A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Ummi yaushe kika shigo?
Ya xa ayi kasan shigowata kabude Baki da Hanci kana barci, Kaduba lkci kagani ynxun karfe nawa? Ba test naji kace ke garekuba?
Yana diba lokaci yatashi da sauri yafada tolet yyi wanka, koda yafito ummi ta tafiyarta tabashi wuri yashirya.
Yana fitowa a gurguje ya shirya yasanya kananun kaya, sunyimasa kyau, ya dauki key din motarsa yafito domin tafiya makaranta, duk inda ya wurga bayi sai kaimasa gaisuwa sukeyi ko kallonsu bayayi, suma basudamu da hkanba domin idon da sabo sunsaba da halinsa. prince adnan kenan,
Birnin kano garine mai yalwar mutane, acikin garin a kwai wata masarauta wadda sarki Bashir yake tsaye tsayendaka domin yaga ya amsarwa talakawansa hakkinsu.
Sarki Bashir yanada mata biyu
Matarsa ta farko hajia nafeesa haihuwarta daya namiji saidai bexo da raiba, tundaga lokcin ko batan wata bata kuma yiba,
Mahaifiyar sarki ta matsamasa akan yakara aure, hka ya amince, ya aure diyar kaunarta maryam, ansha shagulgular biki amarya maryam Tatare a gdan sarauta, bikinsu da wata biyu tasamu ciki, sarki yyi murna da samun cikin maryam, ko ba komai xaisamu magajin sarautarsa,
Baking ciki awurin hajiya mafeesa kuwa ba a mgna, domin duk duniyar nan bbu wadda ta tsana samada maryam da kuma Addah, domin cewa takeyi duk munafurcin Addah ne, datasanya sarki yayi aure.
Haihuwar maryam ta farko ta haifi danta namiji, Wanda yaci sunan fahad, yaro mai kama da mahaifinsa, kamarsu data da sarki,
sarki ya dauki son duniyar nan yadorashi a kan fahad
Fahad Nada shekara hudu, ta kuma samun wani cikin tahaifi adnan, sarki yyi murna da haihuwar adnan domin anyi shagulgular biki irin na gdan sarauta.
Fahad da adnan suntaso cikin kulawa da gata domin sarki bayason abunda ya tabasu,
Adnan shine karami, amma bayajin magana ga miskilanci da qasaita, da ixxah, Takai takawo fahad shine babba amma kamar shine karami.
Yanada shekara shidda ta haifi yarta mace, taci sunan fareedah, tundaga lkcin bata kuma haihuwaba fareeda itace autar sarki Bashir,
Motocine suka tsaitsaya nesa da makarantar, prince abdull da gimbiya bilkisu tareda jakadiya suka karasa makarantar, wurin shugaban mkrantar suka wuce dama yasan da xuwan nasu, maimartaba yyiwa shugaban mkratar bayin xuwan nasu.
Domin maimartaba yaturawa shugaban mkratar kudi yanemawa gimbiya bilkisu madaidaicin gida inda data xauna tare da jakadiya.
Prince abdull tareda bilkisu da shugaban mkratar suka fito daga office, xairakasu gdanda akasayawa bilkisu domin ta xauna tayi karatunta.
Isarsu gdan kenan Prince abdull ya kalli gdan ya kuma kallon bilkisu yace mata, ke ynxun kinfison xama a irin wnn rywar?
Murmushi tayi tace yaya abdull a halin yanxun addu’arka nake nema Allah yabani abunda nafito nema, baice mata komaiba daga kafadarsa yyi alamar taji xata iyane
Yyimata sallama tare da fatan alkhairi yatafiyarsa, yabarta tare da jakadiya.
Prince adnan ne tareda yarima fahad yayansa, cikin mota direba na tukasu, tsaki kawai adnan keyi, yanayi2 yana dibon agogon gwal dake sanye a hannunsa, yajuya ya kalle fahad dayake kallon kwalta, ynajinsa yana tsaki amma yakyalesa,
Sai a adnan ne yajuyo da fuskarsa yana kallon fahad yace yaya nakusan latti fa, sai lokacin fahad ya kallesa yyi mgna.
Yace Kaine adnan bakajin mgna, ai INA ganin kasanda xakuyi test din amma kashige daki kadinga barcika harda wani sanya fadawa sutsareka don kar a tasheka, Allah danice ummi baxan tashekaba kyaleka xanyi tunda bakada son karatu, bnda ummi tatasheka dakayi lorxing din test din gabadaya, niyanxun taimako daya xan iyayimaka shine dama direba ajiyeni xaiyi, nan gaba kadan, nashiga motata nakarasa inda xantafi, to amma kafini uxuri, idon mukaxo kashiga motar tawa saika karasa mkrantar ynda zakayi sauri.
Murmushi yyi yace ngd big brother don hkan nkesonka, dariya fahad yyi, ddai nan direba yayi farking yafito, yashiga motar yayan nasa yajatada karfi sai mkranta.
Written by ummu Safwan lov u all????????
????????????????????????????????????????
A wata masarautar…..
????????????????????????????????????????
Writting by Ummu Safwan 07066214433
Page3⃣
Motocine na tsaitsaya a nesa da makarantar, prince abdull ne tareda gimbiya bilkisu da kuma jakadiya, suka fito, suka nufi mkrantar, kai tsaye offishin shugaban mkranta suka nufa, kasancewar prince abdull yasan offishin basu sha wahalar tmbyaba, kaitsaye sukayi sallama sukashiga, dama yasan da xuwan nasu, maimartaba yakirashi a waya yyimasa bayanin komai, ya kuma turamasa da kudi domin a sayawa gimbiya bilkisu gidanda xata zauna tare da jakadiya.
Nan suka kareyin komai, suka dunguma gaba dayansu, suka tafi gidanda gimbiya bilkisu xata xauna tareda jakadiya.
Gidane karami naxaman mace daya madaidace, prince abdull yajuya ya kalli gimbiya bilkisu, sai ya merebaki, yace, ynxun kinfi bukatar xama a irin wnn rywar? Kina ganin gatane kikayiwa kanki daxaki xauna a irin wannan gidan, Kibaro masarautarku dagatanki da komai kidawo inda ba a sankiba, ba a san koke wacece ba kice anan xakiyi rywa.
Gimbiya bilkisu ta sunkuyar da kanta kasa, tace yaya katayani da addu’a Allah yabani abunda nafito nema, domin ynxun addu’arku nake nema.
Ya kada kafada, a lamar ita tasani, yyi mata sallama yatafiyarsa.
A nan take jakadiya tanufota, tafadi kasa alamar girmamawa, tana fadin, Allah yajadaran gimbiya mekike bukata, a girka maki?
Saita bata fuska, banaso, a matsayin ammi ta nadaukeki banason wasu sugane wani abu a taredamu,
Jakadiya ta kuma runsunawa tana fadin ayi hakuri idon nabata ran gimbiya????????
Kinga irinta ko, ni kidaina cemun gimbiya, kikirani a bilkisu na????????
Jakadiya tace gaskiya ranki ya dade baxan iya kiran sunankiba, domin idon nayi hkan sainaga kamar naxubar da darajar masarauta, amma daga ynxun zandinga kiranki da diyata,
Sai lokacin gimbiya tayi murmushi, tace bakomai na fahimceki jakadiya,ko hkan kika kiranidashi yayi.
Nan tawuce daki domin tayi wanka, dakin ba laifin angyarashi kuma yyi kyau dai2 gwargwado, tafada toilet tayi wanka, koda tafito jakadiya hartakare masu abinci, nan tafaraci suna fira, tana kammalawa, ta haye gdonta takwanta, tareda tunanin gobe xatafara daukar darasi
Gimbiya bilkisu ce cikin shirinta na xuwa makaranta, tasanya atamfarta pink and yellow, da hijabinta shima kalar pink tayi kyau, dama gata farar mace kuma kyankyawa.
tafito ta iske jakadiya takaremasu abinci ta xauna taci, Saida ta koshi sannan tace jakadiya saina dawo,
Jakadiya ta ajeye abunda takeyi tanufota tanafadin, Allah ya tsareki gimbiya takawarki lafiya yar sarki jikanyar sarki gaba sararauta gefinki mulki, Allah yadawo dake lfy gimbiya.
Bilkisu tayi dariya tace jakadiya baxaki dainaba kenan.
Tafiya takeyi kamar batason taka kasa, waya ta takeyi da antynta bahijja tana fadamata ynda sukayi missing dinta a family nasu, bataji horn din motaba saidai jitayi anbugeta da ita har saida tafadi kasa,
Saijitayi anja motar da karfi kowaye yyi tafiyarsa, saibiyar motar tayi da ido tana mamakin shi kuma wnn waye da xaibugeta da mota kuma yyi tafiyarsa,
Safeena ce taxo wucewa ta wurin taga abunda ke faruwa, ta sauri ta karaso wurin takamata, ta Taiyida ita tsaye, tana kakkabe mata jikinta, sannu kinji, ina fatan bakiji ciyoba?