa,
Shikuwa Abdullah ya zuba da gudu yabar jakar kayansa a motar soja????

           Writing by
               Fareeda 
                   Bashir✍????

????????????????????????????????????????

A WATA MASAUTAR…..

????????????????????????????????????????

     Writing by
         Ummu 
            Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

Page 3⃣3⃣ 3⃣4⃣

Dedicated to my lovely sister NA’IFA YAHAYA Allah yasauki lafiya mutafo garin Kano mukwashi shoki????????????????????

Gudu yake akan titi yana motsa jininsa,
Dama haka al’adarsa take, dazar yayi sallar asuba tunkafin safiya tawaye, kafin mutune sufara firtuwa,
Prince yake gudun a kan titi domin motsa jininsa,

Yauma hakan takasance gudu yake a kan titin, saiji yayi mota ta bangajeshi, tayi sama dashi ta yafar akan titi,
Tundaga lokacin Be kuma sanin inda kansa yakeba,

Mai motar kuwa Yakama gabansa yayi tafiyarsa, yabar prince kwance cikin jini kota ina zubar masa yakeyi,

Gimbiya Bilkisu tareda fadawanta a kan hanyarsu ta barin gari,

Sun iso daidai wurin da abun yafaru,
Ganin mutane sunyi cincirindo a tsaitsaiye yasa ta kai dibanta a wurin taga mutane sun tsaitsaya alamar wani abun suke kallo,

Tayi saurin d’agawa fadawa hannu alamar su tsaya.”
tabasu umurni sufita suga meke faruwa?” taga mutane tsaitsaiye a kan titi?”

Wasu daga cikin fadawan suka fito, suka nufi wurin da abunyafaru,
sukaga mutum a kwance cikin jini, anrasa mai taimakamasa.”

Sukayi saurin nufo Bilkisu dake cikin mota a zaune, suna shaida mata, da cewa
Hatsarine ne yafaru ranki ya dad’e, wadda kuma abun yafaru a kansa yana buk’atar taimakon gangawa domin duk mutanen dake wurin tsoron tab’asa suke.

Tayi saurin bud’e murfin mota tafito, tana bada umurni da a d’aukeshi a nufi asibity dashi,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33Next page

Leave a Reply

Back to top button