A WATA MASAURAUTAR COMPLETE NOVEL

Adnan kuwa gaba d’aya yasusuce baya da maganar kowa sai ta Bilkisu,
Anty Bahijja ke k’ara kwantar masa da hankali akan cewa Bilkisu insha Allahu takusan zama matarsa,
Likita ya turo k’ofa yashigo had’ida yimasu sallama yanufi gadon Adnan domin ya ciremasa rubar jinin da ke hannunsa,
Doctor yakai dibansa ga Adnan yayi murmushi yace ” Adnan angon Bilkisu ina fatan ba abunda kemaka ciyo domin munasan ran sallamarka nan da zuwa gobe,
Adnan kwance yake amma jin doctor ya ambaci Bilkisu yayi zumut ya mik’e zaune,
Yana murmushi yace doctor kokasan Bilkisu ne?”
Kaga mundace da juna ko?”
Gata fara kyankyanwar yarinya mai dogon hanci, ga k’aramin baki,
Yace “doctor kaga Bahijja yayi nuni da Bahijja yace kamarsu d’aya da Bilkisu na,
Amma Bilkisu tafita kyau,
Gaba d’ayansu dariya suke masa ganin yanda soyayyar Bilkisu ta kusa zautar dashi,
Bahijja tace, ayye Adnan yanzun Nice Bilkisu tafini kyau?”
To lallai bazan baka aurantaba nafasa,
Aisai ganinshi tayi durk’oshe a gabanta rik’e da k’afafunta, yana fad’in “yi hakuri Anty Bahijja ki aura mun Bilkisu wlh idan narasa Bilkisu zan iya rasa rayuwata,
Sai a kunnen maimartaba, yace bazaka rasa ranyuwarka ba Adanan indai akan Bilkisu ne domin munyi mgana da mahaifinta yabaka Bilkisu amma dasharad’in sai ta kammala karatunta.”
Writing by
Ummu
Safwan
????????????????????????????????????????????
A WATA MASARAUTAR…..
????????????????????????????????????????
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S
Page3⃣7⃣ 3⃣8⃣
Adnan yace “dady kataimakamun karnarasa Bilkisu wlh idan narasata zan iya rasa rayuwa,
A yanda nakeji Bilkisu itace rayuwata rashinta a gareni komai zai iya faruwa dani, pls dady kataimakamun.
rik’e yake da k’afar dady yanayimasa magiya,
Maimartaba ya dafashi ya mik’ar dashi tsaye, tareda rungumeshi a jikinsa, cike da tausayin d’an nashi, ganin yafad’a tarkon soyayyah.
Yace “Adnan nafad’amaka ka kwantar da hankalinka Bilkisu tazama matarka,
Koyanzun idan kashirya za’a d’aura maka aure da Bilkisu amma da sharad’in zaka barta tacigaba da karatunta,
Idan kuma baka buk’atar matarka tadinga yawun makarata to kak’ara hakuri har lokacinda ta kammala karatun nata sai ayi bikin naku.
Pls Adnan kadaina damun zuciyarka da yawan damuwa,
Domin kaji bayanin da likita ya yimuna akan cewa ciyon zuciya ne yakeson kamaka saboda yawan tunanin da kakeyi,
Adnan yace “dady nayarda a aura mun Bilkisu zanbarta tacigaba da karatunta daga nan har k’asar waje idan tana buk’ata, wlh dady nayimata alk’awari zankaita domin tayi karatunta,
Ya juya ya kalli Bahijja dake zaune duk tausayinsa yama lunlub’eta,
Yace dady ga Anty Bahijja nan itace shaidata
zanbar Bilkisu tayi karatu.”
Dady yace "toshikenan tunda ka amince zamuyi waya da mahaifin nasu, sai nafad'a masa yanda mukayi dakai kaga daga k'arshe sai a sanya ranar aurenku lokaci d'aya tare da yayanka fahad gaba d'aya.
Murmushi yayi harsaida hak'oransa suka fito, cike da jin dad'i yace nagode dady."
Gaba d'ayansu suka sanya dariya."
Bilkisu ce keshir shirenta domin komawa makaranta, ta kamalla shiryawa, tsaf.
amma zuciyarta cike take da kunci domin tun jiya kobarci bata samutayiba, saboda tashin hankalin maganar da Abba yayi mata na auren Adnan,
D’akin maimartaba Tanufa, domin yimashi sallama,
Tura k’ofar tayi tareda sallama,
Ta isa kusa dashi ta durk’usa k’asa tareda sunkuyarda kanta, “tace Abba barka da hutawa.
Allah yataimakeka Allah ya tsare mana lafiyarka
Abba nashirya zan koma makaranta.
Abba yatashi daga kwancen dayake, yana mai murmushi a fuskarsa yace “gimbiya Bilkisu harkinsherya?”
Sai makaranta yanzun ?”
To Allah yakaiki lafiya, Allah ya tsaremumke a duk inda kike ,
Ina alfahari dake Bilkisu a cikin ‘ya’yana domin jajircewarki a kan karatunki, Allah yabaki ilimi mai amfani.”
Tasunkuyar da kanta k’asa tana mai zubar da hawaye, tace “Amin Abbah.
Maimartaba cikin rashin jin dad’in ganin hawayenta yace “Bilkisu mekikeyiwa kuka?”
Meke damunki?”
Tun lokacin da nayimaki mgnar auren d’an gidan sarki Bashir naga kinshiga wani yanayi natashin hankali bayan kuma ance kunfahimci junanku tun a makaranta,
Bilkisu waimeke damunki ne?”
Takuma sunkuyarda kanta tana mai shinshikar kuka, data tuna da cewa wai Adnan ne zaicewa sun fahimci juna dashi.
yabiyo ta wannan hanyar ne domin wata mummunar manufa tashi, ya aureta don yaji dad’in wulak’antata, amma tayi alk’awari a rayuwarta bazata tab’ayiwa mahaifinta musuba,
kuma bazata tab’a sanyashi yaji kunya a idon jama’a ba, bazan tab’a barin Abbanah yazama mai magana biyu,
amma zata nemi alfarma a wurinshi, wadda tasan zaiyimata ita.
Tasunkuyar da kanta k’asa, tace ” Abba babu abunda yake kedamuna,
Amma don Allah Abba ina Neman alfarma a wurinka.
Cikin yanayin tausayi, yace “fad’i Bilkisu ina saurarenki,
Tace “Abba don Allah katausayamun koda sun aikoma da cewa A d’aura aurenmu tare da Anty Bahijja,
Abba don Allah kataimamun kar d’aura dani,
Harsai na kamalla karatuna sannan.
pls Abba kataimamun ta kuma fashewa da kuka,
Abba yace “share hawayenki Bilkisu bazantab’ata yimaki abunda bakyasoba,
Tunda kinfi buk’atar saikin kammala karatun naki sannan kiyi aure, to shikenan sai ayi na antynki Bahijja daga baya sai a yinaki bikin,
Hakan yayi maki kuwa?
D’aga kai tayi had’ida yin murmushi jindad’i, tace “ngd Abbah
Abba shima murnushin yayi yace “daina yimun godiya burina shine akullum naga nafarantamki rai yanda kema kike k’okarin farantamun nawa ran, .
Tashi kitafi kar dare yayi maki a hanya.
Tamik’e tafita had’ida yimasa sallama,
Adnan jiki yayi kyau ansalameshi a asibiti,
Dashigarsu gida ya fad’a d’akinsa ya yayi wanka yayi kwanliya ta d’aukar hanka,
Sauri kawai yakeyi isa makaranta domin yayi ido biyu da Bilkusu,
Motar Abbansa yashiga wadda tafi motarsa komai, da shigarsa motar ya kalli fuskarsa a madubi yaga yayi kyawon da betab’ayin irinsaba murmushi yayi a ransa kuma sai cewa yake dole ne idan Bilkisu ta ganni taji itama takamu da matsanancin sona,
Yaja motar yanufi makaranta, domin Neman Bilkisu,
Dashigarsa makarantar mazaje group sai kuwa sukeyi naganinsa, amma be kulasuba sai waige waige yakeyi shidai burinsa yayi ido biyu da Bilkisu.”
Fareeda basheer????
????????????????????????????????????????
A WATA MASARAUTAR…
????????????????????????????????????????
Writing by
Ummu
Safwan
PURE MOMENT OF LIFE WRITER’S
3⃣9⃣ 4⃣0⃣
Amma besamu ganinta ba,
Acan ya hango safeenat zaune ita kad’ai, tana karatu, yanufota yana waige waige koda zaiga Bilkisu,
ko alamunta beganiba,
Yayiwa safeenat sallama had’ida samun wurin ya zauna a kusa da ita
Safeenat kallon mamaki tabishi dashi, sannan tabud’e baki tace malam lafiya ?”
Kowane sabon rashin mutuncin ne ka b’ullo dashi dashi ta hakan?”
To bud’e idanunka da kyau kaga kowacece kake zaune a kusa gareta,
Safeenat CE
Ba Bilkisu ba????
Don haka kashiga hankalinka,
Adnan yace “pls safeenat saurara kiji banzo da niyar cutarkuba wannan karon alkhairi ne yakawoni wurinku,
Pls Don Allah ina Bilkisu?”
tund’azon nake nemanta bangantaba,
Safeenat tayi zumut tamik’e tsaye,
Ta hararesa???? tace “bansa ran da akwai alkhairi a tareda kaiba.
Kabiyomun ta wata sigane, wadda bantab’a ganinka a cikintaba domin kana bukatar nafad’amaka inda Bilkisu take, dan kaji dad’i wula k’antata,
To kasani bazan tab’a fad’amaka a inda Bilkisu takeba saidai jin haushin hkan yasanya kayimun wulak’acin da kayi niyar yimata,????
Tad’auki littafanta tayi tafiyarta bata tsaya kuma saurarensa ba,
Shi kuwa sai kiranta yakeyi “safeenat tsaya kiji,
Wlh ba mugunta ce takawoniba alkhairi ne yakawoni Neman Bilkisu,
ki yarda dani,
Ko wai wayanshi batayi ba tayi tafiyarta tabar makarantar gaba d’aya,