A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

A WATA MASARAUTAR….
????????????????????????????????????????
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S
page2⃣6⃣ 2⃣7⃣
Prince tafiya yake hankalinsa gaba d’aya baya jikinsa,
Sai tunanin Bilkisu yakeyi yana mamakin rayuwa irin nata,
Bilkisu kuwa tun lokacinda tasanya fadawanta suki Abdullah take dibun prince shima yazo yafitar da ita cikin wannan gidan, amma shuru takeji bezoba,
Durk’ushe take tana mai zubar da hawaye, idan tatuna halinda jakadiya take ciki a yanzun na rashinta datayi,
tana tausaya mata domin tasan hankalinta a tashe yake yanzun,
Tsayowar motarsa tajiyo, da sauri tayi tashare hawayenda ke zuba a fuskarta, domin karyaga nadama a fuskarta,
Tashi tayi daga tsugunnen datake tayi saurin hawa kan kujera ta kwanta tarufe idonta alamar barci takeyi,
Tanajinsa lokacinda yasanya key yabud’e k’ofar d’akin yashigo ya ganta a kwance tana barci cikin nutsuwa,
Matsowa yayi kusa da ita ya tsora mata ido yana kallonta cike da tausayi, ganin yayi takoma masa Bahijja sak, murza idonsa ya kumayi domin ya tabbatar da gaskyar ita d’ince ko kuwa gizau take masa, ita d’in daice yagani kwance tana barci cikin kwanciyar hankali,.
Sai gani yayi tak’ara masa kyau da gwarjini, ya kai dibunsa a agogon gwal dake d’aure a hannunta yaganshi da tambarin masarautar yola, a nan take tausayinta ya lunlubeshi ya durk’usa saiti kujerar da take kwance yasunkuyar da kansa dai dai saiti bakinta ya kaimata kiss a baki, sai ganin yayi tabud’e idanunta,
zurbur tayi tamik’e zaune tanaimasa kallon tahuma, tace “to Allah yakamaka, mekakeso ka aika mun?” Rayfen d’ina zakayi kome kake nufi?”
Shi kuma kunya duk ta lunlub’esa, amma sai ya wayance ya mere baki, yace mezanyi dake?” dibeki, dan Allah malama kitashi na maidake inda na d’aukoki,domin inada abunyi, yana kaiwa nan yanufi hanyar waje yabarta a nan zaune.”
Ganin yafita, itama ta mik’e tabi bayansa, ta tarar dashi har yashiga motarsa ita kad’ai yake jira,
Tana zuwa wurin Taja tayi tsaye jikin motar taki shiga,
shima ita yake kallon cike da mamaki,
Saida suka d’auki kusan minti 30 yaga batada niyar shiga motar,
Bud’e murfin motar yayi yafito yana huci, yace “dan Allah malama idan bakitashi tafiya ba, ki kauce kibani hanya na wuce, domin ni inada abunyi,
Bata kallesaba kuma bata d’aga daga inda takeba,
Ganin zata b’atamasa lokaci yaja hannunta yabud’e murfin motar ya turata a ciki,
Yazagaya mazauninsa yashiga yatayar da motar suka bar gidan,
Kallonsa takeyi cikin k’asaita mulki tace “a she kasan abunda nake nufi?”
Ya zama Dole abud’ewa gimbiya mota idan tazata shiga,
Be tankamata ba domin ya fahimci neman magana take dashi, yaci gaba da tuk’in motarsa.”
Hanyar makaranta yanufa da ita, zai ajiyeta a inda ya d’auketa,
Tsayarda motarsa a cikin makarantar yayi daidai da gaba d’aya d’alibai sunfito lacture motar prince na tsayawa sai a kan idon Safeenat dake zaune tayi tagumi tana tunanin Bilkisu
Atake gaban Safeenat yafad’i da tahango Bilkisu a cikin motar prince,
Wata irin k’ara tasaki tazubar da littafan hannunta, wadda taja hankalin d’aliban makarantar gaba d’aya a gareta domin ganin meke faruwa?”
Wurin Bilkisu tanufa da gudu, ta rungumeta tana zubar da hawaye,
Kallo d’alibai suka bisu dashi, suna mamakin ganin Bilkisu tafito a motar prince, domin suna da labarin b’acewarta yau kwana biyu kenan,
Safeenat tamaida kallonta a wurin prince dake tsaye a bakin motarsa,
Tanunasa da yatsa idanunta cike da hawaye, Tace “wannan azzalumin ne yad’aukeke?”
Wlh Allah saiya sakamaki,
Ta kuma rungume Bilkisu tana kuka tace “sister ina fatan beyimaki komaiba.
Bilkisu ido cike da hawaye ta kalli Safeenat ta kuma juyawa ta kalli mutanen dake kallonsu jira sukeyi suji dalili,
Tace ” jama’a kudibesa,
tayimasu nuni da prince dake tsaye cike da mamaki,
Ko wannesu ya maida kallonsa a wurin prince
Tace shine yasace ni,
da kansa bawai sanyawa yayi a saceniba,
a matsayinsa na d’an sarki meye hukuncinsa?”
Kowa shuru yayi, rike da baki, yana kallon prince cike da mamaki,
Ta kuma matsawa kusa da shi ido cike da hawaye tace ” nace banasonka, kakirani a waya, katuramun sak’on text duk a kan nayi hakuri nasoka, domin ka fahimci cewa ni ‘yar sarkice,
Nanumaka bana ra’ayinka, bana iya soyayyah dakai, shine kasace katafi dani gidanka domin kayi rayfen d’ina,
To Allah yafika azzalumi mai mugun nufi, Allah zaice gaba da tsareni daga shairinka,
Aikuwa a nan d’alibai kowa yasaki baki da kunne, suka had’a baki sukace fed’e???? to Allah ya kyauta
Amma dai prince kabamu mamaki???? kowa ya kama gabansa yana fad’in albarkacin bakinsa,
Safeenat tamatso kusa gareta ta dafa kafad’arta tace sister ina fatan beketa maki haddiba?”
“tanunasa da hannu tace “Allah yafishi,
Allah ya kwaceni a hannun azzalumi irinsa,
Amma kasani bazan barkaba har saina d’auki fansar saceni dakayi kwana biyu batare da hakkina ba,
Prince mutuwar tsaye yayi yana mamakin makirci irin na ‘ya mace, yanuna kansa cikin sarkewar murya yace ” rayfen nizanyi rayfen d’inki?”
Me gareki wadda zaibani sha’awar da zaisanya nai maki fed’e?”
To bari kiji ni har yanzun banganki a mace ba.
Amma idon hakan kike buk’ata zan aikata maki basai kin had’a dayimun k’azafiba.
Idanunsa sunkad’e sunyi jajir alamar ransa yab’aci sosai, yashiga motarsa yayi tafiyarsa
Tok’i yake yana tunanin tuzarcin da Bilkisu tayimasa a bainar jama’a,
Ya kaiwa sitiyarin mota doka, had’i da Jan wani dogon tsaki,
Tambas zand’auki mataki a kanki Bilkisu,
Ba ‘yar uwata kikeba ko ciki d’aya muka fito dake saina d’aukar maki mataki mai muni,
Wadda yafi fed’e ciyo.”
Writing by
Fareeda
Bashir✍????
????????????????????????????????????????
A WATA MASARAUTAR…
????????????????????????????????????????
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S
Page 2⃣8⃣ 2⃣9⃣
Gudu yake a kantiti kamar ba’a hanyacinsa yakeba, Allah ne kadai yakawosa gida lafiya,
Aguje yashigo da motarsa ya ajiyeta parking space, a can ya hango Bahijja da Fahad suna tattauna maganar aurensu,
Ganinsa dasukayi yashigo ba a hayyacinsaba duk Kansu sukashi mamaki meke damun?”
Fahad yace “kwana biyun nan yarasa abunda kedamun prince kullom cikin k’unci yake ba fara’a a fuskarsa, duk yashigo gida baya kula duk wadda ke masa magana, yanzun diba kigani yanda yashigo gidan nan kuma a haka zai rab’amu yawuce batare da yayi makowa maganaba a cikinmu
Bahijja tace “wlh kuwa nima hakan nakeganinsa kullum cikin damuwa,
Basu gama rufe bakinsuba yanufosu idanunsa sunkad’e sunyi jajir,
Kallon tuhuma suka bishi dashi gaba d’ayansu, suna jiran suji tabakinsa.
Ya k’ak’aro murmushin dole, yad’an saki fuskarsa yace “amarya da ango kunan zaune ashan soyayya,
Fahad betanka masaba,
sai Bahijja ce tace masa “zaunan kowa yayi aure yabarka,
baka daniyar yin auren, sai fama kake da bak’in rai tsakankanin nan gidan nan kowa maganarka yakeyi anrasa abunda ke damunka,
Sai a lokacin Fahad ya kallesa yace,
Idan kaga dama memartaba na nemanka.
Ya kalli Fahad yayi dariya domin a yanayinda yayi masa mgana ya fahimci fushi yakeyi dashi.
Ya kuma maida kallonsa a Bahijja yace Anty Bahijja na tambaye?”
Bahijja tace “ina saurarenka Adnan Allah yasa nasan amsar tambayarka,
Yace “waini ina k’auwar nan taki Bilkisu?”
Bahijja tace “Allah sarki Bilkisu baiwar Allah, tana nan lafiyarta k’alau anan garinma take karatu,
Adnan yace ce wata yarinya ce mukahad’u da ita a makaranta naji ina mutuwar sonta,
Kamarku d’aya da ita sak,
Duk damuwarda kukaganni nashiga kwana biyun nan, duk a kantane,
Ina tunin a raina cewa kamar Bilkisu ce domin kamarku haryab’aci, kinsan tunlokacin da Bilkisu nak’ara rabona da ganinta.