A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Fahad yace “ina zakasanta tunda bakason zumunci,
Farkon ganinka da Bahijja ai kasa ganeta kayi sai daga baya sannan kaganeta,
Adnan yayi murmushi a zuciyarsa yanason ya tabbatar da Bilkisu ‘yar uwansa ce?” Itace k’auwar bahijja kuwa?”
domin yasan kalar hukuncin da zai d’aukar mata, dan yayi alk’awali da rayuwarsa tunda tayimasa k’azafin yatashi yin rapean d’inta,
A gaban bainar jama’a to tabbas tunda hakan takeso zai aikatashi a kanta, ko kuma yayi mata abunda yafi rapean ciyo.”
Yace Anty Bahijja don Allah kid’an nunamun photo nan Bilkisu a wayarki nagani, domin na tabbatar da k’auwatace tashiga birnin zuciyata.
Dariya sukashiga yimasa gaba d’ayansu,
Fahad yace Ashe soyayya ce take neman ta zautarmun da d’an uwa, muka rasa gane kansa a gidan nan,
Bahijja ya takamomasa photo nan Bilkisu tanuna masa tace kaganta nan, Allah yasa dai itace tanemi zarar dakai,
Yayi dariyar da tafi kuka ciyo shekad’ai yasan abunda ke zuciyarsa,
Ya amshi wayar yashiga diba photo nan Bilkisu,
Ganin photo Bilkisu dayayi ya tabbatar da ita d’in daice, yayi saurin mik’ewa tsaye yana fad’in tabbas itace itace wlh,
Gaba d’ayansu dariya suke masa a ganinsu ya zare a soyayyar Bilkisu.
Cikin dariya Bahijja tace zauna mana Adnan muyi magana.
Sai a lokacin ya nemi wuri ya zauna,
Tareda cewa Anty Bahijja kuna kama da ita sosai,
Inason natuna da wani abun shin Ku biyu ne ‘ya’ya mata a wurin Ammi ko?”
Bahijja tace kwarai kuwa, mu uku ne ‘ya’ya a wurin Ammi yaya Abdulraham shine babba sai ni, sannan kuma Bilkisu ita k’arama a d’akinmu wadda gaba d’aya halinta ya babbanta da nakowa a familynmu,
Saboda kyawawan halayanta maimartaba yafi sonta a cikin ‘ya’yansa.
Yacije baki yace Anty Bahijja inason Bilkisu kuma aurenta zanyi,
Wlh idan bansamu Bilkisu ba zan iya rasa rayuwatah.
Kitaimakeni Anty Bahijja kibani Bilkisu.
Dariya sukadinga yimasa gaba d’ayansu lokaci d’aya duk yafita hankalinsa a kan soyayya,
Fahad yadafa kafad’arsa yace “ka kwantar da hankalinka Adnan indai Bilkisu ce kasanyawa rayuwarka tazama matarka,
Yanzun katashi katafi kaji kiranda maimartaba yake maka daga can kafad’amasa k’udirinka a kan Bilkisu.
Mi’kewa yayi yanufi sashin maimartaba, a zuciyarsa kuwa yana Addu’ar Allah yasa kudirinsa ya cika.”
Writing by
Fareeda
Bashir✍????
????????????????????????????????????????
A WATA MASARAUTAR..
????????????????????????????????????????
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S
3⃣0⃣ 3⃣1⃣
Dashigarsa sashin maimartaba,
Ya tarar dashi zaune rik’e da jarida a hannunsa yana karatu.
Sallama yayi masa jiki ba gwari yashiga cikin d’akin,
Yanemi wuri ya zauna a k’asan
gefin k’afar maimartaba , ya sunkuyar da kansa k’asa,
yace “Allah yataimakeka Allah yakara maka lafiya ranka ya dad’e gani yarima Fahad yace kana nemana.
Maimartaba ya maida kallonsa akan Adnan yaga duk yarame masa yayi bak’i.
Sannan yayi kyaran murya yace “Adnan waimeke damunka?” Kwana biyu na lura dakai bakacikin hankalinka?”
Meke damunka wadda mu mahaifanka bazaka iya fad’a mana shiba,
Tun shekaran jiya nasanya d’an uwanka Fahad yakiramun kai domin mutattauna akan tafiyar da zamuyi a gobe zuwa yola, domin nemawa Fahad auren Bahijja,
Amma dazarar antukari d’akinka sai aji kofa a rufe harka fita.”
Ina kake zuwa?”
Meke damunka wadda a matsayinmu na mahaifanka bazaka iya fad’a mana Shiba?”
Adnan yasunkuyar da kansa k’asa yace “ranka ya dad’e tuba nakeyi,
Munkun fara jarabawa karatu ne yake hanani sukuni kwana biyu nan, kayi hakuri insha Allahu hakan bazai sake faruwaba, tuba nakeyi.
Maimartaba yayi murmushin jin dad’i
Yace “meye shawararka na tafiyar da zamuyi yola gobe Neman auren Fahad da Bahijja?”
Banida wani buri a rayuwata illah naga na aurar daku lokaci d’aya dakai da d’an uwanka, amma kai har yanzun ba kasamu matar da kakeso ba,
Mamynka tasha nema maka ‘ya’yan k’awayenta amma gaba d’ayansu bbu wace tayi maka a rayuwarka,
Adnan yakuma sunkuyar da kansa k’asa yace Allah ya taimakeka ai nesa tazo kusa,
Murmushi jindad’e yayi, yace “Allah yasa cemun zakayi kasamu matar aure, danafi kowa jin dad’i,
Sai na had’aka da d’an uwanka na aurar daku gaba d’aya.
Adnan yayi murmushin jin kunya, yace “kusan hakan ne ranka ya dad’e,
Maimartaba yace “Alhamdulillah.
‘Yar waya?”
A wace unguwa take?”
Waye mahaifinta?”
Adnan yayi murmushi ya sunkuyar da kansa, yace Allah ya taimakeka k’auwar Bahijja ce Bilkisu, tare muke karatu da ita, kuma munfahimci junanmu tana sona Nima inasonta, Abba ka taimakamun karnasa Bilkisu.
Maimartaba yace Alhamdullah abu yazo gida kenan, amma naji dad’i sosai Allah yasa abukanin arzikinkune.
Murmushi yake yana cike da jin kunya ya amsa da Amin Abba,
Mikewa tsaye yayi zaitafi d’akinsa, yace Abba natafi sai da safe,
gobe tafiyar safe zakuyi kuwa?”
Maimartaba yace “tafiyar safe nakeso muyi in Allah ya yarda.
Allah ya tsareku Abba ya kuma kaiku lafiya dawo mana dakai cikin koshin lafiya.
Cike dajin dad’i Abba ya amsa da Amin Adnan.
Yafito yanufi d’akinsa shekad’ai yasan abunda ke cikin zuciyarsa.
Shigarsa d’akin yacire kayansa, yana mai dariyar mugunta yana fad’in gimbiya Bilkisu kenan kinshigo hannuna zanwula k’antaki yanda naga dama, domin ba d’igon sonki a cikin zuciyata ko d’aya,
kuma dole kiyi biyayya saboda kina k’arkashin inuwar aurenah,
Zanyi amfani da wannan damar na aure ki domin nad’auki famsar abunda kika aikatamun a gaban bainar jama’a.
Ya kuma yin murmushin mugunta, yacije baki, yace “nalura da idanunki saikin buk’atar d’a namiji,
da wannan zanyi amfani, na azabtardake azaba mai tsanani, saikinyi danasanin aurenah rayuwarki.”
Yayi kwanciyarsa yana tunanin mugunta iri iri a rayuwarsa.”
Maimartaba sarki Bashir mahaifinsu Adnan yasauka garin yola lafiya,
Inda yasamu tarba da karramawa a masautar yola,
Yayi farin cikin karramashi da akayi,
Daga nan yashiga fad’awa mai martaba abunda ke tafe dashi.”
yazo neman auren Bahijja da Bilkisu,
Sarki Abdulraham yaji dad’i kuma yayi farinciki da zuwan nasa,
yace ” aidakayi zamanka ba saikazoba ko aike kayi ya wadatar, kuma Bahijja da Bilkisu ‘ya’yankane duk yanda kazartar da hukunci a kansu dai dai ne, ba saika taso tun daga kano zuwa yola nemawa Fahad da Adnan aureba.
Amma wani hanzari ba guduba, ‘yarka Bilkisu karatu takeyi bansaniba ko Adnan zai iya jiranta harta kammala karatun nata sannan daga baya sai ayi bikin nasu, a lokacin ta mammals karatun nata.
hakan naga yafi.
Sarki Bashir yayi murmushin jin dad’i yace Bakomai hakan da katsara yayi dai dai zanje na shawarci Adnan idan yanada ra’ayin barinta karatu bayan anyi auren saitaci gaba da karatun dama kuwa makarantarsu d’aya.
Murmushi sarki Abdulraham yayi yace “hakan shine daidai idan ya amince sai ayi auren gaba d’aya,
Nima zankira Bilkisu domin naji ra’ayinta a kan hakan,
A haka sukayi sallama suka rabu cikin farin ciki da kewar juna.
Bilkisu kwana biyu hankalinta ya kwanta ta natsu karatunta tasanya a gaba, domin sunkusan fara exam, tsakaninta da prince sai dai kallo, itama mamaki yakebata domin gata gashi sai dai yarab’ata yawuce itama hakan,
Tana mamakinsa amma a zuciyarta bata yarda dashi ba domin tasan a kwai wata kullanliya dayake kullawa a rayuwarsa,
Ita kuma ta d’auki d’amarar duk abunda yake nufi tafishi jinsa.
TOPHA OHH NI UMMU SAFWAN