A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Bilkusu tayi karfin halin yimata mgba tace sis tsayar mana da mai a daidaita karya tafiyarsa.
Tsaidashi sukayi takama hannun jakadiya tasanyata a ciki, sanan tadawo d’aukar kayansu, ba komai tad’aukaba sai jinkar takardunta, sai kuma a kwatin kayansu, tasanya a bayan adaidai ta.
Mutane sai kallonta suke suna mai tausaya mata.
Dawowa ta kuma kiyi, tanufi gefenda makwanciyarta take tsaye tana zubarda hawayen tausayinsu domin sunyi matuk’ar sabawa da ita
Cikin yanayin kuka ta nufo Bilkisu ta rungumeta tana kuka, Bilkisu tayi k’arfin halin yimata mgna, tace
“Hajjah daina kuka zandawo gareku bada jimawaba, abunda nakeso dake yanxun kisamu yara sukwashe maki duk wani abu dake wurin nan, nabaki shi kyauta, sanan ta Nuna wani k’aton frege tace wanan kuma a kai sa gidan liman nabasashi.”
liman dake tsaye cikin yanayin tausayi yanufota yana godiya, domin tun zuwan Bilkisu a unguwar duk ranar juma’a saitasanya ayimasu abincin sadaka duk wanda yazo sallah a masalancin to saiyaci abincin Bilkusu yana mai sanyamata albarka, sannan shima liman d’in duk zai sallar juma’a dasabon d’unki yakeyi wadda Bilkisu take d’unka masa.
Abunda yasa suka saurarawa wadda yayi mata hkan, ganin fadawa dasukayi da kuma Prince da ke tsaye domin sunsan halin prince ba imani ke garesa ba.
Sanan tanuna wasu durum2 na ruwa tace liman a kai wad’an nan masalanci a dinga zuba ruwan alwala.”
Tana kaiwa nan tajuya tanufi wurin prince dake tsaye yana kallonta sai a lokacin yafara tausayamata, tanuna masa hannu tace” kasaurare hukuncin da zanyi maka gobe dakai da duk wasu magoya bayanka.”
Tabarshi nan a tsaye tashiga a dai2 ta suka nufi gidansu sakeenat.”
Ummu Safwan ????????
????????????????????????????????????????
A WATA MASARAURAR..
????????????????????????????????????????
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S
Page1⃣6⃣
Gimbiya Bilkisu ce kwance a kan makeken gadonta, tana xubar da hawaye, tana tuna irin wulak’ancinda prince Adnan yake mata, a bainar jama’a, to ita metamasa? meta taremasa a rayuwarsa?”
To tabbas idan befita rayuwartaba sai yayi nadama, a rayuwarsa.”
domin zatayi amfani da mulkinta da sarautarta tasanya a azabtar dashi,axaba mai tsanani.”
A haka tak'arasa kukanta har b'arci barawo ya saceta."
Shiri takeyi domin tafiya makaranta, yau Monday, test kegaresu maizafi, domin test d’in darasinda zasuyi malamin ba sauk’i ke garesa.
A gurguje ta kamlla shirinta tafito, domin tayi breakfast.
Safeenat sai wayatakeyi mata da tayi sauri lokaci yakusan k’orewa.
Fitowa tayi tana shedawa jakadiya, tafiyarta.
Jakadiya sai addu’a takeyamata, tareda kirari
Murmushi Bilkisu tayi tace “jakadiya bazaki dainaba kenan. Tayi tafiyarta.”
A makaranta tasame safeenat tana jiranta domin saura binti 10 sufara test d’in,
samu wuri tayi tazauna a kusa da safeenat, Bilkisu tace “sis yau makara nasoyi. Allah kawai yatsare danayi loosing din test d’in nan.
Safeenat tace baki kwanta dawuri bane sis, kina can kina tunanin masoyinki da ke yola, tana fad’a mata hakan ne cikin yanayin wasa,
Bilkisu takai mata dukan, wasa tace “Allah yatsareni aini banada saurayi. Ke banma tab’ayin soyayya a rywataba, saboda ni har ynzun banga namijin da yayi dai dai da tsarin rayuwata ba.”
Safeena tarik'e baki???? tace "keko sis wani namiji ne wannan kikeso ki aura haka?
Bilkisu tace wannan nabarwazuciyata.”
tashi mutafi kinga ga uncle can na hango zai shiga class kinsan halinsa idon ya rigamu shikenan munyi loosing d’inta, muyi sauri murigashi k’asarasawa.”
Suka mike suka nufi ajin.
Tafiya sukeyi wadda zata sadasu ajin nasu,
Bilkusu saiji tayi ancire mata hijabi daga bayanta, kankame jikinta tayi cikin jin kunya.
tayi tsaye wuri d’aya, juyawa tayi domin ganin waye yacire mata hijabi, sai ganin prince tayi a tsaye tareda k’awayensa, yacije baki yana murmushin mugunta, k’awayesa sai dariya sukeyimata.
Safeenat tasoma yimasu magiya, tace ” don Allah prince kayi hakuri kabata mayafinta, idan wani abu takeyimaka wlh daga yau ta daina bazata kuma yimaka shiba, pls Prince????????
Tsawa yadaka mata, yace “ina ruwanki”? rufemun baki, kada ki kuma yimun katsalande s al’amunrana”.
Shuru tayi taja gefe ta tsaya.
daga k’arshe tacire d’ankwalin kanta, tabawa Bilkusu tarufe jikinta dashi.
Dariya suka dinga yimata suna nunanta da hannu, musamman prince Adnan da Abdullah,
Matsowa yayi kusa da ita, yana mai murnushin mugunta, yace “Bilkisu ne sunanki kowaye? Ashe ke ba kowa bace? Ba kuma ‘yar kowabace face ‘yar talaka, masu zaman kansu.
Harkike neman fad’awa jinin sarauta. mu samman ni prince Adnan yanuna kansa da hannunsa.
To zakiyi nadamar abunda kikayimun, za kuma kiyi danasani a rayuwarki, domin daga yau, bazaki kuma zama a garin nan ba.
Zanyi amfani da mulkina da kuma sarautana, nasanya akoreku a garin, nan dake da mahaifiyarki. domin nanumaki k’arfin mulkina, kuma kitabbatar da cewa mulki da sarauta, ba abun renawabane, musamma a irinku talakawa matsiyata.
Makure take a bayan Safeenat, sai kuka takeyi, musamman jikinta dake sake kowa sai kallonta yakeyi, sanye take da atamfa riga da siket, sun d’an kama jikinta, amma ba sosai ba gata Allah yahoremata dukiyar Fulani. d’ankwalin da Safeenat tabata shine tarufe k’irjinta dashi.
Kuka takeyi tana kallonsa sama da k’asa, tace ” tabbas yau na tambatar da cewa kai jahiline, baka da tausayi.
zuwa makarantar kawai kake, amma baka amfani da abunda ake koyarda kai, nagane zuwa makarantar kawai kakeyi badon kayi karatuba sai domin kanuna cewa kai d’an sarauta ne, kataka talaka wanka, yanda ranka yakeso, kai a tunanin ka shine mulki Ko sarauta?
To ba mulki bane, wannan shi akekira da jahilci wadda yake d’awainiya da kai a yanzun,
Sannan kasani baka i’sa ka koremu a garin nanba, domin bada ku’din masarautarku aka gina garin nan ba, sannan ina mai tabbatar maka da saikayi nadamar abunda ka aikatamun,”
Kuka take mai tsuma zuciya. Shikuwa sai kallonta yake cikin jin dad’i domin yasan daga yau bazata kuma yimasa rashin kunyaba.
Abdullah yace ke ‘yar matsiyata duk’a kibawa prince hakuri yabaki hijabinki, domin ransa yab’aci.
Kallo tabi Abdullah dashi, cikin b’acin rai, ta d’aga masa hannu ya isah, sarkin molarsa, tobada kai nakeyiba dashi nakeyi, kabarshi yabud’e kazamin bakinsa yayi magana, bakaiba.
Kuma ina fatan a cikin mgnarka babu kalaman ban hakuri a cikin domin idon zamu shekara hka baka isa nabaka hakuriba.
Prince dake tsaye takawomasa mak’ura, ya kalleta yace “tabbas yau saina bak’antamaki, kuma saina musguna maki, har saikin durk’usa k’asa kinbani hakuri sannan zankyaleki, sai nanuna maki keba kowa bace, face baiwa, ba kuma baiwar kowaba face baiwata wulak’anta tarciyar baiwa.”
Yana rufe bakinsa saiji yayi ta d’auke masa fuska da mari, tana wani huci.
k’arya kakeyi nazamar maka baiwa kuma mafi wulak’antar baiwa a wurinka.
Ta kuma matsawa gab dashi, tasanya talkaminta mai tsini???? ta takamasa k’afa, ta Murza, saida prince yasaki k’ara mai sauti wadda tajawo hankalin d’aliban makarantar yadawo kansu, sanan tasa hannu ta k’arbe hijabinta a hannunsa
taja hannu safeenat, suka bar wurin tana mai zubarda hawaye.”
Anan tabar prince durk’ushe yana murk’usun k’afarsa, Abokaninsa sai sannu suke jeramasa, idonsa ya rikid’e yayi jajir.
Kallo yabi Abdullah dashi, yace “tabbas yau d’in nan sai sunbar garin nan ita da matsiyaciyar uwarta, mik’ewa yayi tsaye ja hannun Abdullah suka shiga mota suka nufi gidansu bilkisu.”