A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Ummu safwam
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR…

????????????????????????????????????????

Writing by
Ummu
Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

Page 1⃣8⃣

Prince naganin tafiyarsu, Bilkisu, ya shiga motarsa tareda Abdullah suka nufi asibiti domin adiba masa k’afarsa dake xubar da jini.”

Likita ya kyaramasa k’afar tareda bashi maganun nuka domin yayi amfani dasu yasha.”
A jiye Abdullah gida yayi, shikuwa ya k’arasa gida.”

Da shigarsa gida, ya hango Bahijja tareda yarima Fahad a zaune suna hiransu ta masoya.”
Ganinda yayiwa Bahijja saida gabansa yafad’i domin ya d’auka Bilkisu ce tabiyosa har gida domin d’aukar fansar abunda yayi mata, dan shi yanzun harga Allah tsoron Bilkisu yakeji, dan muguwace, ta iya mugunta.”
ya kai dibansa a k’afarsa, inda ta takasa da talkaminta mai tsini,
har k’afar tafara kunbura, yace “Allah ya i’sarmun muguwa.”
Yawuce su Bahijja ko kallon inda suke beyiba ya k’arasa shiga gida.”

Tafiya sukeyi a dai2 sahu, Bilkisu sai kuka takeyi, jakadiya da Safeenat sai hakuri sukebata,
Jakadiya tace meyasa kika zab’arwa kanki wanann rayuwar.”?
Karki manta kinada gata kinada k’udi, kuma kinada mulki, gimbiya amma kika zab’arwa kanki rayuwar wulak’anci haka.”?

Da sauri ta kalli jakadiya, tayimata nuni da tadaina maganar kar Safeenat dakeyin waya ta fahimci abunda take fad’i.”

Bakinta taja tayi shuru, domin bin umurnin gimbiya.”

Adai dai wani katafaren gida madai daici, mai a dai2 sahu, ya tsayardasu, Safeenat ce tafara fitowa ta biyasa kud’insa, sanan suka soma d’aukar kayan suka nufi cikin gidansu.”

Shigarsu gidan kenan, suka tarar da mahaifiyar Safeenat a Zaune tana yankan yakuwa,
Da fara’arta ta tarbesu , tanufi pallonta dasu.”

Anan sukaita gai gaisawa, daga k’arshe Safeenat tafad’awa mahaifiyarta abunda ke faruwa,
Momy mahaifiyar Safeenat ta tausayawa Bilkisu tareda mahaifiyarta jakadiya, a cewarsu.”

Momy tabawa Safeenat umurni da akwashi kayansu a kaisu d’akin saukar bak’i, hkan kuwa a kayi.
Angyara masu d’akin had’i da kankab’e masu k’ura sannan aka shigar masu da kayan ciki.”

Jakadiya ta mai da kallonta a d’akin, sannan ta kalle Bilkisu tace Allah ya taimakeki, a nan zamuci gaba da rayuwa kenan?

Bilkisu ba ta kula Jakadiya ba.”

Jakadiya ta kuma fad’in ranki ya dad’e nasan bakyason yawan tambaya, amma naso naji ko meya had’inki da wanda yakoromu a gidan damuke zaune.”? naga alamarsa kamar jinin sarauta ne.”?

Jinda Bilkisu tayi jakadiya nafad’in ankorosu a gidansu, yasanya idanunta suka kad’e sukayi jajir,
Sai hawaye take zubarwa.”

Wayarta tad’aga takira maimartaba sarki Abdulraham yola, mahaifin Bilkisu kenan,
Abba naganin wayar gimbiya Bilkisu yatashi daga kishin gid’en
dayake ya zauna, cikin farin cikin dajin dad’i ganin kiran gimbiya Bilkisu, yayi saurin d’aukar wayar.
Yace gimbiya Bilkisu ina fatan dai lafiya k’alau kike?

Bilkisu tayi kokarin saita muryanta dake cikin yanayin kuka, tace ‘Abba lafiya k’alau nake, sai dai kewarku dakai da Ammi da kuma yaya Abdull,

Abba yace “gimbiya Bilkisu ko kina buk’atar trasfar ne kidawo kusa damu.”?

Tayi murmushin dole, tace a’a Abba inajin dad’in karatuna anan.
Munkusan samu hutu Abba zanzo na zauna tare daku.”

Yace yawwa gimbiya Allah yashigemaki gaba damak’iyanki, tace “Amin Abbanah, sukayi dariya gaba d’ayansu.”

Tace Abba kasan dalilin dayasanya nakiraka kuwa.”?
Yace ” gimbiya ina zansani sai kinfad’amun.”

Tace Abba ina buk’atar katuromun fadawa gobe.”

Abba yayi murmushi yace gimbiya dama nafad’a maki zaman makaranta irin wannan dole saida basu tsarunki,
Kika kafe ke saida jakadiya kawai zakitafi,

Meke faruwa dakene.”?
Babu wani abu dayasame ki ko.”?

Tayi murmushi tace Abba babu komai,
Ina dai buk’atarsu a kusadani, nawani d’an lokaci,
Akwai wani taro daza’ayi a makarantar. Abba ina buk’artasu saboda tsaru,

Abba yayi murmushi yace kinyi tunani maikyau gimbiya Bilkisu.”
A cikin fadawan wad’anne kike buk’ata a turumaki.”

Tace “yawwa Abba nah, don haka nakesonka,
Abba ina buk’atar katuromun sarkin gida, da sarkin hukunci da sarkin gishiri, Abba katurumun fadawa masu hukunci, mota ashirin, sannan Abba ina buk’atar kud’i a accaunt d’ina masu yawa.”

Yace “gimbiya Bilkisu duk abunda kike buk’ata zanyimaki shi, saboda nasan bazaki Zubar da mutuncinki da darajarki ta ‘ya mace ba,

Yaushe kike buk’atar aturomaki fadawan.”?

Tace “Abba gobe nake buk’atarsu k’arfe goma na safe.”

Abba yace “gobe zasuyi sammako, su tafo insha Allah.”

Gimbiya Bilkusu tace “nagode Abbanah.”

A nan sukayi sallama, da Abban nata,
Ta maida kallonta a gun jakadiya dake zaune kan katifa tana saura renta,
murmushin jin dad’i tayi, tace “banason amfani da mulkina domin na musgunawa mutane, amma yazama dole nakwace ‘yancina a wurin Prince Adnan
Jakadiya tace “ranki yadad’e meye tsakaninki da Wanda yayi muna wulak’anci, nan.”?
ina ganin kamar jinin sarautane.”

Bilkisu ta kalli jakadiya tace “dare yayi jakadiya mukwanta muyi barci, gobe idan Allah yakaimu,
insha Allah zanbaki amsar dukan tambayoyinki dakikayi mun.”

Jakadiya tace “to Allah yakaimu goben saida safe.”

A hka suka kwanta Bilkisu kuwa barci ya ga gareta,
sai tunani take ta yanda zata d’auki fansar wulak’ancin da prince yayi mata a gaban bainar jama’a.”

Ummu safwan????????????????
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR..

????????????????????????????????????????

Writing by
Ummu
Safwan

 PURE MOMENT OF 
     LIFE WRITER'S

page1⃣9⃣

A haka barci b’arawo yayi awun gaba da ita.”

Shiri takeyi domin tafiya makaranta, domin tunda asuba Abba yakirata a waya yake shaida mata, fadawan da yaturo mata sunkunsan k’arasowa .”

Shiri take a gurguje, saiga Safeena takawo masu breakfast dinsu, kallon agogon hannunta tayi, tace “sis kinsan lokacin cin abincina beyiba sai zuwa anjima zanyi breakfast,
Kifito kawai muk’arasa makaranta karmu makara.

Safeena tace “to bara na d’auko mayafina, ta ajiyewa jakadiya abincin tajuya tafita.”

Tafiya sukeyi suna fira ita da safeenat, d’alibai sai nunata sukeyi suna magan ganunsu, bata kulasuba, class tanufa domin d’aukar karatu,

Fitowarsu kenan daga class, Bilkisu tasamu wuri tazauna, tare da safeenat a kan wasu fararen kujerun roma,
Suna diba littatafansu, sai ganin prince tayi a gabanta tareda Abdullah sai wani huci yakeyi,
Kallon tsana yabita dashi yace “ke ‘yar matsiyata waye yabaki izinin zama a kan wad’an nan kujerun.”?

   Nakoreki a garin nan ashe bakitafi bako?

To yau zanyimaki kurar kare,
sai anrakamun ke kibar garin nan saboda na tsaneki banason ganin fuskarki mai kama da aljanu, muguwa kawai,
yakai dibansa a k’afarsa data kumbura yace kinyi nasara kinyimun illah to kisani kafin nasanya ayimaki rakiya kibar garin nan kema sainayi maki illah wadda ko mak’iyinki sai ya tausayamaki.”
Abdullah yace ” bazaki tashi a kan kujerar anamaki magana ko kallon mutane bakyayi,mai sunfar muna fukai,
ya sanya hannu ya zame kujerar da take zaune saida tafad’i k’asa.”

Ranta idan yayi dubu ya b’aci idanunta cike da hawaye ta d’aga kai ta kallesu, samada k’asa bata tankamasu ba, saima sunkuyarda kanta ta kumayi k’asa tana zubar da hawaye.”
Safeenat ce kejan hannunta, alamar subar wurin, amma tayi tsaye tak’i d’agawa daga inda take.”

Sai jiniya suka jiyo a bayansu, da bushe bushe irin na sarakuna, motocine keta shigowa cikin makarantar sunfi talatin, aikuwa kallo yakoma Kansu kowa mamaki yakeyi, ko bak’i sukayi a makarantar ne.”? wasunsu na fad’in wanan sarki wane garine yakawo masu ziyartar bazata,
Prince kuwa naganinsu yabisu da kallon burgewa yanda suke busa da jiniya, yasan ko gaba da gabanta a sarauta.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33Next page

Leave a Reply

Back to top button