A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Yakaiwa Adnan harara???? yace gaskiya ka daina cewa gimbiya Bilkisu muguwa, domin ita ba muguwa bace, illah maison alkhairi da daraja d’an adam,
Ni wlh a baya d’aukar da nake mata wata wuk’antanciyar ‘yar talaka marasa galihu a she ba haka abun yakeba,
Adnan yasaki baki da hanci yana kallon Abdullah cike da mamaki,
Yace “gimbiya kana nufin Bilkisu ‘yar sarki ce?”
Abdullah yace kwarai kuwa, ‘yar sarki ce, wadda mahaifinta da masarauta gaba d’aya suke alfahari da ita saboda kyawawan halayennta da kuma daraja d’an adam.”
Adnan yace ” ‘yar wace masarautarce?” Waye ubanta?” Kuma A wane gari suke gudanar da mulkunsu?”
Duk a jere yajerawa Abdullah wad’an nan tambayoyi,
Abdullah ya wurgamasa harara, yace ” kobaka tambaye niba nad’aukoma labarai da d’umi d’uminsu,
Zakasan kowacece Bulkisu amma kabarni nashiga gida nahuta zuwa anjima sai muhad’u kasha labari.”
Yana kaiwa nan yayi tafiyarsa yabar Adnan a nan tsaye yashiga tunani,
Saida Abdullah yakai k’ofar gida ya waigo yaga Adnan tsaye yana tunani,
Yace gaskya prince baka kyautamun ba, dakasanya a kafito dani daga cikin daular mulkin gimbiya Bilkisu,
Domin gaskiya da bakai bane danace kamar kanajin bak’incikin ganina a cikin daular masarauta
Yana kaiwa nan yashigewarsa gida
Yabar prince Adnan tsaye yana tunani.”
Writing by
Fareeda
Bashir✍????
????????????????????????????????????????
A WATA MASARAUTAR…
????????????????????????????????????????
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S
page 2⃣4⃣ 2⃣5⃣
Prince Adnan kasa tafiya yayi a k’ofar gidansu Abdullah,
Domin gaba d’aya Abdullah mamaki yake bashi lokaci d’aya ya firgice masa har yake iya fad’a masa Magan ganu a kan Bilkisu,
Motarsa Yakoma ya zauna yana tunanin sauyawar da Abdullah yayi,
Kiran sallar azahar ne yafito dashi daga cikin motar, yanufi masalanci dake kusa da gidansu Abdullah domin yayi sallah,
Yasan dolene Abdullah yafito domin yayi sallah, daga nan yabafashi labarin kowacece Bilkisu, ‘yar wace masarautace shine kawai abunda yakeso yasani a bakin Abdullah.”
Shiru kakeji har a’ka kammala sallah bega Abdullah ba, dibe dibe yashigayi koda zaiganshi amma beganshi,
Yanke shawara yayi yashiga cikin gidansu kai tsaye yayi masa dabarar da zai fanyace masa komai a kan Bilkisu,
Domin yanda yaga kan Abdullah namasa rawa ko aika yaro yayi yakirashi yasan bazai fitoba."
Kaitsaye yanufi gidan tare da sallama,
Mamarsu Abdullah ya tarar tsakar gida tana arwala,
Ya durkusa k’asa ya gaida ita, ta amsa masa cikin fara’a da sakin fuska,
Tace “Adnan dawowa kayi ne?” Yaufa bazaman lafiya amininka yadawo,
Adnan yayi murmushi ya sosa kai, yace “Ummu yana ciki kuwa?”
Ummu tace “yana d’akinsa shiga katashesa lokacin sallah yayi yana kwance,
Adnan ya mik’e yashiga d’akin Abdullah dake kwance saman makekeyar katafarsa yana shak’ar barci,
Adnan yashiga tashinsa yana bunbugar k’afarsa,
Abdullah yabud’e idonsa a hakanli yakai dibonsa ga maitashinsa yana cikin jin dad’in barcinsa,
Ai kuwa yayi ido biyu da Adnan
Zurbur yamike zaune yana mai kallon Adnan
Yace “dama nasan kaine, domin babu mai katsemin jin dad’in duniya sai kai,
To yanzun da katasheni me kakeso naimaka?”
Adnan yayi murmushin dole domin a xahirin gaskiya maganganun da Abdullah yake fad’a masa sunayimasa ciyo a rayuwarsa amma baya nuna masa, saboda yana buk’atar yabashi labarin Bilkisu wadda ya dad’e yana nema.”
Danne zuciyarsa yayi, yace “sorry abokina tashi lokacin sallah ne yayi kana kwance kanata shak’ar barci,
Kuma kasan kwana biyu nayi missing d’inka,
Bilkisu ta d’aukemun kai.”
Jin ya ambaci sunan Bilkisu Abdullah yamik’e zaune yana murmushin jin dad’i a fuskarsa,
Wadda yabawa Adnan mamaki.”
Abdullah yace “wlh kuwa nima nayi missing d’inka abokina bari nayi sallah kasha labari da d’umi d’uminsa.”
Adnan yayi murmushin dole, yace “yawwa my friend ayi mana addu’a.”
Dariya yayi ya d’auro alwala ya shinfid’a darduma tayar da sallah,
Adnan na kallonsa.”
Bayan ya idar da sallah ne Ummu tagabatar masu da abinci,
Damun shinkafane yasha kayan lambu da busanshin kifi,
Adnan yakai dibansa ga abincin, yaga kalar abincin da Addah take dafa masu duk ranar juma’a,
Filet d’in abincin yajawo a gabansa yana mai had’iyar yawu,
Soma cin abincin yayi yana mai kallon Abdullah domin ya matso yafad’a masa asalin wace ce Bilkisu,
Yana gudun yafayiwq Abdullah maganar,
Yace yafasa gayamasa, domin ya fahimci dawowarsa wani rashin mutunci yakeji dashi,
Besan abunda ya hango a masarautar su Bilkisu ba,
Wadda shi a masarautarsu basu dashi.”
Ya kuma kallonsa yace “abokina baka bani labarin zamanda kayi da fadawa ba?”
Abdullah yayi dariya yace “bari kawai prince nasha wuya,
Kuma daga baya nasha dad’i, domin kuwa abincin damukece tare da fadawa kamar abincin da sarki yakeci,
Bari kawai prince ai mulki da daraja d’an Adam na masarautar su Bilkisu,
Sannan kullum cikin farin ciki muke kwana mutashi cikinsa sab’anin nan,
Prince yayi saurin katsesa zuciyarsa nayimasa tafasa, yana yabun kirkin wata masautar da batasuba, kuma abunda yakeso yafad’a masa bashi yake fad’a masaba????
Yayi karfin halin yimasa magana yace “friend abunda nakeso nasani shine,
Wace ce Bilkisu?”
Kuma a wane gari take?”
Waye mahaifinta?”
Abdullah yayi dariya yace “Bilkisu Abdurraham yola kenan, haifanfiyar ‘yar yolace,
Mahaifinta Abdurrahaman yola shike mulkin garin yola ma’ana shine sarkin garin yola,
Najiya a bakin fadawanta cewa mahaifin Bilkisu duk a cikin ‘ya’yansa yafisonta, domin kyawawan halayenta da kuma daraja d’an Adam,
Kuma Batada girman kai irin ba ‘ya’yan sarauta,
Asalima bataso a san cewa ita ‘yar sarkice,
Wannan dalilin ne yasa taxab’i karatu a garin, domin babu wadda yasan ko ita wace ce bare adinga bata girman da zai hanata karatu cikin kwanciyar hankali.”
To kaji tak’aitancin tarihim gimbiya Bilkisu.”
Magana yakeyiwa Prince amma hankalinsa gaba d’aya yatafi tunanin Bilkisu,
Dayaji cewa ‘yar sarkin yola ce,
To ‘yar wacece a cikin matan maimartaba?”
Tunawa yayi da fuskar Bahijja, tabbas tun farkon ganinsa da Bahijja yaga tanayimasa kama da fuskar dayasani,
Sai a yanzun yagane bada kowa take masa kamaba face Bilkisu,
Kodai d’akinsu d’aya da?”
Zurbur yamik’e tsaye sai maganganu yakeyi kamar wani zaranre,
Yana fad’in tabbas k’auwar Bahijja ce,
Domin sai a yanzun yatuna Bahijja tanada k’auwa wadda take bimata, domin su biyu ne ‘ya’ya mata a wurin Ammi,
Kuma yasan Bilkisu tun tana k’aramarta ganeta ganeta kawaine beyiba,
Yaja wani dogon tsaki wadda sai da Abdullah yazabura ya mik’e tsaye,
Yadafasa yace “prince lafiya kake kuwa?”
Naji kana wasu maganganu dangane da Bilkisu kodai kunada alak’atane da masarautar su Bilkisu ne?”
Domin da alamar hakan a fuskarka,
Adnan yace ban tabbatarba sainayi bincike,
Ya d’auki key d’in motarsa yayi ficewarsa, yabar Abdullah a tsaye yana mamakin d’an uwanka amma bakasan d’an uwanka bane, saboda rashin sadarda zumunta tsakaninka da d’an uwanka babu wadda yasan juna saida idon kun had’u a hanya katuru kudinga yiwa junanku rashin mutunci saboda babu wadda yasan juna a tsakaninku,
Allah yabamu ikon sada zumunci.”
Abdullah yayi murmushin jin dad’i yace “Allah yasa idan kabincika kagano ‘yar uwarka ce,
Danafi kowa jin dad’i domin gaba d’aya zan tattara kayana nakoma masarautarsu Bilkisu da zama.”????
Writing by
Fareeda
Bashir✍????
????????????????????????????????????????