A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Nan take fadawa suka tallebesa a kasanyashi a mota suka nufi asibity dashi,
Asibitin kud’i suka nufadashi,
Bilkisu tabada ATM CARD d’inta akaciro mata kud’i ta dank’awa d’aya daga cikin fadawan kud’in, tabashi umurni duk abunda ake buk’ata yayi amfani da kud’in asaya.
Takoma warta mota tayi zamata tareda jakadiya.”

Likitoci suka kawowa prince taimakon gangawa, suka tallabesa suka nufi d’akin da za’a dibashi.

Prince kwance cikin jini kamar bayada rai saiwani numfashin wahala yake fitarwa,
Likitoci tsaitsaye a kansa domin ceto rayuwarsa,

Babban likitan yabada umurni da akiramasa d’aya daga cikin wad’anda suka kawosa,

Fadawa suka nufi ofishin likita yake shaida masu majinyacinsu yana buk’atar asanyamashi jini da gangawa,
Idan ba hakan ba yana iya rasa rayuwarsa a kowane lokaci, domin jininsa yakusan k’arewa ajikinsa,

Dan haka aje cikin ‘yan uwansa a nemo wasu daga ciki wad’anda jininsu yayi daidai danasa sai a d’ebeshi a sanya masashi,

Fadawa suka fito suka nufi wurin gimbiya Bilkisu suna shaida mata abunda likita ya fad’amasu, jini ake buk’ata asanyawa mutumin da suka kawo,

A razane tafito a motar tana kallonsu, d’aya bayan d’aya tace, to Ku meye amfaninku da bazaku bada jininku a sanyawa musulmi d’an uwanku domin ceto rayuwarsa ba?”

Kallo suka bita dashi cike da jin tsoro,
Fahimtar haka da tayi daga garesu yasa,
Tarab’asu tawuce cikin sauri tanufi ofishin likita,
Tura k’ofa tayi tashiga tareda yimasa sallama, bata jira amsawarsa ba, ko kuma ya bata umurnin zama ba,
Taja kujera ta zauna,

Likita saibinta yake da kallon mamaki,
Yace malama lafiya?”
Daga ina haka?”

Takai dibanta a wurin likita tace ” yi hakuri docter banyi maka bayanin koni wacece ba, wlh duk a rud’e nake,

Marar lafiyar damuka kawo yanzun,
wadda ke buk’tar jini cikin gangawa, shine nazo domin a d’ebi jinina a sanya mashi, domin idan akatsaya Neman ‘yan uwansa zai iya rasa rayuwarsa,
Don Allah docter kayi Sauri ka auna jinina idan yayi daidai danasa a sanyamashi.

Likita yatsora mata ido cike da mamaki, yace “idan son samune munfi buk’atar asanya masa jinin namiji a kan na mace,
Saboda mace tana haihuwa kuma tana zubarda jini duk k’arshin wata,

Mik’ewa tsaye tayi cike da b’acin rai, tace “dakata Docter ✋???? kaifa kace yana cikin mawuyacin hali mutuwa ko rayuwa?”
Amma kakeyimun wani dogon zance, magana d’aya nakeso kafad’amun,
Ana iya d’ibar jinin mace a sanyawa wani koba’a d’iba?”

Docter yace ana d’iba amma idan mace ta jima bata haihuba,

Bilkisu tace “toni bantab’ayin aure ba bare na haihu,
Docter sanyamun abun d’ibar jini, kad’iba kak’arawa bawan Allah karya rasa rayuwarsa.

Da Sauri likita ya d’auko kayan aiki ya kwantar da ita kan gado yashiga d’ibar jininta.

Bayan minti talatin ta tashi daga kan gadon, fadawa sai sannu suke jera mata.

Ganin likita tayi a gabanta yana mata sannu had’i dayimata tambayoyi,
Babu abunda kikeji a jikin?”

D’aga masa kai tayi tace “banajin matsalar komai docter.

Yace “Alhamdulillah mund’ebi jininki roba biyu,
Asanya masa wadda insha Allahu munasaran farkawarsa nan da awa d’aya,

Tace “Allah yabashi lafiya.”

Likita ya amsa da “Amin.”
Ya kuma kallonta yace “amma ke matarsa ce ko?”

Domin a zamanin damuke ciki babu wadda zai iya taimaka maka da jini sai mahaifiyarka, ko kuma matarka, kodai wani d’an uwanka koshi d’an uwanka najini,

Bilkisu tayi murmushi tace niba matar sabace, ba kuma ‘yar uwarsa bace,
Asalima bansan koshi wayebane,
Domin har yanzun banga fuskarsaba, tsoho ne, ko yarone, bansaniba, taimako nayimasa saboda Allah domin duk wadda ya taimaki wani Allah zaitaimakesa.”

Pls ‘yan uwana kutaimakamun da addu’a idanuna ciyo yakemun sosai

Writing by Fareedah bashir
Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

  WHATSAPP NO:

+2347039625239
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR….

????????????????????????????????????????

   Writing by
       Ummu
         Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

Page 3⃣6⃣ 3⃣7⃣

Bilkisu ta sauka garin yola lafiya,
Inda dukkanin wad’anda ke cikin gidan masarautar yayi murna da farin cikin dawowarta.

Bayan tayi wanka tashirya taci abinci, ta sauko k’asa tanufi sashen maimartaba domin taji Neman da yakemata,

Ta Tarar da maimartaba kishin gid’e a kan kujera,
Tayi sallama tashiga.
Tasamu wuri a k’asa gefen k’afarsa ta zauna, ta sunkuyarda kanta k’asa tace “Allah ya taimakeka Allah ya k’ara maka lafiya,
Gani nazo ranka ya dad’e Allah yasa ba laifi tanayiba,

Maimartaba yayi murmushin nan irin nasu na manya,
Yace “aibakya laifi Bilkisu,
Domin kina kiyaye duk wani abuda kikasan zaib’amun rai,
Dan haka nafifitaki a cikin ‘ya’yana.

Wato Bilkisu wata shawara nakeso muyidake wadda maganar waya bata isa,
Saikinzo gani gaki.
Bilkisu kinsan d’an sarkin kano,
Fahad shiyakeson Bahijja,
Ta girgiza kai.
To satinda yawuce mahaifin yaron wato sarki Bashir, yazo da kansa ba aike yayiba,
yazo neman aurenku keda Bahhija.
Saida gaban Bilkisu yafad’i

Yaci gaba da cewa Kema d’ansa Adnan yaganki a makaranta, yanunamun dacewa, harkun fahimci junanku, dan hakan nayanki hukunci aurardaku gaba d’ayanku keda Antynki Bahijjah.

maimartaba magana yakeyi amma gaba d’aya hankalinta bayajikinta, musamman dataji ya ambaci yabadasu gaba d’ayansu,
Idanunta ne suka cika da hawaye tasunkuyarda kanta k’asa yadda Abbanta bazai iya ganin hawayentaba,

Maimartaba tunda yafara yin magana yake kallon yanayinta yalurada lokaci d’aya tacanza masa daga k’arshe hawaye take zubarwa,

Yace subahanallahi Bilkisu laifi?”
Meyasanki zubarda hawaye?”

Goge hawayenki kidaina kuka,
Idan maganar aure ce bakyaso daki zubarda hawayenki k’ara afasashi,
Nima abunda yak’arabani kwarin gwaiwar yimasa alk’awalin badake, yazomun da mgnar cewa kunfahimci junanku a makaranta dake da yaron.
Amma wallahi Bilkisu mundun bakyaso to alk’awari ne bazan maki auren dole ba,

Kanta a sunkuye k’asa sai zubarda hawaye take,
Gaba d’aya tausayin mahaifinta duk yagama lunlub’eta, a zuciyarta,
Wato domin ya faranta mata rayuwa yana iya ruguza alkharin dayayiwa sarki Bashir nabayardasu dayayi gaba d’ayansu,
Abba idan yayi haka kuma har abada sarki Bashir bazai kuma yarda da maganarsaba,
Sannan kuma idan yayi hkan, yaya k’auwarsa sarki bashir Amminmu zaji dad’i wadda suke uwa d’aya uba d’aya, da sarki Bashir,
Zai iya zamantuwar rugujewar zumcinsu,

Maimartaba yace “gimbiya Bilkisu kenake saurare, kukan da kikeyi nameye?”

   Takuma sunkuyar da kanta k'asa tace"Abba karatuna banaso nayi aure batareda na kammala karatunaba,
    Abba inaso nayi karatu sosai domin nataimaka 'yan uwana mata takowace hanya,

Abba yace “nasan kudirinki a kan karatunki, gimbiya Bilkisu,
Nayiwa sarki Bashir bayanin karatunki,
Yace zai tambayi Adnan d’in idan yaji yagani ya amince zaibarki idan akayi auren saikici gaba da karatunki
Idan kuma be aminceba to lallai bazan auran dakeba sai bayan kin kammala karatunki har lokacinda burinki yacika, gimbiya Bilkisu,

Murmushin dole ta k’wakwalo tayi, had’ida kallon mai marmarba,
Tace nagode Abba,

Yace “goge hawayen kitashi kitafi kikwanta kihuta nasan kinsha gajiyar hanya,

Tamik’e tsaye had’ida yimasa sai anjima,
Tafita daga d’akin,
Tafiya takeyi kamar wadda kwai yafashewa a cikin domin gaba d’aya batacikin hankalinta, da kyar tasamu ta isa d’akinta cikin mawuyacin hali.

Akan gadonta tafad’a tasaki wani wahalallen kuka mai tsuma zuciya,
Tana magana ita d’aya kamar wata zaranriya,
Ashe dama Adnan d’an uwanane yake wulak’antani hakan?”
Meyake nufi da turowa Neman aurena?”
Wani sabon salon wulak’anci dacin zarafi zaikuma yimun bayan ya aureni?”
Domin a bakinsa yasha furtamun bayasona, bayason ganina,
Me kama danima idon ya ganta sai ya hukuntata,
Sannan ace da wannan zanyi rayuwar aure?”????
Takuma b’arkewa da wani sabon kuka mai tsuma zuciya,
Tana danasanin had’uwarta da Adnan a rayuwarta gashi yanzun yana neman ruguzamata rayuwa.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33Next page

Leave a Reply

Back to top button