A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Shima ita yake kallo cikin mamaki,
Tace “karyane wlh baka isa kakashiniba sai dai idan lokacina ne yayi.”
Abdullah bazan fad’i inda yakeba harsai ka d’an d’anni bak’in cikin daka sanyani na tsawon wani lokaci.”

don hka kabani hananya nafita nayi tafiyata, tunkafin warin wannan d’akin yayimun illah.”

Cikin b’acin rai yanufuta a fusace, ya had’a bayanta da bango hannunsa a kwalar rigarta ya matseta yana ce mata.
“Ina Abdullah? Iyee ina Abdullah nace?”

Tafita hanyacinta don tsabar tsoro da firgitar abunda yayimata a rayuwarta babu namijin daya tab’ayi mata abinda yayi mata yanzun.”
Ta runtse idanunta hawaye na fita daga idanunta,
Ya k’ara matseta ya kuma matso da fuskarsa daidai tata yana wani huci, zakifad’amun inda Abdullah yake ko saina kasheki?”

Ta katse shi dacewa, “hannunka a k’irjina!” Ta fad’i hakan cikeda shagwab’a kuma cikin sanyin murya wadda ke k’unshe da wahala.”

Besan lokacinda ya saketaba, dashima ya gano hannunsa a kan k’irjinta yake.”
Ya ciji leb’ensa na k’asa a ransa kuwa haushinta ya k’ara kamashi so take tayi suducing d’inshi?”
Tambayar da yakeyiwa kansa kenan,
Lallai yarinyar nan tayi nisa, ganinta zata iya jan hanlinsa ne kome take nufi?”

Duk Kansa yakeyiwa wad’an tambayoyin, a zahiri kuma yanunata da yatsa yana Jamata kunne kokifad’i inda kikai Abdullah ko na d’aukar maki kwankwaran mataki a kanki yanzun nan.”

Karfin hali tayi domin ta tsorata da ganinsa cikin wannan yanayin, idanunsa sunkad'e sunyi jajir
           Tace "malam kabud'emun k'ofa nafita bana iya k'ara minti d'aya a cikin wannan k'azamin d'akin.
       Tanufi wurin k'ofar da niyar tabud'e tafita, saiji tayi ya fisgota ya had'ata a bango ya matseta gam  ajikinsa, saiwani numfashi yake fitarwa  kamar wani zaki." 

Tuni hankalin Bilkisu yatashi, tarufe idonta, tana fad’in SUBHANALLAHI!”

Ina kikasanta? Ashe kinsan Allah?”
To wlh duk Baki fad’i Inda kika kai Abdullah ba zakiyita zama a nan gidan,
Har sai ranar da kikafito da Abdullah sannan kema nasakeki,
Muguwa kawai, aibashi yayi maki laifiba, ni ne nayaki laifin, meyasa bazaki d’auki mataki a kaina ba sai a kansa?” Kina tunin ninafi k’arfinki kenan shiyasa zaki sanya samudawan fadawanki sutafi da Abdullah

Kisakesa mana, ni sai kisanya a kamani.”

Magana yakeyi amma bata tankashi,
Ya kuma kuluwa, yajaye a bakin k’ofar d’akin yaturata a kan katifa,
Yabud’e k’ofar d’akin yafita, yasanyawa k’ofar key yayi tafiyarsa ya barta nan.”

Bahijja da Fahad soyayya tayi nisa domin har ansanya ranar da maimartaba zaitafi yola neman auren Bahijja k’arshen watan nan.”

writing
By
Fareeda
Bashir✍????
????????????????????????????????????????

A WATA MASARAUTAR…….

????????????????????????????????????????

Writing by
      Ummu
         Safwan

PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S

Page2⃣3⃣

Kwana d’aya babu labarin gimbiya Bilkisu hankalin jakadiya duk yatashi,
Tanufi gidansu Safeenat domin duk a tunaninta suna tareda Safeenat,
Saima taji labarin Safeenat batasamu zuwa makarantaba saboda bata da lafiya,
Ba jakadiya k’adaiba gaba d’aya hankalin iyayen Safeenat saida yashi ,
Domin abbansu Safeenat fitowa yayi daga gida yana salati yashiga motarsa nufi neman Bilkisu.”

Safeenat kuwa kuka tashigayi kwana d’aya babu Bilkisu babu labarinta,
Saitafara tunanin ko prince Adnan ne yasanya a d’auketa, domin d’aukar fansar abunda taimasa,
Wata zuciyar kuwa na gargad’inta da bazai iya sanyawa a d’auke ta ba.”

Bilkisu kuwa ya kulleta a d’aki yayi tafiyarsa, sai dai duk bayan a’wa biyu zaizo domin ganin koda tayi nadama tafad’a masa inda Abdullah yake,

Amma babu alamar nadama a fuskarta, sai dai ya tarar da ita tana games a wayarta hankalinta a kwance babu damuwa a tareda ita,

haushinta ya lunlub’eshi yace “wato ita wannan yarinyar batada niyar nadama tafad’i inda takai Abdullah kenan?”

Ya kai hannunsa zai fisge yawar dake hannunta k’irar 1phone tayi saurin b’oye wayar a bayanta,
Ganin zai iya murd’eta ya kwace wayar a hannunta , tatura wayar cikin rigarta,
shi kuma ganin ta tura wayar a rigarta, yayi mata wani kallo,
Yace “shed’aniya ni babu abunda zanyi dake, kidaina wani tura waya a riga, wato d’azun kinji dad’in nahad’a jikina da nake shine yanzun kike Neman nasanya hannuna a cikin rigarki, saboda kina jarabanbiya, to Allah yakiyayeni babu abunda nake iyayi dake, kitafi can kinemi dai dai dake, ninafi k’arfinki babu abunda zanyi dake,
Yaja wani dogon tsaki malama kifito mun da Abdullah nasakeki kikama gabanki .”

Ta kallesa taja wani dogon tsaki, tayimasa kallon sama da k’asa,
Tace “mezanyi dakai, dibeka, me gareka wadda harnake sha’awar had’a jikina da kai,
tanuna masa d’akinsa dayi wani kaca kaca da kaya tace ” k’azami kawai.”????

Tace Abdullah bazan fad’i a inda yakeba domin har yanzun bangaji da ganinka cikin k’unci da bak’in cikin rashin ganin Abdullah ba.”

Yace “a she kema zama bek’aremaki a gidan nan ba kenan,
Domin mundun bakibada umurnin a sake Abdullah ba nima kisani bazan tab’a sakinki ki koma gida ba,
Kuma kisani abincin da nake kawomaki daga yau na daina,
Sai dai kizauna da yunwa idon kikaji wuya zakiyi bayani da bakinki inda kikai Abdullah,

Ganin yanda yake magana sai wani cincira yake cike da b’acin rai da bak’in ciki, kamar ba Adnan d’in da tasani ba,
Dariya tashiga yimasa tana nunasa da hannu tana dariya harda rik’e ciki,

Haushi da bak’in ciki ya kuma lunlub’esa,
Ya d’aga hannu alamar zai daketa meya tuna oho sai ya sauke hannun yana cizon yatsa,
Sai yafita d’akin a fusace yaja k’ofar d’akin da k’arfi yasanya makulli ya kulleta yayi tafiyarsa.”

Ganin ya kuma kulleta bayada niyar sakinta bare takoma gida,
Duk hankalinta yatashi tana tunanin jakadiya, tasan yanzun duk inda take tana cikin tashin hankalin rashin ganinta kwana d’aya dabatayiba
Idon kuma tayi yunkurin shedawa maimartaba to Tabbas hukuncine zai hau kanta watak’ila harta rasa rayuwarta, wadda idan hakan yafaru bazataji dad’i a rayuwarta ba.”

zubur tamik’e tsaye da tuna da Safeenat tasan yanzun labari ya kai a kunnesu na b’atanta
Suma tasan tabbas basa cikin kwanciyar hankali a wannan lokacin.”

Wayarta ta d’auka takira fadawanta tace tana buk’atar a sakar mata Abdullah yanzun nan,

Suka amsa mata da to angama ranki ya dad’e,

Suka sakesa, suna kewar juna domin d’an zamanda sukayi da Abdullah sunshak’u dashi sosai,
Wadda shi kuma Abdullah beso aka sakesaba ko dan saboda kalar abincin dayakeci irin na masarauta,

Sai yashiga tunani a zuciyarsa, gaskya betab’a ganin masarautar da fadawa suke daula haka, sai a wannan masarautar,

inama shima a maidashi cikin fadawan yaci gaba da rayuwasu,
da ya bautawa masarautarsu Bilkisu,
Domin zama taredasu ya fahimci me’ake nufi da sarauta,
Kuma ya fahimci k’aramci da daraja d’an Adam irin na masarautarsu Bilkisu

A haka dai yabar wurin fadawan,
yana kewarsu,
yana mai tsinewa Adnan a rayuwarsa domin yasan shine silar sanyawa a sakesa, domin yaga kwana biyu beganshiba, saikace a tare a ka haifemu.”???? Yaja wani dogon tsaki???? yayi tafiyarsa.”

Adnan yana k’ofar gidansu Abdullah yana kwantarwa da mahaifan Abdullah hankali a kan cewa insha Allahu gobe Abdullah zaidawo gida, ba b’acewa yayi ba yanan cikin k’oshin lafiya da kwanciyar hankali,

Begama rufe bakinsaba sai ganin Abdullah yayi a gabannsu yana dariya, yayi kyau yayi k’iba har wani shek’i yake, yana masu dariya, yanufi mahaifansa ya rungumesu cikin jin dad’i, suma sai murna sukeyi naganin tilon d’ansu,

Prince baki yasaki yana kallon Abdullah yana mamakin kwana biyu, yaga yayi kyau kuma yayi k’iba.

Gefe yajanyeshe yana kallonsa cike da mamaki,????

yace “Abdullah wai meke faruwa ne?” ina fatan muguwar yarinyar bata sanya anyimaka illah ba?”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33Next page

Leave a Reply

Back to top button