A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Gimbiya Bilkisu na ganinsu tayi murmushin jin dad’i, sun iso a dai dai lokacinda take da buk’atarsu.

Prince sai kallon motocin yakeyi yaga sunk’i k’arewa sai shigowa sukeyi gwanin ban sha’awa.”

Be ankaraba sai ganinsu yayi a gabansa sun tsaitsaya mamaki yashigayi,

Gimbiya Bilkisu tashi tsaye tayi tasamu wuri ta zauna a kan kujera, ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya mulki da sarautar ya motsa, Safeenat sai kallo tabita dashi tana mamaki,

Fadawan kowanensu yafito a mutarda yake a guje suka runsunawa Bilkisu suna kwasar gaisuwa had’i dayimata kirari, “Allah yataimake, Allah ya tsaremana lafiyarki, hak’ika masarauta tayi rashinki, ranki ya dad’e gamu, sarki ya turomu kina buk’atarmu a kusa dake,

Bilkisu dake kan kujera ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya, ta maida kallonta agun prince da duk yawani rud’e sai mamaki yakeyi,yana tunani a ransa to ita wanan wacece?
shi kuwa Abdullah sai goge zufa yake, domin yafita hanyacinsa gaba d’ya.

Ta maida kallonta a fadawan tayimasu nuni da hannu alamar sutashi,
Da Sauri suka mik’e tsaye, Suna mai jiran umurninta.

Shikuwa Prince da Adnan saboda rud’ewa rik’e yake da hannun Abdullah suna k’okarin Barin wurin,
Dalibai da malamai duk sunzagayesu sai kallon mamaki sukeyiwa Bilkisu.”

amma banda shugaban makarantar domin yasan ko ita wacece.”

K’okarin barin wurin sukeyi Prince da Abdullah tayiwa fadawa nuni da hannu da su tsayar mata dasu,

Aikuwa a guje suka sha gabansu, suna fad’in gimbiya ke buk’atar mgna daku,
Prince ya kalli kansa yace wacece kuma gimbiya?
Kusan kodawa kuke magana kuwa? Yanuna kansa da hannu.”

Duk abunda sukeyi akan idon gimbiya, tayi murmushin mugunta.”

Gimbiya Bilkisu tace ina sarki hukunci? Yamike tsaye yace gani ranki ya dad’e.”

Sanan ta kuma cewa ina sarkin gishiri.”?
yace “gani rankin ya dad’e.”

“Tayi masu nunu da Prince da Abdullah dake tsaye suna musu da fadawa,

Tace ” kud’aukomun wad’ancan yaran masuyimawa mutane gardama.”
Suka runsuna sukace angama ranki ya dad’e

Prince da Abdullah na tsaye saiji sukayi and’aukeso sama, ba’a diresu a ko inaba sai a gaban Bilkisu dake zaune a kan kujera.”

sarkin hukunci yace ranki ya dad’e gasu.”

tayi nuni da hannu alamar subar mata su a nan, ????

Ta kallesu sama da k’asa tayi murmushin mugunta,
Tace prince Adnan ina mulkinka yake? Ina sarautarka take? Kana amfanida mulkinka da kuma sarautarka kana taka talakawanka yanda kakeso.”
bakasan irin baiwar da Allah yayiwa wani a cikin wad’anda kake wulak’antawa ba,
To gani gabanka kana i’k’irarin zakasanya fadawanka suyimun korar kare a garinka,
Kana i’k’irarin zaka wulak’antani, wulak’anci mai tsanani.
Ba dan komai kakeyin haka ba, sai dan kana yarima d’an sarki,
A yanzun zan nunamaka ko a sarautar, gaba da gabanta,
Zan nunamaka mulkin wata masarautar yafi mulkin masarautarku.”

Tace “ina sarkin hukunci yace “gani ranki yadad’e, tanuna Abdullah tace ” meye hukuncin mekatsalanda a magana.”?
sarkin hukunci yace “bulala hamsin,ne gimbiya

tace sarkin hukunci ayimasa bulala d’ari gamida hukunci mai tsanani.”

 Yace angama rankin ya dad'e."

 Abdullah najin anbaci bulala d'ari saida  yasaki fitsari a wando d'alibai sai dariya sukemasa, dama addu'a sukeyi Allah yakawo masu k'arshin zaluncin prince a makaranta,

Abdullah ya kalli prince dake durkushe a gaban Bilkisu, yace “aiga irinta nan saida nafad’amaka ka kyale yarinyar nan amma ka kafe saitabar garin nan, yanzun gashinan kadazamun bala’i.”

Ya runsuna a gaban Bilkisu yace ranki ya dad’e kiyi hakuri natuba wlh ko kallonki baza kuma yiba, kice a sansautamun hukuncin nan, wlh bazan sakeba.”????

Bilkisu tayi masa wani kallo sama da k’asa
“Tace wai mekuke jira dashine? Kunbarshi yana damuna da suruto.” aikuwa aka tungumi Abdullahi akasanyashi a mota, yana kuwa ya komai, duk yajik’e wandonsa da fitsari????

Ta maida kallonta a kan prince, tace “natsaneka kamar yanda kaima kake i’k’irarin ka tsaneni, bana buk’atar ganin fuskarka,
Tace ina sarkin gishiri? yace “gani ranki ya dad’e tace asanyashi a mota a tafi dashi, a horashi a koyamasa yanda ake daraja d’an adam a duk inda yake.”

Ummu safwan????????
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR….

????????????????????????????????????????

       Writing by
             Ummu
                Safwan

PURE MOMENT
OF LIFE WRITER’S

Page2⃣0⃣

Fadawane rik’e da prince suna k’okarin sanyashi a mota,
Shikuwa Ya sunkuyar da kansa k’asa, idanunsa sunriked’e sunyi jajir.” jiyakeyi kamar k’asa ta tsage ya shige saboda kallon da d’alibai suke masa.”

Gimbiya Bilkisu na zaune a kan kujera ta d’ora k’afa d’aya kan d’aya,
tana kallon yanda za’a sanya shi a mota a tafi dashi.”

  za'ayi sanyashi Mota kenan, tayiwa fadawa magana tace " kudakata."✋????       

Suka tsaitsaya suna masu jiran umurninta.”

Tace “kusakesa, kurabu dashi.”
Nasan yayi nadama domin Daga nadama a idanunsa.”
Ta matso kusa dashi taimasa kallon sama da k’asa tace “ko yanzun, kafahimci gaba da gabonta.”
Tajuya ta kalli d’aliban dake kallonsu, ta kuma maida kallonta gareshi, tace “diba can???????? taiyi masa nunida d’aliban dake kallonsu.”
tace ‘duk kai suke kallo.”
“Adnan ina k’asaitarka da kuma sauratarka.”?
Adnan ina mulkinka yake? Wadda kake tak’ama dashi kake wulak’anta talakawanka yanda kaga dama.”
Duka babu ko d’aya a yanzun.”
domin yanzun kana k’arkashin mulkina da sarautata.”
Na fad’amaka zansanya ayimaka hukunci mai tsanani da kaida duk wani magoya bayanka.”

 zan  sansauta maka ne yanzun, domin halinda naganka ciki, a yanzun yayi mun dad'i a rayuwata."

Tace “sarkin hukunci,
Yace ” Allah ya taimakeki.” tace “kusakesa, kurabu dashi yayi tafiyarsa.”

Amma, Kutafimun da wancan ????????tanuna Abdullah.”
kuyi masa hukunci mai tsanani, wanda gobe idon yaji manyansa na magana baya kuma yimasu katsalandan a magana.”

Abdullah yanajin anbanci atafidashi.”
saida yabud’e murfin mota yafito a guje, yana kuwa yanakiran ya tuba bazai sakeba.”
Fadawa suka tugumesa suka sanyashi a mota suka tafi dashi.”

 Ta maida kallonta a Safeena datayi mutuwar tsaye cike da mamaki."

Tace “sister mutafi gida lokacin cin abincina yayi, ta kalli agogon dake hannunta.”

Safeenat tace to rankin ya dad’e.”
ta kalli Safeenat tayi dariya, tace “nasan yau akwai magana a bakin nan naki.”
Safeenat tace kusan hakan ne gimbiya tarunsuna kamar yanda taga fadawa nayi mata.”????
Bilkisu tayi dariya takaimata dukan wasa, tace “to mutafi gida ki furta abunda ke cikin ranki.”

Suka nufi mota suka shiga sai jiniya akemasu suka bar makarantar suka nufi gida.’
d’alibai kowane fad’in albarkacin bakinsa yakeyi.”

Prince yana samun fadawa nan sakesa, bebi takan kowaba, yanufi motarsa yabata wuta, saida ya bad’e mutane dake wurin tsaiye da k’ora.”
sanan ya bar makarantar.”
Gudu yakeyi a kan titi Allah ne kawai yakaishi gida lfy.”
Da isarsa gida Bebi takan kowaba, kai tsaye d’akinsa yanufa, dashigarsa d’akin nasa. yayi wurgi da key d’in motarsa gefe, ya cire rigarsa yayi wurgi da ita, ya kaiwa bango nushi, idanunsa sukad’e sunyi jajir sai magana yakeyi, ni Adnan yau nine wata banza ke tuzartawa a gaban bainar jama’a.”?
Domin tana tak’ama dawata sarauta can tata.”
To Ita wacece a cikin gidan sarautar.”?
‘Yar wace masauta ce?
Idon ita ‘yar sarkice ubanta shine nanawa a hawa kujerar sautar?

To tabbas zansanya ayimun bincike a ganomun ko ‘yar wace masarautace.”? tana matsiyin ‘yar sarki, take yawo a k’asa batareda da fadawaba.”? take wulak’antarda kanta haka.”
Tabbas akwai wani b’oyanye sirri a tareda ita, wadda zan banyak’oshi domin tunuwar asirinta.”

Ya kai hannu ya d’auko wayarsa domin kiran Abdullah.”
Sai a lokacin yatuna da Abdullah a can yabarshi dasu.”
Toko mesukai masa Abdullah.”?

Zumur ya mik’e tsaye, yana safa da marwa, daga k’arshe zama ya gagaresa ya d’auko key d’in motarsa yanufi bid’ar Inda Abdullah yake.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33Next page

Leave a Reply

Back to top button